Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Shugaban Hukumar NIA na Farko Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Shugaba na farko a Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa, NIA, Albert Horsfall, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya
- Iyalansa sun ce ya rasu cikin kwanciyar hankali bayan ya yi rayuwa mai cike da nasarori da hidima ga Allah, iyali, al’umma, Jihar Rivers da Najeriya
- Horsfall ya yi aiki a hukumomin tsaro da dama, ciki har da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya watau DSS
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa, NIA, na farko a tarihin Najeriya, Albert Horsfall ya riga mu gidsn gaskiya yana da shekaru 84 da haihuwa.
Ɗansa, Donald Horsfall, ne ya sanar da rasuwar mahaifin du a wata sanarwa da ya fitar a madadin iyalan gidansu.

Source: Facebook
Tsohon shugaban NIA ya mutu
The Cable ta ruwaito vewa iyalin marigayin sun ce Horsfall ya rasu ne “cikin kwanciyar hankali bayan ya yi rayuwa mai cike da nasarori da tasiri, wadda ya sadaukar ga Allah, iyali, al’umma, Jihar Rivers da Najeriya”.
Sun ce a lokacin rayuwarsa, Horsfall ya yi wa Najeriya hidima da “ƙwazo na musamman, gaskiya da kishin ƙasa."
Haka zalika iyalan marigayin sun bayyana cewa ya bar gado mai ɗorewa na shugabanci, hikima da hidimar da babu son kai a cikinta.
Iyalansa sun fadi ayyukan da ya yi
Sanarwar ta ce:
“A matsayinsa na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Jihar Rivers kuma dattijo mai daraja a matakin ƙasa, Cif Horsfall ya bayar da gagarumar gudummawa wajen ci gaban Jihar da ƙasar nan baki daya.
“Shawarwarinsa, ƙarfin halinsa da jajircewarsa wajen tabbatar da adalci, zaman lafiya da shugabanci na gari sun sa shugabanni da ’yan ƙasa na mataki daban-daban suka girmama shi.”
Iyalin sun ce duk da cewa suna jimamin wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba, suna samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali daga irin rayuwar ta musamman da ya yi da kuma tasirin da ya bari a tarihi.
Sun ƙara da cewa tunaninsa zai ci gaba da ƙarfafa duk waɗanda suka samu damar saninsa da kuma amfana da dimbin iliminsa, ƙwarewarsa da tausayi.

Source: Original
Takaitaccen tarihin marigayin
An haifi Horsfall ranar 22 ga watan Disamba, 1941. Ya yi aiki a hukumomin tsaron ƙasar, ciki har da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar Sabis ɗin Tsaron Jiha, DSS.
Horsfall ya kuma taɓa zama shugaban tsohuwar Hukumar Raya Yankunan Masu Hakar Man Fetur da Ma’adanai, OMPADEC, da kuma kwamitin gyaran zamantakewa na Jihar Rivers.
Babban jigo a PDP, Orbih ya mutu
A wani labarin, kun ji cewa an tabbatar da rasuwar daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP, Cif Daniel Osi Orbih a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, 2026.
Iyalan marigayin ne suka sanar da rasuwar cikin kaduwa da mika wuya.ga kaddarar Allah, a wata sanarwa da suka fitar.
Iyalan marigayin sun roki ’yan uwa, abokai da masoya da su ci gaba da tunawa da su a cikin addu’o’insu yayin da suke cikin jimamin wannan babban rashi.
Asali: Legit.ng

