Surutu Ya Kare, An Yanke Wa Matashi Hukunci kan Taba Martabar Annabi Muhammad SAW

Surutu Ya Kare, An Yanke Wa Matashi Hukunci kan Taba Martabar Annabi Muhammad SAW

  • Anojan Sivarasa, ɗan Sri Lanka mai shekara 24, na fuskantar hukuncin kisa a Saudiyya bayan an same shi da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW
  • Mahaifiyarsa ta roƙi a yi wa ɗanta afuwa, tana mai cewa ta na son a dawo mata da shi amma har yanzu babu alamun hakan
  • Lamarin ya tayar da hankula a Sri Lanka, inda ƙungiyoyin farar hula da jami’an gwamnati ke ƙoƙarin ganin an ceto shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudiyya - Wata kotun ɗaukaka ƙara a Saudiyya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Anojan Sivarasa, matashi ɗan kasad Sri Lanka mai shekara 24.

Kotun ta yanke masa wannan hukunci ne bayan an same shi da laifin yin ɓatanci ga addinin Musulunci da Annabi Muhammad SAW a wani saƙon da ya wallafa a kafar sada zumunta.

Kara karanta wannan

Shugaban Amurka ya ɗora laifin abin da ke faruwa a Faransa kan addinin Musulunci

Anojan Sivarasa
Matashi dan shekara 24 da aka yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya, Anojan Sivarasa Hoto: Anojan Sivarasa
Source: Facebook

BBC Hausa ta ruwaito cewa mahaifiyarsa, Rasamanickam Yogalakshmi, ta roƙi a yi wa ɗanta afuwa cikin kuka, tana mai cewa: “Don Allah ku yafe masa, ku dawo mana da shi.”

Lamarin ya tayar da hankula a faɗin Sri Lanka, inda ƙungiyoyin farar hula suka gabatar da ƙorafi. Jam’iyyun siyasa da hukumomin gwamnati da dama sun haɗa kai wajen ƙoƙarin ganin an yi masa afuwa.

Dangin matashin sun nemi bayani

Iyalin matshin sun ce har yanzu ba su samu wani ƙarin bayani kan halin da yake ciki ba tun ranar 28 ga Satumba, 2026, amma gwamnatin Sri Lanka ta kwantar masu da hankali.

Har yanzu dai Saudiyya ba ta sanar da ranar zartar da hukuncin kisa kan matashin ba yayin da kasar Sri Lanka ta ce tana kokarin warware lamarin ta hanyar diflomasiyya.

Bayanai sun nuna cewa an gurfanar da Anojan ne bayan wata takaddama da ta taso a shafukan sada zumunta sakamakon wani lamari da ya faru yayin wani aikin ibada na mabiya addinin Hindu a Sri Lanka.

Kara karanta wannan

Dan majalisar tarayya da ya yi wa Obi shagube kan zabe ya sha ihun 'ba mu yi'

Yadda matshin ya yi kalaman batanci

A ƙarshen watan Yuni, wani bidiyo da ke nuna wani matashi Musulmi yana dukan wani kare da ke bin mabiya addinin Hindu ya yaɗu sosai a shafukan sada zumunta.

Lamarin ya haifar da muhawarar addini a intanet. A yayin muhawarar, wani mai amfani da shafin ya yi kalaman ɓatanci ga wani abin bautar mabiya addinin Hindu.

Saudiyya.
Yarimar kasar Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud Hoto: Bastien Ohier
Source: Twitter

Hakan ya sa Anojan ya mayar da martani da harshen Tamil, inda ya yi kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW amma daga bisani ya gode, sai dai wasu sun riga sun dauki hoton abin da ya fada

Bayan haka ne aka kai batun ga kamfanin da yake yi wa aiki da kuma hukumomin Saudiyya, lamarin da ya kai ga kama shi a watan Yulin da ya gabat, har aka yanke masa hukuncin kisa a watan Satumba.

Saudiyya ta kama dubban baƙin haure

Kun ji cewa hukumomin tsaron Saudiyya sun kama mutane 14,782 da ake zargi da karya dokokin zama da shigowa kasar ba bisa ka'ida ba cikin mako guda.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar ta ce an gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro da hukumomin gwamnati tsakanin ranar 10 zuwa 16 ga Satumba, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262