Esther Okereke: Fitacciyar Jarumar Fim a Najeriya Ta Samu Tikitin Takarar Shugaban Kasa a 2027

Esther Okereke: Fitacciyar Jarumar Fim a Najeriya Ta Samu Tikitin Takarar Shugaban Kasa a 2027

  • Jarumar fina-finai a Najeriya, Esther Okereke ta samu nasarar zama 'yar takarar shugaban kasa ta jam'iyyar NRM a zaben 2027
  • An tabbatar da Jaruma Okereke a matsayin ‘yar takarar NRM ne ta hanyar maslaha yayin zaben fitar da gwani da aka gudanar ranar Juma'a
  • Okereke ta bayyana cewa idan aka zabe ta a shekarar 2027, za ta aiwatar da wani babban shiri na farfado da Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar NRM ta ayyana fitacciyar jarumar fina-finai kuma furodusa, Esther Okereke, a matsayin ‘yar takararta ta shugaban kasa a zaben shekarar 2027.

An tabbatar da Jaruma Okereke a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar ne ta hanyar maslaha yayin zaben fitar da gwani da aka gudanar ranar Juma’a a birnin Abuja.

Esther Okereke
Futacciyar jarumar fina-finai a Najeriya, Esther Okereke yayin tabbatar da ita a matsayin yar takarar NRM a zaben shugaban kasa na 2027 Hoto: Esther Okereke
Source: Facebook

Yadda Okereke ta samu tikitin takara

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NDC ta jawo Kabiru Marafa, ta ba shi tikitin takarar gwamnan Zamfara a 2027

The Cable ta ruwaito cewa shugaban jam’iyyar NRM na kasa, Chinedu Obi, ya bayyana cewa Esther Okereke ce kadai ta cika dukkan sharuddan tantance ‘yan takara da jam’iyyar ta gindaya.

A cewarsa, duk da cewa wasu masu neman takara sun shiga fafatawar, amma ba su samu nasarar cika ka’idojin da aka shimfida ba.

Ya ce:

"Ko da yake akwai masu neman takara, amma ba su cika sharuddan da kwamitin tantancewa ya gindaya ba, sai dai shigarsu cikin wannan tsari ya kara karfafa dimokuradiyya da tsarin cikin gida na jam’iyyarmu."

Chinedi ya yaba wa sauran masu neman takarar bisa jajircewarsu da kuma yadda suka nuna kishin kasa da goyon baya ga manufofin jam’iyyar NRM.

NRM ta yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasashe

Shugaban NRM ya kuma nuna jin dadinsa kan yadda ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje suka nuna sha’awar shiga aikin sake gina kasa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya ce jam’iyyar na da yakinin cewa hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya a gida da waje zai taimaka wajen dawo da martabar Najeriya a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Aisha Yesufu ta janye daga neman takarar sanata a jam'iyyar NDC

Abubuwan da Esther Okereke ta yi alkawari

Da take jawabi bayan tabbatar da ita a matsayin ‘yar takara, Esther Okereke ta bayyana cewa idan aka zabe ta a shekarar 2027, za ta aiwatar da wani babban shiri na farfado da Najeriya.

Ta ce shirin nata zai mayar da hankali kan Inganta harkokin ilimi, samar da wadataccen makamashi, farfado da tattalin arziki, karfafa tsaro da inganta walwalar jama'a.

Esther.
Jaruma Esther Okereke lokacin da ta karbi tutar jam'iyyar NRM a matsayin shaidar zama yar takarar shugaban kasa Hoto: Esther Okereke
Source: Facebook

Haka zakila ta ce za ta maida hankali habaka fasaha da kirkire-kirkire, tabbatar da gaskiya da rikon amana a gwamnati, samar da gidaje masu araha, Inganta harkokin lafiya, karfafa matasa da ‘yan kasuwa da samar da ayyukan yi.

A cewarta, ba za a iya ceto Najeriya yadda ya kamata ba sai an samar da daidaito tsakanin maza da mata a harkokin shugabanci.

Marafa ya lashe tikitin NDC a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa tsohon sanatan Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa, ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

"A maido mani da kudi na," Matar da ta fito takarar shugaban kasa ta tada rigima a DLA

Sanata Marafa ya samu tikitin jam’iyyar ne ta hanyar maslaha bayan kasancewarsa shi kaɗai ya nemi takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar NDC.

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar NDC, Aminu Jelani, shi ne ya sanar da Marafa a matsayin dan takarar gwamna a hukumance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262