Akwai Matsala: Farashin Litar Fetur na Iya Haura N5,000 bayan Zaben 2027, An Gano Dalili
- Dan takarar shugaban ƙasa na SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi gargadin cewa litar fetur na iya kaiwa N5,000 idan Shugaba Bola Tinubu ya zarce
- Adebayo ya ce cire tallafin fetur da barin darajar Naira a hannun yan kasuwa na iya ƙara jefa tattalin arzikin Najeriya cikin hauhawar farashi
- Dan takarar ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta farfaɗo da matatun mai na cikin gida tare da samar da tallafin da aka tsara don kare ’yan ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi gargadin cewa farashin man fetur na iya tashi zuwa N5,000 kan kowace lita idan Shugaba Bola Tinubu ya samu wa’adi na biyu.
Adebayo ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Babban Mai Ba da Shawara kan Sadarwa na yaƙin neman zaɓensa, Comrade Mark Adebayo, ya fitar.

Source: Twitter
Ya ce manufofin tattalin arzikin gwamnatin yanzu, musamman cire tallafin man fetur da kuma tsarin sakarwa Naira mara, sun sanya tattalin arzikin Najeriya a wani hali, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Ya ce duba da sauya manufofin tattalin arziki gaba ɗaya ba, wa’adi na biyu ƙarƙashin irin wannan tsarin zai iya sa farashin fetur ya kai matakan da a baya ake ganin ba zai yiwu ba.
Adebayo ya fadi dalilan hasashensa
Adebayo ya danganta gargadin nasa da abin da ya kira karuwar faduwar darajar kuɗin Najeriya watau Naira.
Ya ce:
“Ana shigo da fetur Najeriya kuma ana sanya farashinsa ne da dalar Amurka. Matukar Babban Bankin Najeriya ya ci gaba da barin Naira a wannan tsari, darajar kuɗin za ta ci gaba da raguwa.
“Idan farashin canjin kuɗi ya kai N3,500 kan dala ɗaya a shekaru masu zuwa, kuɗin da za a kashe wajen shigo da fetur kaɗai zai haura N4,000."
Ya soki cire tallafin fetur
Da yake magana kan cire dukkan tallafin fetur, Adebayo ya ce hakan ya kawo karshen karfin gwamnati na rage wa ’yan ƙasa tasirin tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya.
“Idan farashin ɗanyen mai ya tashi saboda rikice-rikicen siyasa da tsaro a duniya, masu amfani da fetur a Najeriya za su ɗauki kashi 100 cikin 100 na nauyin hakan a gidajen mai, wanda kai tsaye zai haifar da hauhawar farashi mai ɗorewa.
“Tsadar fetur na ƙara hauhawar farashin sufuri. Hauhawar farashin sufuri kuma na ƙara farashin abinci. Wannan yana rage ƙarfin sayen Naira, lamarin da ke tilasta ’yan kasuwa ƙara farashi domin su iya biyan kuɗaɗen gudanar da ayyukansu," in ji shi.
Adebayo ya ce akwai mafita
Adebayo ya jaddada cewa matsin tattalin arzikin da ake ciki yanzu an dauko shi ne daga tsare-tsaren IMF na ƙasashen wajebmaimakon tsarin tattalin arziki da ya fi mayar da hankali kan ’yan ƙasa, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000

Source: Getty Images
Dan takarar na SDP ya ce idan aka zaɓe shi a shekara mai zuwa, gwamnatinsa za ta gaggauta farfaɗo da matatun mai na cikin gida ta hanyar tsarin haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Ya kuma ce gwamnatinsa za ta sake samar da tallafin da za a tsara musamman domin kare talakawa da sauran ’yan Najeriya daga durƙushewar tattalin arziki.
Atiku ya soki Tinubu kan tsadar fetur
Kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda farashin man fetur ya kai N1,470.
Atiku ya ce farashin danyen mai a yanzu ya kai $102.52 kan kowace ganga, amma 'yan Najeriya na biyan kudin mai fiye da lokacin da danyen mai ya kai $147 a 2008.
Asali: Legit.ng

