An yi wa Jaruma Fati Muhammad Rubdugu kan Tallata Tinubu
- Jarumar Kannywood Fati Muhammad ta sha rubdugu bayan ta yi kira ga masoyanta da su zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Wasu daga cikin mutanen da suka mayar da martani sun soki matakin nata, yayin da wasu suka yi magana kan tsadar rayuwa da matsalar tsaro
- Martanin ya biyo bayan wani saƙo da jarumar ta wallafa a ranar Litinin, inda ta ce: “Masoya na, don Allah ku zaɓi Tinubu” yayin da ake shirin zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jarumar Kannywood, Fati Muhammad, ta fuskanci martani mai zafi daga wasu masu amfani da kafar sada zumunta bayan ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan fim, musamman wadanda suke tafiya tare da Dauda Kahutu Rarara ke fitowa suna tallata Bola Tinubu.

Source: Facebook
Jarumar ta wallafa saƙon da ke kira ga masoyanta da su zaɓi Tinubu, lamarin da ya jawo muhawara a sashen sharhi na shafinta na Facebook.
An caccaki Fati Muhammad
Daga cikin waɗanda suka mayar da martani akwai Naziru Alhassan, wanda ya ce su kam za su zaɓi Atiku Abubakar a zaben 2027.
Shi ma Abba Galke ya yi tsokaci kan goyon bayan Tinubu, inda ya ce:
“A bisa wani dalili? Ɗaya daga cikin abubuwan ban sha’awa shi ne cewa goyon bayan Tinubu ba zai hana ku sayen man fetur kan N1,500 ko N1,450 a wasu wurare ba.
"Haka kuma ba zai hana ku biyan haraji ba, kuma ba zai hana ku fuskantar rashin tsaro a ƙauyenku ba. Don haka masu goyon bayan Tinubu ku ci gaba da goyon bayan Tinubu.”
Martani kan tsadar rayuwa
Abdoul Ap ya mayar da martani cikin gajeren saƙo, inda ya ce:
“Banga ubanda ya isa ya hadani da Allah ya cuceni ba. Sha sha sha kawai.”
D J Auwal Kaz kuma ya ce:
“Zaɓimmu ai bana Allah ba ne, adinga aiki da ilimi. Idan muka zaɓe shi Allah kuma ya ƙi shi fa, za ki yi?”
Hajiya Megwanjo kuwa ta rubuta:
“Kaka ai yanzu an gama yayinki.”
Korafi kan halin da kasa ke ciki
Safeenat Abatcha ta ce ba za ta zaɓi Tinubu ba, inda ta bayyana damuwarta kan yadda take kallon halin da ƙasar ke ciki.
Ta ce:
“Ba za a zaɓe shi ba, kawai saboda jin daɗinku na lokaci kaɗan mu kuma mu halakar da kanmu ko? Ban taɓa ganin mulkin zalunci irin na Tinubu ba. Abin da ya rage kawai saura a bi gida-gida ana kashe mu, muna ji muna gani.”
Ahmad Nagudu kuma ya ce idan ana son mutane su zaɓi shugaban ƙasa, ya kamata a nuna musu abin da zai amfani al’umma na tsawon shekaru huɗu.
Ya ce:
“Abin da aka ba ki ki fito ki raba wa mutane, kuma wanda zai ishe su duk wata bukatarsu na tsawon shekaru huɗu na mulkin, a nan ne za ki ce su zaɓe shi, sai su zaɓe shi ɗin da hujja.”
Abdulrahman Mohammed ya ce:
“Allah ya sawwaƙe, ke ma saboda ba ki da manufa ne ya sa kike wannan maganar. Tinubu kam sai ya koma Legas shekara mai zuwa, in Allah ya yarda.”

Source: Facebook
Ibrahim Waziri kuwa ya lura da yawan martanin da aka yi wa saƙon, inda ya ce:
“Kai toh fa, za a samu matsala. Kwamen 3,000 amma babu ɗaya na alheri wa shugaban ƙasa. Lalle an sha wahala, gaskiya a yi gyara.”
Abdullahi Muhammad Hassan ya ce:
“Ki kawo abin da aka ba ki mu raba.”
Naseer Rabi’u shi ma ya ce:
“Masoyanki ai ba yayanki ba ne, bare ki ce za ki sa su yi abin da ba sa so. To, amma dai sanda kike amsar kuɗinki na tallar Tinubu, wa kika ba wa?”
An nemi lakada Rarara a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu fusatattun matasa sun nuna rashin amincewarsu da waƙar da Dauda Kahutu Rarara ya yi ƙoƙarin gabatarwa a Monaliza Park da ke Abuja.
Lamarin ya faru ne a wani taron bikin ranar samun ’yancin Najeriya, inda rahotanni suka ce wasu daga cikin mahalarta sun yi ihu tare da jefa abubuwa zuwa wajen dandalin.
Rahotannin sun ce jami’an tsaro sun shiga tsakani domin tarwatsa jama’ar tare da fitar da mawaƙin daga wurin, sai dai babu wani bayani a hukumance da ya tabbatar da ko an kama wasu mutane.
Asali: Legit.ng



