"Ba Kamar Buhari ba"; Peter Obi Ya Yi Maganar Yakar Cin Hanci a Najeriya

"Ba Kamar Buhari ba"; Peter Obi Ya Yi Maganar Yakar Cin Hanci a Najeriya

  • Peter Obi ya ce zai jagoranci yaƙi da cin hanci da rashawa da kansa idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya a 2027
  • Obi ya ce yaƙi da rashawa zai fara ne da tabbatar da cewa shi da iyalinsa ba su shiga harkar cin hanci ba
  • Dan takarar NDC ya ce zai dawo da tallafin fetur, amma zai kawar da cin hancin da ya ce ke lalata tsarin tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), ya yi magana kan yaki da cin hanci da rashawa.

Peter Obi ya ce zai cika alkawarinsa na yaƙi da cin hanci da rashawa idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya.

Peter Obi ya yi magana yakar cin hanci
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da Sashen Afirka na BBC da aka wallafa ranar Talata, 6 ga watan Oktoban 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan

Da gaske akwai hujjar Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasa na 2023?

Obi ya ce zai jagoranci yaƙi da rashawa

Tsohon gwamnan Anambra ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai iya magance cin hanci da rashawa kamar yadda ya yi alkawari ba, saboda bai jagoranci lamarin da kansa ba.

“Shi bai kasance mai jagorantar lamarin ba. Bambancin shi ne wannan: ni zan jagoranci yakin,” in ji Obi.

Ya ce matakin farko wajen rage cin hanci da rashawa shi ne shugaban ƙasa ya tabbatar da cewa shi da iyalinsa ba sa shiga irin wannan harkar.

“Idan ba ka sata, ba ka da hannu a ciki, matarka da iyalinka ba su da hannu a ciki, za ka rage shi da kashi 50,” in ji shi.

Obi ya soki shirin 'yan adawa na ɗan takara ya janye

Obi ya kuma ce gabanin zaɓen 2027, haɗakar ’yan adawa ya kamata ta yi watsi da tunanin cewa wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya janye domin goyon bayan wani.

Kara karanta wannan

Umahi: Minista ya raba gardama, ya fadi abin da zai sa Tinubu ya zarce a 2027

A cewarsa, ya kamata ’yan adawa su fi mayar da hankali wajen ƙara yawan masu zaɓe maimakon neman ɗan takara ya janye.

“Ba buƙatar ɗan takara ya janye. A zaɓen da ya gabata, Sokoto na da sama da masu rajistar zaɓe miliyan biyu. Ya kamata ’yan adawa su tattauna kan yadda za a ƙara samun wasu mutane miliyan 25 su fito su yi zaɓe. Ba mu buƙatar ɗan takara ya janye,” in ji shi.

Ya ce zai dawo da tallafin fetur

Da aka tambaye shi ko zai dawo da tallafin fetur idan ya zama shugaban ƙasa, Obi ya amsa da cewa zai yi hakan, amma ba tare da barin cin hanci da rashawa ya mamaye tsarin ba.

“Eh, amma ba tare da cin hancin da ke tattare da shi ba. Shi ya sa na ce zan kawar da cin hanci da rashawa, sannan in ci gaba da tallafin,” in ji shi.
Peter Obi ya ce zai yaki cin hanci da rashawa
Dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Peter Obi ya yi magana kan zaben 2023

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, ya ce babu wata hujja da zai gabatar da za ta tabbatar da ikirarinsa na cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Duk da haka, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ci gaba da cewa ya yi amanna cewa shi ne ya lashe zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng