An Gano Shugaban Kasar da Ya Kafa Kungiyar Lakurawa da Yadda Suka Shigo Najeriya
Ana tunanin cewa kalmar Lakurawa ta samo asali ne daga Hausa, wanda ke nufin “sababbin horarru.” Ana amfani da ita wajen kwatanta matasa da ke samun horo na soja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
An kafa rundunar Lakurawa a shekarar 1997 a karkashin shugabancin Ibrahim Baré Maïnassara a Nijar, don kare makiyaya daga masu satar shanu.

Asali: Getty Images
Asalin kasar da aka assasa Lakurawa
A lokacin, ‘yan fashi dauke da makamai daga Mali na yawan kutsawa cikin Nijar domin satar dabbobi, suna jefa makiyaya cikin hatsari, inji rahoton Zagazola Makama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce, saboda karancin tsaron soji a yankunan karkara, gwamnati ta ga wajibi a samar da wata ƙungiyar agaji don kare jama’a.
Don tunkarar ‘yan fashin da ke da manyan makamai, an bai wa Lakurawa horon soja da makamai masu ƙarfi, kuma an kafa sansanin kungiyar na farko a Ekrafane.

Kara karanta wannan
Biyan haraji: Majalisa ta yi wa sojoji gata, an gabatar da muhimmin kudiri a gabanta
A karkashin shugabancin Baré, Lakurawa sun yi nasara wajen fatattakar ‘yan fashi daga Mali, wanda hakan ya hana su sake kutsawa cikin Nijar.
Sakamakon wadannan nasarori, Shugaba Baré ya fadada shirin, inda aka kafa karin sansanonin horo guda uku tsakanin Ekrafane da Banibangou.
Rarrabuwar kawuna da rushewar Lakurawa
Bayan kashe Shugaba Baré a shekarar 1999, makomar Lakurawa ta zama babu tabbas, yayin da Shugaba Mamadou Tandja ya nemi hada su da Ƙungiyar Tsaron Kasa.
Rikicin siyasa tsakanin Firayim Minista Hama Amadou da ministan cikin gida, Albadé Abouba, ya hana aiwatar da shirin haɗa Lakurawa da sojoji.
Albadé ya bayar da umarnin a rusa Lakurawa, amma Hama Amadou ya ki yarda, daga baya kuma ya kafa wata sabuwar ƙungiya a Ouallam.
Manyan sojojin da suka yi aiki karkashin Baré da Tandja sun san da wanzuwar Lakurawa, ciki har da wasu daga cikin shugabannin mulkin soja na yanzu.
Gwamnatin Nijar ta kasa shigar da su cikin tsarin tsaro yadda ya kamata, hakan ya sa wasu suka arce da makamai, suka kafa ƙungiyoyin ‘yan bindiga masu zaman kansu.
Sauya akida: Daga dakarun gwamnati zuwa ‘yan jihadi
Bayan kifar da gwamnatin Shugaban Libya, Muammar Gaddafi a shekarar 2011, wasu daga cikin Lakurawa sun koma cikin MUJAO, wata kungiyar jihadi a Mali.
A shekarar 2013, bayan hare-haren sojin Faransa a arewacin Mali, wasu daga cikin waɗannan mayakan sun tsere zuwa Nijar da Arewacin Najeriya.
Daga wannan lokaci, wadannan mayaka da gwamnati ta horar don tsaron makiyaya, suka rikide suka koma mayakan Jihadi.
Yadda Lakurawa suka kwaroro zuwa Najeriya

Asali: Twitter
Bayan Faransa ta kaddamar da Operation Serval a shekarar 2013 domin fatattakar kungiyoyin jihadi daga arewacin Mali, lamarin Lakurawa ya sake sauya salo.
Wasu daga cikin mayakan MUJAO, ciki har da tsofaffin Lakurawa, sun tsere sakamakon farmakin soji, inda wasu suka kutsa cikin yankunan kan iyakar Nijar, har suka zauna Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman jihohin Sokoto da Kebbi.
A farkon zuwansu, al’ummomin yankunan sun karɓe su da kyau saboda tsayuwarsu kan yaki da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Kaduna, an samu asarar rayuka
Kwarewarsu a fagen yaki ya sa suka sami karbuwa a tsakanin al’ummomin karkara da ke fama da matsalar tsaro. Sai dai daga baya, hakikanin manufarsu ta fara bayyana.
Sabanin sauran kungiyoyin jihadi, Lakurawa ba sa neman suna ko bayyana kansu a fili. Ba kawai yaki da ‘yan ta’adda suke yi ba, manufarsu ita ce kafa daular Musulunci a yankin.
Ba sa daukar alhakin hare-haren da suka kai ko sakin bayanai na yada akida, sai dai su fake cikin kungiyoyin ‘yan fashi da ke aiki tsakanin Najeriya da Nijar.
Wannan dabara ta boye kansu ta basu damar yaduwa ba tare da an gano su ba. Sai dai yayin da tasirinsu ya fara karuwa, gwamnatin Najeriya ta dauki mataki.
A watan Disamba 2024, hukumomin Najeriya sun kaddamar da farmaki na soji a kan sansanonin Lakurawa.
A hadakar hare-haren sama da na kasa, daruruwa daga cikin mayakan kungiyar suka sheka barzahu.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya karbi bakuncin kungiyar 'Obedient' a Kano, ya ba su shawarwari
Mayakan Lakurawa sun kashe mutane a Kebbi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan ta'addan Lakurawa sun kai farmaki a Birnin Dede, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum 13 tare da kona kauyuka bakwai.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun afkawa kauyuka takwas da ke kusa da Birnin Dede, amma basu samu damar kai hari kan daya daga cikinsu ba.
Ana zargin cewa wannan harin na da nasaba da kisan Maigemu, shugaban 'yan ta'addan Lakurawa, wanda dakarun tsaro suka kashe a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng