'Yan Ta'adda Sun Bindige Babban Manajan Banki a Najeriya har Ya Mutu

'Yan Ta'adda Sun Bindige Babban Manajan Banki a Najeriya har Ya Mutu

  • Wani manajan reshen bankin Polaris, mai suna Ossy, ya rasa ransa bayan wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane sun harbe shi
  • Lamarin ya faru ne a yammacin Lahadi, lokacin da manajan bankin, wanda ke zaune a Owerri, ya kai ’ya’yansa jami’ar FUTO da suke karatu
  • A yayin harin, ’yan bindigar da suka tsere sun kuma yi awon gaba da wasu ɗalibai mata biyu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da binciken lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Owerri – Wani manajan reshen bankin Polaris, wanda aka bayyana da suna Mista Ossy, ya mutu bayan wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane sun harbe shi a harabar Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri, Jihar Imo.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 6 ga Satumba, 2026, yayin da manajan bankin ke kai ’ya’yansa da suke karatu a jami’ar.

Kara karanta wannan

Ana zargin Bello Turji da kai mummunan hari a Sokoto da aka sace mutane 40

Taswirar jihar Imo
Taswirar jihar Imo a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Original

An tabbatar da rasuwar manajan

Punch ta wallafa cewa shugaban sashen sadarwa na bankin, Rasheed Bolarinwa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Bankin ya bayyana cewa ma’aikacin nasa yana kai ’ya’yansa jami’ar ne lokacin da wasu ’yan bindiga suka tare shi tare da kai masa hari.

Ya kara da cewa ’ya’yan mamacin sun samu damar tserewa daga wurin, amma shi bai samu damar tsira ba.

Bankin ya ce:

“Mun yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar Manajan Reshen Bankinmu, kuma muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa, abokansa, abokan aikinsa da sauran masoyansa a wannan lokaci mai wahala.
“Muna sane cewa hukumomin tsaro da abin ya shafa suna gudanar da bincike kan lamarin, kuma muna fatan za a gano cikakken abin da ya faru.
“Muna ci gaba da yi wa iyalan mamacin addu’a, tare da roƙon jama’a da su bar hukumomin da abin ya shafa su kammala bincikensu.”
Sufeton 'yan sanda, Tunji Disu
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

FUTO ta yi magana

Hukumar gudanarwar Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri, FUTO, ta tabbatar da cewa an harbe wani baƙo har lahira a cikin harabar jami’ar.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki da yan sanda suka tabbatar da hari kan ayarin motocin Peter Obi

A wata sanarwa da Magatakardar jami’ar, Chinonso Uba, ya sanya wa hannu, jami’ar ta ce an kuma yi garkuwa da ɗalibai mata biyu a yayin harin.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 6 ga Satumba, 2026, inda aka harbe wani baƙo a jami’ar har lahira.

Jami’ar ta ce hukumomin tsaro na gudanar da bincike, yayin da ita ma take aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin ganin an ceto ɗaliban biyu cikin aminci.

An kashe 'yan ta'adda a Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa jiragen saman soji sun kai hare-hare kan wasu da ake zargi da ’yan ta’adda a yankin Yankuzo na Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Harin ya faru ne a yammacin Litinin a ƙarƙashin Operation Fansan Yanma, inda rahotanni suka ce jiragen saman soji guda biyar ne suka shiga aikin haɗin gwiwa kan mayakan da ake zargi da ta’addanci.

An ruwaito cewa mayaka da dama sun mutu, duk da cewa ba a tabbatar da adadin waɗanda suka rasa rayukansu ba. Daga cikin waɗanda aka ce an kashe akwai wani ɗan ta’adda mai suna Isiya Gurgu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng