An kai Trump Asibiti domin Duba Lafiyar Shi, Likita Ya Fadi Sakamakon Bincike

An kai Trump Asibiti domin Duba Lafiyar Shi, Likita Ya Fadi Sakamakon Bincike

  • Sabon rahoton lafiyar Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda aka fitar a ranar Juma’a, ya bayyana halin da shugaban mai shekaru 79 ya ke ciki
  • Likitan Trump, Dr. Sean Barbabella ya ba shi shawarar rage kiba da kuma kara motsa jiki a matsayin wani bangare na matakan kariya ga lafiya
  • Rahoton ya fito ne daga likitan Fadar White House, Dr Barbabella, bayan Trump ya yi gwajin lafiya na yau da kullum a cibiyar kiwon lafiya ta Walter Reed

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Fadar White House ta fitar da sakamakon gwajin lafiyar Donald Trump na watan Mayun 2026 a daren Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewa an yi wa shugaba Donald Trump gwaje-gwaje ne a daidai lokacin da ya ke kusa da cika shekara 80 a duniya.

Kara karanta wannan

Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

Shugaba Donald Trump
Donald Trump a wajen wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayani kan lafiyar Trump

CNN ta ce White House ta wallafa wata takarda daga likitansa da ke ba shi shawarar rage kiba da kara motsa jiki, tare da jaddada cewa yana cikin kyakkyawan yanayin lafiya.

“Shugaba Trump na ci gaba da kasancewa cikin kyakkyawan yanayin lafiya, tare da nuna karfin zuciya, huhu, jijiyoyin kwakwalwa da kuma lafiyar jiki gaba daya,”

In ji likitan Fadar White House, Dr. Sean Barbabella, a cikin wasikarsa.

Ya kara da cewa:

“Yana da cikakken koshin lafiya domin gudanar da dukkan ayyukan babban kwamandan rundunar soji da shugaban kasa.”

Times of India ta wallafa cewa Dr Barbabella ya rubuta cewa an ba shugaban shawarar kariya ga lafiya yayin gwajin:

“Ciki har da shawarwari kan tsarin abinci, amfani da karamin adadin maganin aspirin, kara motsa jiki da kuma ci gaba da rage kiba.”

Likitan ya bayyana cewa tsayin shugaban ya kai kafa 6 da inci 3, yayin da nauyinsa ya kai 238. A gwajin lafiyarsa da aka yi a watan Afrilu na bara, Trump ya kai 224.

Kara karanta wannan

Iran ta harbo jirgin yakin Amurka a sama, dakarun Trump sun yi martani

Karo na 3 ana duba lafiyar Trump

Ziyararsa zuwa cibiyar kiwon lafiya ta sojoji ta Walter Reed a ranar Talata ita ce karo na uku da ya je wurin domin gwajin lafiya tun bayan da ya zama shugaban kasa mafi tsufa da aka rantsar a tarihi a bara.

Kafin ziyarar, Fadar White House ta ce gwajin zai hada da gwaje-gwajen hakora da na lafiya na shekara-shekara, duk da cewa ya riga ya ziyarci likitan hakora sau biyu a Florida a wannan shekarar.

Lokacin da kurji ya fitowa Donald Trump
Wani kurji da ya fitowa Donald Trump a wuya a farkon 2026. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tun bayan komawarsa Fadar White House a shekarar 2025, matsalolin lafiya da ake iya gani da kuma hasashe kan lafiyarsa sun sa Fadar White House ta fara fitar da karin bayanai game da yanayin lafiyarsa.

Batun sa hoton Trump a kudi

A wani rahoton, mun kawo muku cewa gwamnatin Donald Trump na shirye-shiryen buga sabuwar takardar kudi ta $250 wadda za ta kasance da hotonsa idan ’yan majalisa suka amince.

Dokar tarayya ta Amurka ta haramta buga kudi masu dauke da hoton mutumin da ya ke raye, amma abokan siyasar Trump a majalisa sun gabatar da kudirin doka da zai ba da damar hakan.

Kakakin ma’aikatar baitulmalin Amurka ya shaida cewa hukumar na gudanar da shirye-shiryen da suka dace da kuma cikakken nazari dangane da kudirin dokar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng