Tirkashi: An Huro Wutar da Za Ta Iya Sanya INEC Hana Pantami da Wasu Yin Takara a 2027
- Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin zaɓe ya umarci INEC ta hana ’yan takarar da ba sa cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu tsayawa takara
- Kwamitin ya ce hukuncin Kotun Ƙoli ya kawar da rashin tabbas kan tanade-tanaden Sashe na 77 na Dokar Zaɓe ta 2026
- An bukaci INEC ta duba sunayen duk ’yan takarar 2027 tare da tabbatar da cewa suna cikin rajistar da jam’iyyunsu suka gabatar mata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin zaɓe ya mika bukatarsa ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Kwamitin ya bukaci hukumar INEC ta hana ’yan takarar da sunayensu ba sa cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu tsayawa takara.

Source: Facebook
Shugaban kwamitin, Bayo Balogun, ne ya bayyana hakan a wata wasiƙa da ya aikewa INEC, inda ya yi nuni da Sashe na 77 na Dokar Zaɓe ta 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Zance ya kare: INEC ta yi magana kan hukuncin kotu da zai iya shafar takarar su Pantami
Kwamitin ya nemi INEC ta aiwatar da Sashe na 77 Balogun ya bukaci hukumar ta tabbatar da aiwatar da wannan tanadi ga dukkan jam’iyyun siyasa masu rijista, bisa la’akari da wani hukunci da Kotun Ƙoli ta yanke kwanan nan.
A watan da ya gabata, Kotun Ƙoli ta maido da wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe da suka shafi rajistar mambobin jam’iyyun siyasa da kuma tantance ’yan takara.
Balogun ya kuma yi tsokaci kan matsayar da INEC ta bayyana a ranar 26 ga Yuli, 2026, inda hukumar ta nuna damuwa kan wasu hukunce-hukuncen kotuna da kuma kararrakin da ke gabanta game da yadda za a fassara da aiwatar da Sashe na 77.
Hukuncin Kotun Ƙoli ya kawar da rashin tabbas
Shugaban kwamitin ya ce matsayar INEC a wancan lokaci abin fahimta ce, saboda hukumar na son kauce wa ɗaukar matakan da ka iya sauyawa bayan an yanke hukunci na ƙarshe.
Sai dai Balogun ya ce yanayin shari’ar ya sauya bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, jaridar TheCable ta kawo rahoton.
A cewarsa, hukuncin ya kawar da rashin tabbas da ke tattare da tanadin, tare da samar da damar aiwatar da shi.
An nemi a binciki sunayen ’yan takarar 2027
Balogun ya bukaci INEC ta binciki ’yan takarar da dukkan jam’iyyun siyasa suka tsayar domin zaɓen 2027.
Ya ce hukumar ya kamata ta tabbatar da cewa sunayen ’yan takarar suna cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu da aka gabatar wa INEC tun farko, kamar yadda Sashe na 77(5) ya tanada.
A cewarsa, aiwatar da tanade-tanaden Dokar Zaɓe zai taimaka wajen rage yawan ƙararrakin da za su iya tasowa sakamakon rashin bin doka.
Abin da Kotun Ƙoli ta yanke
A watan Satumba, kwamitin alkalai bakwai na Kotun Ƙoli ya amince da ƙarar da INEC ta shigar, tare da maido da Sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2) na Dokar Zaɓe.
Kotun, a hukuncin da Alƙali Adamu Jauro ya jagoranta, ta ce tanade-tanaden da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke a watan Yuli ba sa karo da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
Kotun Ƙoli ta soke hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, tare da maido da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta yi watsi da ƙarar da Zenith Labour Party (ZLP) ta shigar kan waɗannan tanade-tanade.
Abin da Sashe na 77 ya tanada
Sashe na 77(5) ya tanadi cewa mambobin jam’iyya waɗanda sunayensu ke cikin rajistar mambobin jam’iyyar da aka gabatar wa INEC aƙalla kwanaki 21 kafin zaɓen fitar da gwani, babban taro ko taron jam’iyya ne kaɗai za su iya shiga irin wannan zaɓe ko taro.
A ƙarƙashin Sashe na 77(6), jam’iyya ba za ta iya amfani da wata rajistar mambobi daban da wadda ta gabatar wa INEC wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani, babban taro ko taron jam’iyya ba.
Sashe na 77(7) kuma ya tanadi cewa jam’iyyar da ta gaza gabatar da rajistar mambobinta cikin lokacin da doka ta tanada ba za ta iya tsayar da ɗan takara a zaɓe ba.
Tanadin zaɓen fitar da gwani
A gefe guda, Sashe na 84(2) ya tanadi cewa jam’iyyun siyasa za su tsayar da ’yan takararsu zuwa mukaman zaɓe ta hanyar zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato ko kuma ta hanyar cimma maslaha.

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya umarci cafke 'yan 'Tinubu Must Go a Borno'? An ji yadda zancen yake
Matakin kwamitin Majalisar Wakilai ya zo ne yayin da ake shirye-shiryen babban zaɓen 2027, inda ake sa ran INEC za ta duba bin waɗannan tanade-tanade na doka wajen tantance ’yan takara.

Source: Facebook
INEC ta gargadi 'yan siyasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe ta INEC ta gargadi ’yan siyasa cewa burin neman mulki bai kai darajar jinin ɗan Najeriya ba.
Hukumar ta kuma yi alƙawarin kama wa, hukunta wa da gurfanar da jam’iyyu, ’yan takara da wakilan jam’iyyu da suka koma amfani da tashin hankali, kalaman ƙiyayya ko sayen ƙuri’a a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

