Sauki Ya Samu: Farashin Muhimman Kayan Abinci Ya Fadi Warwas a Najeriya
- Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya ce farashin wasu muhimman kayan abinci ya ragu da kashi 50 a faɗin Najeriya
- Kyari ya ce an samu raguwar farashin ne idan aka kwatanta da matakan farashin da aka samu kafin shekarar 2023
- Ya ce gwamnati ta ƙara samar da kayan noma tare da zuba jari a ababen more rayuwa na karkara da tallafa wa ƙananan manoma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa farashin wasu muhimman kayan abinci ya ragu da kusan kashi 50 cikin 100 a faɗin ƙasar idan aka kwatanta da matakan farashin shekarar 2023.
Kyari ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Maiduguri yayin gabatar da jawabin buɗe taron Community of Practice na kwamishinonin noma, lafiya, muhalli da raya karkara daga jihohin Najeriya.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya ce ta shirya babban taron tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Borno, da tallafin gwamnatin Jamus.
An gudanar da taron ne ƙarƙashin taken: “Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Don Samar da Wadatar Abinci a Najeriya.”
Da yake jawabi, Abubakar Kyari ya ce:
“Alhakinmu shi ne mu mayar da wannan manufa zuwa ƙarin samar da abinci, sauƙaƙa samun kayan abinci, ƙarfafa tattalin arzikin karkara da kuma samar da tsarin abinci mai ɗorewa,” in ji Kyari.
Farashin kayan abinci ya ragu
Kyari ya ce an samu raguwar farashin wasu muhimman kayan abinci da ya kai kashi 50 cikin 100, tare da ƙara samar da kayan noma, zuba jari a ababen more rayuwa na karkara da tallafa wa ƙananan manoma.
“Mun ga raguwar farashin da ya kai 50% na wasu muhimman kayan abinci, tare da faɗaɗa samar da kayan noma, zuba jari a ababen more rayuwa na karkara da tallafa wa ƙananan manoma,” in ji shi.
Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanya samar da wadataccen abinci a tsakiyar ajandar ƙasa, yana mai ƙalubalantar masu sukar gwamnati da su duba hujjojin zahiri maimakon mayar da tsadar rayuwa batun siyasa.
Ministan noma ya soki yan adawa
“Mu kasance masu gaskiya, nawa ne buhun shinkafa da masara a shekarar 2023, kuma nawa ne yanzu? Kashi nawa ne? Kada mu mayar da waɗannan abubuwa batun siyasa,” in ji shi.
Ministan ya bayyana cewa taron Maiduguri zai yi nazari mai zurfi kan shirin bunkasa noma na Afirka (CAADP) da kuma Dabarunsa da Tsarin Ayyuka na shekarar 2026 zuwa 2035.

Source: Getty Images
Gwamnatin Tinubu ta fara rabon taki
Kun ji cewa Hukumar Kula da Bunkasa Aikin Noma ta Kasa (NADF) ta fara rabon buhunan taki 100,800 ga kananan manoma 25,200 a jihohin Kaduna, Kano, Katsina , Kebbi da Jigawa.
Rabon takin na gudana ne karkashin shirin Renewed Hope - FISP wanda gwamnatin tarayya ta samar domin rage wahalhalun da manoma ke fuskanta.
Hukumar NADF ta ce za ta tura fiye da jami’an wayar da kai kan noma 1,800 domin taimaka wa manoma da dabarun noma na zamani.
Asali: Legit.ng

