Tinubu Na Ta Samun Goyon Baya a Arewa, Manyan Malaman Jami'o'i 600 Sun Bayyana Matsayarsu
- Sama da manyan malamai 600 daga jami’o’in gwamnati a Arewacin Najeriya sun amince da sake zaɓar Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a 2027
- Malaman sun ce goyon bayansu ba sharadi ba ne, inda suka bukaci gwamnati ta magance tsadar abinci, sufuri, rashin aikin yi da matsalar tsaro
- Sun kuma yi kira da a ƙara zuba jari a fannin noma, ilimi, lafiya, hanyoyi, wutar lantarki a Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Sama da manyan malamai 600 daga jami’o’in gwamnati daban-daban na Arewacin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Goyon bayan na daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a wani taro da mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, ya shirya domin tattauna makomar siyasar Najeriya.

Source: Facebook
An gudanar da taron ne a asirce a Cibiyar Umaru Musa Yar’Adua da ke Kaduna, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.
Manyan shugabannin gwamnati sun halarci taron
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Ibrahim Masari, Gwamnan Kaduna, Uba Sani; Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal; Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; Gwamnan Borno, Babagana Zulum; da takwaransa na Gombe, Inuwa Yahaya.
Sauran mahalarta sun haɗa da Ministan Tsaro, Bello Matawalle; karamin Ministan Gidaje, Muttaqha Rabe Darma; da tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari.
Wata majiya mai tushe a wajen taron ta ce mafi yawan jami’o’in gwamnati da ke jihohin Arewa 19 sun samu wakilci.
An bai wa wakilai daga kowane yanki damar bayyana ra’ayinsu kan siyasar ƙasar da kuma aikin gwamnatin Tinubu.
Wakilan yankunan Arewa sun yi jawabi
Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya yi magana a madadin malamai daga yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Gwamnoni, Malamai da manyan Arewa sun yi taro, sun yiwa Tinubu mubaya'a
Babban mai kula da dakunan karatu a Jami’ar Tarayya da ke Lafia, Farfesa Abdulrazaq Baba Abdulrahman, ya wakilci Arewa ta Tsakiya, yayin da shugaban majalisar gudanarwar Federal College of Agriculture da ke Gwoza ya yi magana a madadin Arewa maso Gabas.
An kuma ce Farfesa Mohammed Umar Sanda na Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma na daga cikin mahalarta taron.
Sai dai Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi na Jami’ar Bayero da ke Kano, wanda wata majiya ta ce yana cikin wadanda suka halarci taron, ya musanta halartar taron. Ya ce ba ma ya san da wani taro makamancin haka ba.
Malaman sun yi nazari kan gwamnatin Tinubu
Farfesa Musa, wanda ya karanta sanarwar da aka fitar bayan taron, ya ce malaman sun yi cikakken nazari kan yadda gwamnatin Tinubu ta gudanar da mulki tun watan Mayun 2023.
Ya ce sun duba yanayin tattalin arziki, siyasa, tsaro da zamantakewar al’umma, musamman irin tasirin waɗannan abubuwa a Arewacin Najeriya.
A cewarsa, malaman sun amince cewa Tinubu ya karɓi tattalin arzikin ƙasar ne a lokacin da yake fuskantar matsalolin kasafin kuɗi, tsarin kuɗi da kuma matsalolin tsari.
Sun kuma ce shugaban ya gaji matsalar tsaro, ƙarancin ababen more rayuwa da gibin jarin ɗan Adam, yayin da wasu daga cikin sauye-sauyen gwamnatin suka ƙara wa ’yan Najeriya wahala.

Source: Twitter
Sun goyi bayan Tinubu
Bayan tattaunawar, malaman sun bayyana goyon bayansu ga sake zaɓar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
“Mun yanke shawarar bayyana goyon bayanmu ga sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.”
Sai dai sun jaddada cewa goyon bayan nasu ba shi da ma’anar bai wa gwamnati damar yin duk abin da ta ga dama ba tare da suka ba.
Sun bukaci gwamnati ta saurari koke-koken ’yan ƙasa, ta amsa suka mai ma’ana, tare da magance tsadar abinci da sufuri, rashin aikin yi da matsalar tsaro.
Omokri ya yi hasashen nasarar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Reno Omokri, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Reno Omokri wanda shi ne jakadan Najeriya da aka nada zuwa Mexixo ya yi hasashen cewa Tinubu zai lashe zaɓen da “gagarumin rinjaye”.
Asali: Legit.ng

