An Saki Sunayen Sojoji da Mutum 25 da Suka Rasu a Hadarin Jirgin Soji a Ondo

An Saki Sunayen Sojoji da Mutum 25 da Suka Rasu a Hadarin Jirgin Soji a Ondo

  • Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, NAF, ta tabbatar da mutuwar mutane 25 da ke cikin jirgin ATR-42 mai lamba NAF 931 da ya yi hatsari a Igbokoda, jihar Ondo
  • Mutanen sun kunshi ma’aikatan jirgin biyar da fasinjoji 20, inda NAF ta ce har yanzu ba a samu wani mutum da ya tsira daga hadarin ba
  • Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasu tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan hadarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, NAF, ta fitar da sunayen mutum 25 da suka rasu a hadarin jirgin ATR-42 mai lamba NAF 931 a yankin Igbokoda na jihar Ondo.

NAF ta ce jirgin yana dauke da mutane 25, wadanda suka hada da ma’aikatan jirgi biyar da fasinjoji 20, a lokacin da hadarin ya afku yayin da yake kan wata tafiya daga Benin zuwa Legas.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga aikin da ba nasa ba, ya fadi abubuwa 3 da suka jawo hatsarin jirgin sojoji

Jirgin da ya yi hadari a Ondo
Wajen da jirgin NAF ya yi hadari. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Mutum 25 sun mutu

A sakon da NAF ta wallafa a Facebook, Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan jami’an da fasinjojin da suka rasa rayukansu.

Ya bayyana hadarin a matsayin babban abin bakin ciki ga rundunar da kasa baki daya, tare da tabbatar wa iyalan mamatan cewa NAF za ta ci gaba da ba su cikakken goyon baya a wannan lokaci na jimami.

Rundunar ta ce an fara aikin neman wadanda ke cikin jirgin da ceto nan take bayan faruwar hadarin, tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa.

Ga sunayen ma’aikatan jirgin

Mutum biyar da ke cikin ma’aikatan jirgin su ne:

  1. Squadron Leader MI Aburime – Kyaftin din jirgi
  2. Squadron Leader AP Man-Ugwueje – Mataimakin kyaftin
  3. Flight Lieutenant IS Bako – Mataimakin kyaftin
  4. Warrant Officer Abubakar A – Masanin gyaran jirgi
  5. Corporal Uguru HC – Masanin gyaran jirgi

Kara karanta wannan

Iyalan sojoji da dukkan dakarun da ke cikin jirgin sojin da ya yi hadari sun mutu

Ga sunayen fasinjojin jirgin

Fasinjoji 20 da suka rasu su ne:

  1. Flight Lieutenant TL Lazarus
  2. Flight Lieutenant M Akinloye
  3. Flying Officer IM Adeshina
  4. Master Warrant Officer Onwuka F
  5. Master Warrant Officer Matini BA
  6. Warrant Officer Nuhu FS
  7. Flight Sergeant James RB
  8. Flight Sergeant Mohammed AI
  9. Sergeant Ani AE
  10. Sergeant Izibenikien SI
  11. Sergeant Alafuka C
  12. Sergeant Mbadugha AN
  13. Lance Corporal Ugwuba FC
  14. Lance Corporal Eledan GE
  15. Mrs Ezeh Nneka
  16. Godstmine Tarabina
  17. Joy Micheal
  18. Sunday Micheal
  19. Ukeme David
  20. Gideon Omotola
Jirgin NAF da ya fado
Karafunan jirgin NAF da ya yi hadari a Ondo. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

NAF ta ce babu wani mutum da aka samu da rai daga cikin mutanen da ke cikin jirgin.

Tinubu ya ayyana zaman makoki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya ayyana kwana uku na zaman makoki na kasa domin karrama jami’an Sojojin Sama da suka mutu a hadarin jirgin a Ondo.

Tinubu ya kuma bayar da umarnin sauke tutocin Najeriya zuwa kasa a fadin kasar domin nuna girmamawa ga wadanda suka rasu.

Shugaban kasar ya umarci rundunar Sojojin Sama da ta fara bincike cikin gaggawa domin gano musabbabin hadarin tare da daukar matakan hana sake faruwar irin wannan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng