'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Cika Baki, Ya Ce Zai Samu Kuri'u kusan Miliyan 70 a Zaben 2027
- Dan takarar shugaban ƙasa na APM, Gwamna Seyi Makinde, ya ce jam’iyyarsa na shirin samun aƙalla kashi biyu bisa uku na ƙuri’un masu zaɓe miliyan 103
- Gwamna Makinde ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa a birnin tarayya Abuja
- Jam’iyyar APM mai alamar rogonta ce za ta gudanar da yaƙin neman zaɓen ne bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban ƙasa na APM, Gwamna Seyi Makinde, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na shirin lashe zaben 2027 da gagarumin rinjaye.
Makinde ya ce APM na da burin samun aƙalla kashi biyu bisa uku na ƙuri’un masu zaɓe miliyan 103 (kimamin kuri'u miliyan 68) da suka yi rajista domin zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu, 2027.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Uba Sani ta fadi abu 2 da suka fi rashin tsaro barazana ga zaman lafiya

Source: Facebook
Makinde ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja yayin ƙaddamar da kwamitin kula da yaƙin neman zaɓensa, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
APM na burin samun 2/3 na kuri'u
Gwamna na jihar Oyo a ce yaƙin neman zaɓen zai gudana ne bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026 domin samun nasara.
Mataimakinsa kuma tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Lawal Daura, ne ya wakilce shi a wajen taron tare da ƙaddamar da kwamitin a madadinsa.
Daura ya ce:
“Bisa bayanan INEC, mutane miliyan 103 ne suka yi rajista domin zaɓen. Muna da burin samun akalla kashi biyu bisa uku na ƙuri’un masu zaɓe miliyan 103 da suka yi rajista.
"A shirye muke mu tabbatar da cewa an gudanar da komai bisa Dokar Zaɓe. Waɗanda suke tunanin za su iya haddasa matsala, to za su sha mamaki.”
Yadda APM za ta tallata Makinde
Ya ce yaƙin neman zaɓen ya mayar da hankali ne kan “Sake Gina Najeriya”, yana mai bayyana hakan a matsayin mafita ɗaya tilo da za ta iya magance ƙalubalen ƙasar da gyara abubuwan da ba sa aiki yadda ya kamata.

Source: Facebook
Daura ya ƙara da cewa:
“Zan iya tabbatar muku cewa mune tawagar da za ta yi nasara. Muna da maza da mata masu mutunci waɗanda ba su san komai ba face nasara.
“Zaɓen mambobin wannan kwamiti alama ce ta muhimmancin da muka bai wa yaƙin neman zaɓenmu da ajandar sake gina ƙasar. Yaƙin neman zaɓenmu ba zai kasance da ƙarya, yaudara ko ha’inci ba. Muna son mu inganta Najeriya domin dukkan ’yan Najeriya.”
Gwamna Makinde ya yi alkawari
Kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya yi alkawarin sake fasalin Najeriya cikin shekaru hudu idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027.
Makinde ya ce ajandar sake fasalin Najeriya za ta shafi tsaro, ilimi, tattalin arziki da yanayin siyasa da zamantakewa, kuma za a iya kammala ta cikin wa’adi guda na shekaru hudu.
Asali: Legit.ng
