'Yan Ta'adda Sun Tare Babbar Hanya a Zamfara, an Yi Awon Gaba da Matafiya
- ’Yan bindiga sun tare hanyar Gusau-Sokoto a Kwanar Sado, kusa da Talata Mafara, tare da sace aƙalla matafiya 30
- Shaidu sun ce ’yan bindigan sun tare motoci uku da yammacin Litinin, inda suka tafi da duk fasinjojin da ke cikin motocin
- Mazauna yankin sun nemi gwamnati ta tura jami’an tsaro zuwa wuraren da ake yawan samun hare-hare domin kare matafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - ’Yan bindiga sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto a Jihar Zamfara, inda suka sace aƙalla matafiya 30 a sabon harin da aka kai kan hanyar.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru da yammacin Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026 da misalin ƙarfe 7:40 na dare, a Kwanar Sado, mai tazarar ’yan kilomita daga garin Talata Mafara.

Source: Original
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ’yan bindigar sun kafa shinge a hanyar tare da tare motoci uku, cewar rahoton jaridar Leadership.
A cewarsa, maharan sun fitar da fasinjojin daga motocin sannan suka tafi da su cikin daji.
An sace dukkan fasinjojin motocin
Wani ganau, wanda ke sana’ar Achaba kuma ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce an sace dukkan fasinjojin da ke cikin motoci ukun.
Ya ce wasu matafiya sun tsaya bayan an yi musu alamar tsayawa tare da sauran motocin da ke kan hanyar.
“Mun tsaya bayan wani ya yi mana alama tare da sauran motocin, har sai da wata motar soja ta zo daga Mafara ta buɗe hanya, amma a lokacin an riga an tafi da fasinjojin."
“Lokacin da muka isa wurin, mun ga motoci uku da dukkan ƙofofinsu a buɗe.” In ji shi.
An ce an hango ’yan bindigan kafin harin
Wani ɗan sa-kai daga Talata Mafara ya ce an riga an gargadi masu ababen hawa da kada su bi hanyar da yamma bayan an hango ’yan bindiga suna dawowa daga wajen wani bikin aure a yankin Sado.
A cewarsa, an hango maharan da misalin ƙarfe 4:00 na yamma suna dawowa daga Sado, inda suka halarci bikin auren wani ɗan bindiga.
“An hango ’yan bindigar da misalin ƙarfe 4:00 na yamma suna dawowa daga Sado, inda suka halarci bikin auren wani ɗan bindiga. Wataƙila sun ɓuya a bayan wuraren fasa dutse guda biyu da ke yankin, suka jira lokacin dare.”
Hanyar Gusau-Sokoto na fuskantar barazana
Ɗan sa-kan ya ce hanyar Gusau-Sokoto ta zama ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi zama haɗari ga matafiya, musamman da yamma da kuma safiyar sassafe.
Ya ƙara da cewa ’yan bindigar na da sansanoni da dama a kusa da madatsar ruwa ta Bakalori da ke Talata Mafara.
Wannan sabon harin ya zo ne bayan jerin hare-haren da aka kai kan hanyar a baya-bayan nan, jaridar Daily Trust ta kawo labaran.
A makon da ya gabata, ’yan bindiga sun tare hanyar a kusa da ƙauyen Kwaren Kirya da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Maru, inda suka sace sama da matafiya 26.
An ce maharan sun sace mutanen ne daga wata motar fasinja mai kujeru 18 da kuma wata motar kirar Volkswagen Golf.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun aika sako a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindigar da suka yi garkuwa da malaman addinin Musulunci shida a jihar Zamfara sun aiko da sako kan kudin fansa.
'Yan bindigan wadanda suka sace malaman sun bukaci a biya su N30m a matsayin kudin fansa domin sakin su.
Asali: Legit.ng


