Mr Ibu: Iyalan Marigayi Jarumin Fim Sun Fada Mummunan Yanayi bayan Mutuwarsa

Mr Ibu: Iyalan Marigayi Jarumin Fim Sun Fada Mummunan Yanayi bayan Mutuwarsa

  • Iyalan marigayi fitaccen jarumin Nollywood, Mr Ibu, sun bayyana irin halin da suka shiga bayan mutuwar marigayin
  • Matarsa da 'ya'anta sun roki ‘yan Najeriya su taimaka musu saboda matsalar kudin makaranta, haya da sauran bukatun rayuwa
  • Matar marigayin ta bayyana cewa sun shafe kusan watanni biyu ba tare da wutar lantarki ba, yayin da suke amfani da ruwan rijiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lagos, Najeriya - ‘Ya’yan marigayi fitaccen jarumin Nollywood, John Okafor wanda aka fi sani da Mr Ibu, sun roki al'umma taimako.

Matarsa da 'ya'yansa uku sun roki ‘yan Najeriya su tallafa musu domin biyan kudin makaranta, haya da sauran muhimman bukatun rayuwa.

Iyalan Mr Ibu suna neman taimako bayan mutuwarsa
Marigayi John Okafor da aka fi sani da Mr Ibu da iyalansa lokacin yana raye. Hoto: ladyjasminec/stellaibu.
Source: Instagram

Iyalan sun yi wannan kira ne a wata hira ta bidiyo da da mai kirkirar abubuwan intanet, King Mitchy ta wallafa a TikTok.

Iyalan marigayi Mr Ibu sun nemi taimako

A cikin faifan bidiyon, sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta tun bayan rasuwar jarumin wanda ya yi suna a baya.

Da take magana kan halin da suke ciki, matar Mr Ibu ta ce sun shafe kusan watanni biyu ba tare da wutar lantarki ba bayan an katse masu layi saboda rashin biyan kudin wuta.

Ta kara da cewa yanzu suna diban ruwa daga rijiya saboda ba su da karfin biyan wasu hanyoyin samun ruwa.

“Mun dogara ne da ruwan rijiya. Ban biya kudin haya ba, sannan an yanke mana wuta tsawon watanni biyu. Kullum muna neman inda za mu yi cajin wayoyi."

- In ji matar Mr Ibu

Iyalan marigayi Mr Ibu na neman taimako
Marigayi John Okafor da aka fi sani da Mr Ibu lokacin da ya ke raye. | Hoto: @realmribu.
Source: Instagram

'Ya'yan marigayin sun yaba wa mahaifiyarsu

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin ta yaba da kokarin mahaifiyarta, tana mai cewa duk da matsin rayuwa tana bakin kokarinta wajen ciyar da su da biyan wasu bukatunsu.

Ta ce:

“Ina godiya ga mahaifiyata. Tana yin duk mai yiwuwa domin ciyar da mu, biyan kudin makaranta da kuma tabbatar da muna cikin farin ciki.”

Matar Mr Ibu ta kuma bayyana cewa matsalar kudi ta fara kawo cikas ga karatun ‘ya’yanta, tana mai cewa rashin biyan kudin makaranta na iya hana su ci gaba da zuwa makaranta.

Ta bayyana cewa yanzu haka makarantar da yaran ke ciki sun turo mata sakon basukan da ake bin su.

Ta ce:

“Yanzu ba za su iya komawa makaranta ba. Har ma zan iya nuna sakon da makarantar ta aiko min yau dangane da bashin kudin makaranta."

King Mitchy, wanda ya gudanar da hirar, ya ce ana neman tallafi ne domin taimaka wa iyalan wajen biyan bashin kudin makaranta, kudin haya da kuma dawo da wutar lantarki gidansu.

An nemi taimakon wajen birne Mr Ibu

A baya, an ji cewa marigayi John Okafor zai samu damar a birne shi bayan shafe watanni yana ajiye ba tare da an yi bikin bisonsa ba.

Ahali, dangi da abokansa na neman taimakon kudade domin tabbatar da an ti bikin binne jarumin wasan kwaikwayon.

Idan ba ku manta ba, John ya shafe tsawon lokaci yana jinya kafin daga bisani ya kwanta dama a asibiti a Lagos.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.