Gwamnan da ke Bakar Adawa da Tinubu Ya Bada Mamaki da Aka Ji Yana Yabon Shi

Gwamnan da ke Bakar Adawa da Tinubu Ya Bada Mamaki da Aka Ji Yana Yabon Shi

  • Gwamnan jihar Bauchi ya karbi bakuncin Ministan tattalin arziki da kuma Ministan harkokin kiwon lafiya na kasa
  • Bala Abdulkadir Mohammed ya yabi Bola Ahmed Tinubu a gaban ministocin, ya ce ya yi masu aiki a Bauchi
  • Mai girma gwamnan ya ce Gwamnatin tarayya ta yi masu kokari ta fuskar tsaro ganin an fatattaki ‘yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi ya ce sauye-sauyen da Bola Tinubu ya kawo suna tasiri a fannonin tsaro da tattalin arziki.

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya yaba da manufofin Gwamnatin tarayya, ya ce suna aiki da Bauchi da sauran jihohi.

Bala Mohammed
Gwamna Bala Mohammed tare da Goodluck Jonathan a Bauchi Hoto: Governor Bala Abdulkadir Mohammed
Source: Facebook

Gwamna Bala Mohammed ya yabi aikin Bola Tinubu

A yammacin Litinin, 5 ga watan Oktoba 2026, The Cable ta rahoto gwamnan yana yaba wa kokarin gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

An ji labarin abin da shugaban gwamnonin APC ya fada wa Tinubu a haduwar farko

Ya yi wannan bayani ne lokacin da ya karbi bakuncin Ministan kudi da tattali, Taiwo Oyedele da kuma takwaransa, Ali M. Pate.

Bala Mohammed ya gode wa shugaban kasa saboda aikin da yake yi musamman ganin yadda yake yakar rashin tsaro a Bauchi.

Gwamnan ya ce mutanen Bauchi suna alfahari da Tinubu, ya ce kokarinsa ya sa miyagun ‘yan bindiga ba su hana mutane sakat ba.

“Ba za mu taba mantawa da wannan ba. Ku gaya masa cewa ba za mu taba mantawa da wannan kyakkyawar ni’ima da ya yi mana ba.”

- In ji gwamnan

Ya ce a sanadiyyar namijin kokarin da ya yi, mutane sun koma gonakinsu da daminar bana.

Abin da gwamnan ya fada game da Tinubu

An rahoto shii yana cewa:

“Ina son in jaddada godiyarmu ga Shugaba Tinubu, musamman kan batun tsaro. Kwanan nan ya kafa bataliyoyin sojoji guda biyu, daya a Alkaleri, dayan kuma a Tafawa Balewa,”

Kara karanta wannan

2027: Minista ya dage yana yi wa Tinubu aiki domin APC ta yi nasara a jihohi 5

“Mutanen Bauchi suna alfahari da shi sosai. A lokacin da ’yan bindiga suka kusa mamaye mu, babu wanda ya zo mana da daukin gaggawa. Na je wurinsa, kuma ya amsa kiranmu duk da cewa ina cikin jam’iyyar adawa.
“Ya turo da rundunar sojoji mai karfi karkashin jagorancin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, tare da rundunonin sojoji da sauran hukumomin tsaro.
“Sun yi nasarar korar sama da mutane 100,000 da ke kokarin lalata zaman lafiyarmu. A yau, duk wadanda aka tilasta musu barin gidajensu sun koma garuruwansu, kuma sun samu damar gudanar da noman bana.

- Bala Mohammed

Tashar TVC ta rahoto gwamna Bala yana fada wa ministocin cewa su sanar da Tinubu cewa ba za su manta da alherin nan ba.

Duk da jihar Bauchi tana adawa da gwamnatin Bola Tinubu, gwamnan ya ce shugaban kasar ya fadada shirin kiwon lafiya.

"Shekaru uku da suka wuce, an kaddamar da wannan aiki a Bauchi, kuma mu 'yan adawa ne.
Bayan Bauchi, sai jihar Oyo, ita ma jihar 'yan adawa ce. Wannan yana nuna irin mutum da kuma asalin Shugaba Tinubu,"

Kara karanta wannan

Amaechi ya zargi Shugaban kasa Tinubu da hannu a mutuwar mahafiyarsa

- in ji Bala Mohammed.

Gwamnan Bauchi bai son makauniyar adawa

A jawabinsa, ya ce ya kamata gwamnonin adawa su rika jinjina wa Gwamnatin tarayya maimakon a yi ta sukarta a makance.

Yake cewa ba sukar gwamnatin sama suke yi babu gaira babu dalili ba, a bangaren kiwon lafiya da tattalin arziki an yi kokari.

Ministocin na shugaba Tinubu sun kawo ziyarar zumunci ne yayin kaddamar da aiki a asibitin jami'a.

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Pate ya ce daga cikin ayyukan da za a kaddamar akwai cibiyar bincike a asibitin ATBU.

Gwamnan Bauchi
Gwamnan Bauchi da Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: Governor Bala Abdulkadir Mohammed/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnan Imo ya bi Tinubu Legas

Kmar yadda rahoto ya zo a baya, Gwamna Hope Uzodimma ya gana da Shugaban kasa Bola Tinubu a gidan sa a garin Legas ranar Lahadi.

Sanata Hope Uzodimma ya bayyana cewa ya yi wa shugaban kasa bayanin abubuwan da aka yi yana ketare da ya tafi hutun kimanin wata guda.

Gwamnan yana cikin wadanda ke kan gaba wajen yakar Nyesom Wike a jam’iyyar APC kuma shi da gwamnoni sun yi zama kan batun 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng