Magana Ta Fito, An Ji Abin da Ya Faru da Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya Kwanaki 5 kafin Ya Rasu
- Olu Ogogo ya yi karin haske kan yanayin rashin afiyar marigayi jarumin Nollywood Taiwo Hassan kwanaki biyar kafin rasuwarsa
- Ya bayyana cewa an gano jarumin na fama da cutar kansa a lokacin da ake gudanar da gwaje-gwaje a asibiti
- Rahoto ya nuna cewa Jarumi Taiwo Hassan ya rasu yana da shekaru 66 bayan fama da cutar kansa ta mataki na huɗu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Azeez Ayinde Onifade, wanda aka fi sani da Olu Ogogo kuma babban mataimaki ne ga marigayi jarumin Nollywood, Taiwo Hassan, ya bayyana yanayin da ubangidansa ya tsinci kansa kwanaki biyar kafin rasuwarsa.
Olu Ogogo ya ce rashin lafiyar da marigayi Taiwo Hassan ke fama da ita ta kara tsananta fiye da kowane lokaci kwanaki biyar kafin ya rasu.

Source: Instagram
Olu ya bayyana hakan ne a wata hira da City People da aka wallafa a Instagram, inda ya yi bayani kan fama da rashin lafiyar da fitaccen jarumin ya yi da kuma abubuwan da suka faru kafin rasuwarsa.
Halin da jarumi Taiwo Hassan ya shiga
A cewarsa, da farko an samu sauƙi a yanayin lafiyar marigayin yayin da yake karɓar magani, inda ya samu damar cin ɗan ƙaramin abinci.
Sai dai kimanin kwanaki biyar kafin rasuwarsa, rashin lafiyarsa ta ƙara tsananta, lamarin da ya sa iyalansa suka riƙa kai shi asibitoci daban-daban domin ƙarin gwaje-gwaje da magani, yayin da likitoci ke ƙoƙarin gano abin da ke damunsa da rage masa radadi.
An gano cutar da ta kashe Taiwo Hassan
Olu ya ce a yayin jerin gwaje-gwajen lafiyar ne aka sanar da iyalan cewa Jarumi Taiwo Hassan na fama da cutar kansa.
Ya ce gano cutar ya girgiza mutanen da ke kusa da jarumin, saboda lafiyarsa ta tsananta cikin ɗan gajeren lokaci.

Kara karanta wannan
Hakar ma’adanai: Atiku ya tausaya wa yaro, ya dauki dawainiyar karatunsa a makaranta
Tun da farko, jarumin ya koka da ciwon ƙirji yayin wata tafiya zuwa Ilaro a Jihar Ogun, bayan haka aka kai shi asibiti kuma aka shawarce shi da ya huta.
Yadda jarumin Nollywood ya yi jinya
Olu ya ce daga baya Taiwo Hassan ya so zuwa Indiya domin ƙarin magani, amma samun bizar tafiyar ya jinkirta shirin.
A cewarsa, lokacin da aka samu bizar, jarumin fina-finan na Najeriya ya riga ya yi rauni sosai har ba zai iya yin tafiyar jirgin sama ba.

Source: Instagram
Olu ya bayyana cewa daga bisani aka kawo wani likita daga Indiya domin kula da jarumin. Daga baya likitan ya ba da shawarar a mayar da shi wani asibiti a Legas, inda kwararrun likitoci suka ci gaba da ba shi magani.
Jarumi Taiwo Hassan ya rasu a ranar 23 ga Agusta, 2026, yana da shekaru 66, bayan fama da cutar kansa ta mataki na huɗu, kamar yadda jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito.
Jarumin Nollywood, Olu Jacobs ya mutu
Kun ji cewa fitaccen jarumi fim a Najeriya kuma mai shirya fina-finai, Oludotun Baiyewu Jacobs, wanda aka fi sani da Olu Jacobs, ya rasu yana danshekaru 84.
Olu Jacobs na daga cikin fitattun tsofaffin jaruman Najeriya, inda ya shafe tsawon rayuwarsa yana taka rawa a wasan kwaikwayo, shirye- shiryen talabijin da fina-finai.
Asali: Legit.ng
