Dan Wasan Fim da Ya Yi Digirin PhD a Wasan Kwaikwayo Ya Mutu
- Masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood ta sake shiga jimami jim kaɗan bayan kammala taron addu’o’in girmamawa ga Alexx Ekubo
- Wani labari mai raɗaɗi game da fitaccen ɗan wasan kwaikwayon fina-finan Yarbawa, Kola Oyewo, ya bayyana a kafafen sada zumunta
- Rahoton ya girgiza mutane da dama, ciki har da mashahuran jarumai, inda suka fara rubuta saƙonnin ta’aziyya da yabon marigayin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legos - Masana’antar fina-finan Nollywood ta yi rashin fitaccen ɗan wasa, marubucin wasan kwaikwayo mai suna Kola Oyewo.
Legit Hausa ta gano cewa rahotannin mutuwar jarumin sun bayyana a kafafen sada zumunta a daren Juma’a, 12 ga Yuni, 2026.

Source: Instagram
Jarumin fim, Kola Oyewa ya rasu
An tabbatar da rasuwar Kola Oyewo ne a wani saƙo da wani abokin aikinsa, Olorunlaiye Yomi, ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan
'Tinubu ya dawo da zaman lafiya a wasu yankuna': Matawalle ya hango nasara a 2027
Yomi ya wallafa hoton marigayin tare da rubuta:
"Allah ya ji kan ka, Oyewo Labaluyege."
Shi ma jarumi Kunle Afod ya tabbatar da rasuwar marigayin a wani sako da ya wallafa a Instagram, inda ya rubuta:
"Yau da dare mun rasa wani babban gwarzo. Kola Oyewo ya yi ban kwana da duniya.
"Ba za a taba mantawa da rawar da ya taka da kuma gudunmawar da ya bayar ga harkar wasan kwaikwayo da fina-finai a Najeriya ba.
"Tarihinsa zai ci gaba da zaburar da al’ummomi masu zuwa. Ka huta lafiya, ranka ya daɗe. Ayyukanka za su ci gaba da wanzuwa. Komai ya yi farko zai yi karshe."
Jarumin ya yi rashin lafiya
Kafin rasuwarsa, Oyewo ya bayyana matsalolin lafiyarsa a wani bidiyo da ya yi tare da jarumi Kunle Afod a shekarar 2024.
Fitaccen jarumin, wanda ya rasa matarsa a shekarar 2020, ya bayyana yadda likitoci suka sanar da shi cewa yana fama da kumburin mafitsara mai tsanani wanda ke hana shi yin fitsari yadda ya kamata.
Ya kuma ba da labarin irin wahalhalun da ya sha, ciki har da tiyata da dama, gwaje-gwaje da binciken lafiya kafin ya samu sauƙi.

Source: Instagram
Kola Oyewo ya yi karatu a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), inda ya samu takardar shaidar karatu a fannin wasan kwaikwayo da kuma adabin baka na Yarbanci, kafin daga bisani ya samu digirin farko daga jami’ar a shekarar 1995.
Daga nan ya wuce Jami’ar Ibadan, inda ya samu digirin na biyu da kuma digirin Ph.D. a fannin wasan kwaikwayo.
Legit ta gano cewa Kola Oyewo ya shahara a fina-finai da wasanni irin su:
- Sango
- Saworoide
- Oleku
Jarumi Alex Ekubo ya rasu
A wani labarin, mun kawo muku cewa masana'antar fim ta Nollywood ta yi rashin babban jarumi Alex Ekubo yana da sheka 40 a duniya.
Jarumai a ciki da wajen masana'antar sun yi jimami rasuwar shi, inda wasu suka bayar da labarin irin alakar da suka yi tare da shi.
Jaruma Rahama Sadau ta wallafa hoton ta tare da Ekubo, inda ta bayyana shi a matsayin abokin aiki na gari da suka fahimci juna sosai.
Asali: Legit.ng
