Masana'antar Fim Ta Yi Rashi, Fitaccen Jarumi a Najeriya Ya Bar Duniya
- Fitaccen jarumin Nollywood, Taiwo Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo, ya rasu, kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar
- ‘Ya’yan marigayin sun nemi taimakon likitoci kwanaki kadan kafin rasuwarsa, bayan da ya shafe lokaci yana fama da cutar kansa
- Abokan aikinsa sun bayyana alhininsu tare da yin addu’ar Allah Ya ji kansa, musamman duba da gudunmawar da ya bayar a bangaren fina-finan Yarbanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Najeriya, Taiwo Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo, ya rasu.
Majiyoyi da dama ne suka tabbatar da rasuwar jarumin, ciki har da Seun Oloketuyi, wanda ya kafa shafin Best of Nollywood.

Source: Instagram
An tabbatar da rasuwar Ogogo
Oloketuyi ya sanar da rasuwar jarumin a wani sako da ya wallafa a kafar sada zumunta ta Instagram a ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026.
Ya rubuta cewa Taiwo Hassan Ogogo ya rasu, yana mai cewa jarumin ya “rasa yakin fafutuka da rayuwa” a karshe.
‘Yar jarumin, Kaira Taiwo, ita ma an gan ta tana kuka yayin wani shirin kai tsaye da ta gudanar a Instagram ranar Lahadi, inda ta bayyana rashin yarda da rasuwar mahaifinta.
Saheed Balogun ya yi alhinin rasuwar
Shahararren jarumi kuma mai shirya fina-finai, Saheed Balogun, ya shiga cikin wadanda suka yi jimamin rasuwar Ogogo.
Balogun ya wallafa sakon ta’aziyya a Instagram, inda ya yi wa marigayin addu’ar samun rahamar Allah da shiga Aljanna.
Ya ce rasuwar ta kasance mai matukar radadi, tare da bayyana Ogogo a matsayin dan uwansa.
Ya yi fama da cutar kansa
Rasuwar Ogogo ta zo ne kwanaki kadan bayan da ‘ya’yansa mata, Kaira da Lima Taiwo, suka nemi taimakon likitoci da sauran al’umma domin neman hanyoyin taimakawa mahaifinsu.
Jaridar The Punch ta ce a ranar Litinin, 17 ga Agusta, 2026, ‘yan’uwan biyu sun yi amfani da kafafen sada zumunta wajen neman shawarwarin likitoci da taimako.
A cewar Kaira, likitocin da ke kula da mahaifinsu sun sanar da iyalin cewa ba za su iya ci gaba da yi masa maganin chemotherapy ba saboda halin da lafiyarsa ta kai.
Daga bisani iyalin suka fara neman wasu hanyoyin magani, ciki har da wasu hanyoyin kiwon lafiya na musamman da kuma magungunan gargajiya.

Source: Instagram
Ogogo ya yi fice a fina-finan Yarbanci
Taiwo Hassan ya kasance daya daga cikin fitattun jaruman masana’antar fina-finan Najeriya, musamman a bangaren fina-finan harshen Yarbanci.
Ya shafe shekaru yana taka muhimmiyar rawa a masana’antar, inda ya samu karbuwa daga masu kallon fina-finai a Najeriya da sauran kasashe. Rasuwarsa ta jefa ‘yan uwa, abokan aiki da masoya fina-finan Nollywood cikin alhini.
Dan majalisa ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Sakwa, Hon. Wanzam Mohammed Zaki, ya rasu a Bauchi bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Hon Wanzam Mohammed Zaki shi ne shugaban kwamitin majalisar kan kasafin kudi da samar da kudade har zuwa lokacin rasuwarsa.
Asali: Legit.ng

