Ana cikin Wahala a Ƙasa, Atiku, Tinubu Sun Kwashi Miliyoyin Dala Sun Kashe a Amurka
- Bola Tinubu da Atiku Abubakar sun kashe miliyoyin dala wajen neman tasiri a Amurka, adadin da ya kai sama da N14bn a Najeriya
- N14bn din da aka kashe wajen lobbying na iya tallafa wa kananan ‘yan kasuwa 56,000 idan aka ware N250,000 ga kowannensu
- Masana sun ce ya kamata a tantance amfanin kudin bin kafa, musamman ganin yadda ‘yan Najeriya ke fama da rashin aikin yi da matsalolin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fiye da dala miliyan 10 ne tawagogin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar suka kashe a Amurka.
Majiyoyi sun an ware kuɗaɗen ne wajen bin kafa a Amurka, kamar yadda bincike ya gano.

Source: Twitter
Wannan lamari ya haifar da tambayoyi kan abin da kudaden siyasa da na gwamnati za su iya samarwa a Najeriya, musamman yayin da ake fama da matsin tattalin arziki, cewar Vanguard.
Kudin da aka ware a Amurka
Takardun da aka gabatar a karkashin dokar rajistar wakilan kasashen waje ta Amurka, FARA, sun nuna cewa yarjejeniyoyin biyu sun kai kusan dala miliyan 10.2.
Haka kuma, idan aka ware N250,000 ga kowace sana’a, adadin kudin zai iya samar da jari ko tallafin fara sana’a ga kananan ‘yan kasuwa kusan 56,000.
Sai dai wannan lissafi misali ne kawai, ba wai yana nufin za a samar da kamfanoni 56,000 masu dorewa kai tsaye ba.
Adadin zai dogara ne kan girman tallafin, bangarorin da aka zaba, kudin gudanar da shirin, yadda sana’o’in za su dore, da kuma ko tallafin zai kasance kyauta, rance ko hannun jari.
Duk da haka, kwatancen ya sake haifar da babbar tambaya kan tattalin arziki: a kasar da samun jari na daga cikin manyan matsalolin kananan ‘yan kasuwa, me N14 biliyan za su iya cimmawa idan aka kashe su a cikin gida?
Kudaden da aka kashe a Washington
Bincike ya nuna cewa alaka tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin DCI Group na Washington ta fara ne a watan Disambar 2025.
A karkashin yarjejeniyar, an dauki DCI Group domin taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen bayyana manufofinta ga masu tsara manufofi a Amurka, musamman kokarinta na kare al’ummomin Kirista da kuma ci gaba da samun goyon bayan Amurka ga yaki da ta’addanci a Najeriya.
Yarjejeniyar farko ta watanni shida ta kai dala miliyan 4.5, tare da damar sabunta ta kai tsawon da zai iya kai jimillar kudin zuwa dala miliyan tara.
Gwamnatin Najeriya ta biya dala miliyan 4.5 tun farko domin watanni shida, matakin gwamnatin ya zo ne yayin da ake kara duba halin tsaron Najeriya a Washington da kuma damuwa kan martabar kasar a duniya.

Source: Twitter
Kudin da Atiku ya kashe a Amurka
A nasa bangaren, Atiku ya dauki kamfanin Von Batten-Montague-York, L.C. na Washington aiki a farkon shekarar nan karkashin yarjejeniyar shekara guda mai darajar dala miliyan 1.2.
Takardun da aka gabatar ga Ma’aikatar Shari’ar Amurka sun nuna cewa manufar yarjejeniyar ta hada da karfafa matsayin Atiku a tsakanin masu tsara manufofi a Amurka da kuma kalubalantar labaran da ake dangantawa da gwamnatin Najeriya.
Takardar ta kuma ce kamfanin zai taimaka wajen samar da tuntuba tsakanin Atiku da ‘yan Majalisar Dokokin Amurka da jami’an bangaren zartarwa, tare da ba shi shawarwari kan yadda zai bayyana matsayinsa kan manufofi.
A watan Yuli, rahotanni sun ce kamfanin ya fara rarraba tsofaffin takardun Ma’aikatar Shari’ar Amurka da suka shafi wata shari’ar kwace kadarorin da aka alakanta da safarar miyagun kwayoyi a shekarar 1993 da Tinubu.
An fara sake bayanan Tinubu a Amurka
A baya, an ji cewa Atiku Abubakar ya dauki hayar kamfanin Von Batten a kan kudi $1.2m domin a fallasa masa Bola Tinubu a kasar Amurka.
Yanzu wannan kamfani ya gabatar da takardun da suka shafi shari'ar shugaban na Najeriya ga jami’an kasar wajen.
Von Batten ya mika sama da shafuka 60 na bayanan shari'ar Tinubu, yanzu labarin ya kai ga majalisa da jami'an gwamnati.
Asali: Legit.ng


