Dakarun Sojoji Sun Hallaka Shugaban Dabar 'Yan Bindiga a Zamfara
- Dakarun sojoji masu aikin samar da tsaro sun yi namijin kokari wajen samu nasara a yaƙin da suke yi da ƴan bindiga a Zamfara
- Sojojin sun iya hallaka wani shugaban dabar ƴan bindiga mai suna Yellow Aboki bayan sun yi arangama a ƙaramar hukumar Tsafe
- Tantirin ɗan bindigan dai ya yi ƙaurin suna wajen addabar mutanen da ke rayuwa a ƙauyukan da ke yankin Arewa maso Yamma na Tsafe
- Nasarar da sojojin suka samu na zuwa ne a ci gaba da ƙoƙarin da suke yi na kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a Zamfara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Dakarun sojoji da ke gudanar da aikin kakkabe ƴan bindiga a jihar Zamfara sun hallaka wani sanannen tantiri mai suna ‘Yellow Aboki’.
Sojojin sun hallaka ɗan bindigan ne wanda ke da kusanci da marigayi jagoran ƴan ta’adda, Hassan Bamamu.

Kara karanta wannan
"An samu ci gaba": Matakin da mutane suka dauka don kawo karshen harin 'yan bindiga

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka kashe tantirin ɗan bindiga
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kawar da Yellow Aboki ne a wata arangama da dakarun rundunar Operation Fansan Yanma a yankin Arewa maso Yamma na ƙaramar hukumar Tsafe.
Mutuwarsa ta zo ne mako guda bayan nasarar da sojoji suka samu wajen kawar da Hassan Dantawaye, wanda aka fi sani da Bamamu, wanda yake a matsayin babban kwamandan ƴan bindiga kuma aminin Yellow Aboki.
Rahotanni sun nuna cewa bayan mutuwar Hassan Bamamu, Yellow Aboki ya fara ƙarfafa ikonsa wajen ta’addanci a Zamfara.
Majiyoyi sun ce yana gudanar da hare-hare da satar mutane a yankunan Bamamu, Dan Mali, Agamalafiya, da Makera, inda yake jagorantar ayyukan ta’addanci.
Sojoji sun taso ƴan bindiga a gaba
Rundunar sojoji na ci gaba da fatattakar shugabannin ƴan bindiga a sansanoninsu da aka gano a Zamfara, Sokoto da sauran wuraren da ke fama da matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun kai dauki bayan 'yan bindiga sun farmaki mutane, sun samu nasara
Wannan matsin lamba da sojoji ke yi ya raunana ƙarfinsu na yin gaba-da-gaba da dakarun tsaro, lamarin da ya sa suka koma kai hare-hare a ƙananan garuruwa da ke da ƙarancin tsaro.
Karanta wasu labaran kan sojoji
- Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, sun kashe babban kwamandan Boko Haram
- Dakarun sojoji sun kai dauki bayan 'yan bindiga sun farmaki mutane, sun samu nasara
- Sojoji sun lakadawa ma'aikatan lantarki duka bayan yanke wuta a bariki
Sojoji sun hallaka ƴan ta'addan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno ta Arewacin Najeriya.
Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram aƙalla guda tara bayan sun kai musu farmakin bazata a maɓoyarsu da ke dajin Sambisa.
Sojojin sun ƙaddamar da farmakin ne kan ƴan ta'addan a ƙaramar hukumar Bama bayan sun samu bayanan sirri kan motsinsu a yankin
Daga cikin ƴan ta'addan da aka kashe har da babban mai haɗa bama-bamai na ƙungiyar Boko Haram.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng