Olu Jacobs: Abubuwan Sani game da Fitaccen Jarumin Fim da Allah Ya Yi wa Rasuwa

Olu Jacobs: Abubuwan Sani game da Fitaccen Jarumin Fim da Allah Ya Yi wa Rasuwa

Tauraruwar jarumi kuma mai shirya fina-finai, Oludotun Baiyewu Jacobs, wanda aka fi sani da Olu Jacobs ta haska ba masana'antar Nollywood kadai ba, har a wasu kasashe na duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Yana daga cikin ’yan wasan kwaikwayo na Najeriya da sana’arsu ta shafi nahiyoyin duniya, kuma ya yi fice wajen isar da sakon da ke cikin nau’o’in labarai daban-daban.

Olu Jacobs.
Jarumin Nollywood da Allah ya yi wa rasuwa, Olu Jacobs Hoto: Olu Jacobs
Source: Instagram

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an haifi Jacobs a Kano, iyayen sun fito daga Egba Alake, kuma tun yana ƙarami yake da sha’awar wasan kwaikwayo kafin ya tafi Birtaniya domin neman horo na musamman.

Jacobs ya yi rayuwa a Birtaniya da Najeriya

Ya fara ne daga wasan kwaikwayo a makaranta da dandali a Najeriya zuwa makarantar Royal Academy of Dramatic Arts da ke Landan, shirye-shiryen talabijin na Birtaniya da fina-finai na ƙasa da ƙasa, kafin ya dawo gida Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Fitaccen jarumin fim da ya zauna a Kano ya riga mu gidan gaskiya

A tsawon sana’arsa da ta ɗauki shekaru da dama, Jacobs ya kafa suna wajen iya taka rawar gani a dandali, talabijin da fina-finai.

Ya fito a fina-finan Nollywood sama da 120, sannan ya samu manyan lambobin yabo a masana’antar, ciki har da Africa Movie Academy Award na gwarzon jarumi a babbar rawa.

Abubuwan da ya kamata ku sani

Bayan tabbatar da rasuwarsa yana da shekaru 84, Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwan da ya kamata a sani game da rayuwa, sana’a da gadon ɗaya daga cikin fitattun jaruman Najeriya.

1. Yarintarsa a jihar Kano

An haifi Olu Jacobs a watan Yuli na shekarar 1942 a Kano, duk da cewa iyayensa sun fito ne daga Egba Alake a Jihar Ogun ta yanzu.

Ya yi shekarunsa na farko a Kano, inda ya halarci Holy Trinity School. A lokacin karatunsa, ya shiga ƙungiyoyin mahawara da wasan kwaikwayo na makarantar, waɗanda suka kara kwadaita masa sha’awar harkar fim.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Farashin litar fetur na iya haura N5000 bayan zaben 2027, an gano dalili

2. Haɗuwarsa da Hubert Ogunde

Tunanin Jacobs na mayar da wasan kwaikwayo sana’a ya samu tasiri da kwarin gwiwa ne daga haɗuwarsa da fitaccen ɗan wasan kwaikwayo na Najeriya, Cif Hubert Ogunde.

A lokacin da yake matashi a Kano, Jacobs ya halarci ɗaya daga cikin bukukuwan wasan kwaikwayo na shekara-shekara na Ogunde a Colonial Hotel.

Wannan bikinnda ya halarta ya sa ya ɗauki wasan kwaikwayo da muhimmanci. Ba da daɗewa ba bayan haka, ya samu bizar tafiya zuwa Ingila domin neman horo na musamman a fannin wasan kwaikwayo.

3. Karatun Olu Jacobs a RADA

A Birtaniya, Jacobs ya yi karatu a shahararriyar makarantar nan mai suna Royal Academy of Dramatic Arts (RADA) da ke Landan, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Horarwar da ya samu a makarantar ta zama ginshiƙin sana’arsa, wadda da farko ta kai shi ga wasan kwaikwayo da shirye-shiryen talabijin a Birtaniya kafin ya zama sananne sosai a Najeriya.

4. Farkon sana’arsa a Birtaniya

Kara karanta wannan

Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu

Ɗaya daga cikin farkon rawar da Jacobs ya taka a dandali ita ce a shekarar 1972, lokacin da ya taka rawar The Boy a wasan A Taste of Honey a sabon Crucible Theatre da aka buɗe a Sheffield.

Sana’arsa a dandali ta nuna irin iya canza salo da rawar da yake da ita, tare da buɗe masa ƙofofin samun ƙarin damammaki a wasan kwaikwayo da talabijin na Birtaniya.

Jacobs
Fitaccen jarumi kuma mai shirya fina-finai a Nollywood, Olu Jakobs Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

5. Daga talabijin zuwa fina-finai

A shekarun 1970, Jacobs ya fito a shirye-shiryen talabijin da jerin shirye-shiryen Birtaniya da dama, ciki har da The Goodies, Till Death Us Do Part, Barlow at Large, The Venturers, Angels, 1990, The Tomorrow People da The Professionals.

A shekarar 1978, ya taka rawar Shugaba Mageeba a fim din Night and Day, wasan da aka shirya daga wani aikin marubucin wasan kwaikwayo Sir Tom Stoppard.

A shekarun 1980, ayyukansa a fina-finan ƙasa da ƙasa sun ƙaru. Ya fito a fina-finai ciki har da The Dogs of War, Baby: Secret of the Lost Legend da Pirates na Roman Polanski.

6. Dawowarsa Najeriya

Bayan shekaru yana aiki a ƙasashen waje, Jacobs ya dawo Najeriya a shekarar 1990.

Kara karanta wannan

Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka

Ɗaya daga cikin fitattun rawar da ya taka a farkon dawowarsa ita ce a shirin binciken laifuka na NTA mai suna The Third Eye, wanda ya taimaka wajen sake kusantar da shi da masu kallon talabijin a Najeriya.

Dawowarsa ta zo ne a daidai lokacin da abin da daga baya aka sani da Nollywood ke fara samun bunƙasa da yaɗuwa.

7. Sana’ar fim a Nollywood

Jacobs ya ci gaba da kafa kansa a matsayin ɗaya daga cikin jaruman da aka fi sani a sinimar Najeriya.

Ya fito a fina-finan Nollywood sama da 120, inda ya taka rawar da ta nuna iyawarsa da kuma kwarjinin da yake da shi a gaban kyamara.

Ayyukansa sun jawo masa sanun tallace-tallacen talabijin, inda ya fito a tallan wasu kamfanoni ciki har da Ribena da Binatone.

8. Manyan lambobin yabon da ya samu

Gudunmawar da Jacobs ya bayar wajen wasan kwaikwayo ta sa ya samu manyan lambobin yabo da karramawa da dama.

Daga cikinsu akwai:

  • 2007: Africa Movie Academy Award na gwarzon jarumi a babbar rawa
  • 2011: Karramawar ƙasa ta Member of the Order of the Federal Republic (MFR)
  • 2013: Industry Merit Award a Africa Magic Viewers’ Choice Awards
  • 2016: MAA Lifetime Achievement Award
  • 2021: Lifetime Achievement Award a Africa International Film Festival (AFRIFF)

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso zai ragargaji Atiku da Tinubu a zaben 2027 a Kano

9. Ya auri Jaruma Joke Silva

Jacobs ya auri ’yar wasan kwaikwayo, JarumanJoke Silva a shekarar 1989. Ma’auratan suna da ’ya’ya biyu kuma sun zama ɗaya daga cikin fitattun jaruman da suka yi aure a Najeriya.

Olu Jacobs.
Jarumin Nollywood, Olu Jacobs tare da mai dakinsa, Jaruma Joke Silva a wurin taron ba da lambar yabo ta Africa Magic Hoto: Joke Silva
Source: Facebook

A wani lokaci, Jacobs ya bayyana dalilin da ya sa Silva ta ci gaba da amfani da sunanta na sana’a, inda ya ce ita mutum ce da ta riga ta kafa kanta a matsayin jarumar fim kafin aurensu.

Ra’ayinsa shi ne cewa aure bai kamata ya goge sunan sana’ar da ta riga ta gina a matsayin Joke Silva ba.

10. Gina kamfanin Lufodo Group

Baya ga sana’o’insu na wasan kwaikwayo, Jacobs da Silva sun gina kasuwanci a fannin masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire.

Tare suka kafa kuma suka gudanar da Lufodo Group, wani kamfanin kafafen yaɗa labarai da ke da harkoki a fannin shiryawa da rarraba fina-finai.

Kamfanin ya kuma ƙunshi Lufodo Academy of Performing Arts, abin da ke nuna rawar da ma’auratan suka taka ba kawai wajen nishaɗi ba, har ma wajen bunƙasa baiwar masu sha’awar wasan kwaikwayo.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi babban rashi, shugaban hukumar NIA na farko ya riga mu gidan gaskiya

11. Jita-jitar rasuwarsa a 2021

Jaridar Leadership ta rahoto cewa an jima ana yada jita-jitar rasuwar jarumin, amma wacce ta fi shahara ita ce ta 2021, inda jita-jita ta yaɗu a kafafen sada zumunta cewa Jacobs ya rasu.

Daga baya aka tabbatar da cewa labarin ba gaskiya ba ne bayan da ya bayyana a taron AFRIFF a watan Nuwamban 2021, inda aka karrama shi da Lifetime Achievement Award.

Lamarin ya sake nuna matsalar yaɗa rahotannin rasuwar fitattun ’yan Najeriya ba tare da tabbatar da su ba.

Olu Jacobs.
Jarumin masana'antar shirya fina-finai ta Najeriya, Marigayi Olu Jacobs Hoto: Olusoji Jacobs
Source: Instagram

12. Shekarunsa na ƙarshe

A shekarun baya, batun lafiyar Jacobs ya zama abin tattaunawa a bainar jama’a. Matarsa, Joke Silva, ta bayyana a wata hira da Chude Jideonwo cewa jarumin yana fama da wata cuta, Lewy body dementia.

Duk da raguwar fitowarsa a bainar jama’a, Jacobs ya ci gaba da kasancewa muhimmin mutum a tarihin harkar nishaɗin Najeriya, tare da ci gaba da samun yabo da karramawa saboda gudunmawar da ya bayar ga masana’antar.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bindige babban manajan banki a Najeriya har ya mutu

13. Rasuwarsa yana da shekaru 84

Olu Jacobs ya rasu ranar Larabaa, 16 ga Satumba, 2026 yana da shekaru 84. Ɗansa, Olusoji Jacobs, ne ya sanar da rasuwar a Instagram.

A sanarwar rasuwarsa, iyalan sun bayyana shi da “Zakin Lufodo”, tare da roƙon masu rubutu a yanar gizo da masu tasiri a kafafen sada zumunta da su mutunta sirrin iyalan a wannan lokaci.

Iyalan jarumin fim na tsaka mai wuya

A wani labarin, kun ji cewa Iyalan marigayi fitaccen jarumin Nollywood, Mr Ibu, sun bayyana irinNhalin da suka shiga bayan mutuwarsa.

Matarsa da 'ya'yansa uku sun roki ‘yan Najeriya su tallafa musu domin biyan kudin makaranta, haya da sauran muhimman bukatun rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262