‘Illar da Rikicin Zamfara Zai Yi ga Tinubu, Yari, Matawalle da Dauda Lawal’
- Wani masani ya gargadi cewa rikicin APC a Zamfara na iya raunana jam’iyyar gabanin zaben 2027
- Farfesa Abubakar Abdullahi ya ce rikicin na iya shafar Abdulaziz Yari, Bello Matawalle da Gwamna Dauda Lawal
- Ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya hada Yari, Matawalle da Dauda Lawal domin sasanta tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Ficewar ‘yan majalisar dokokin Zamfara takwas daga APC na iya yin mummunan tasiri ga jam’iyyar gabanin babban zaben 2027, inji wani masani.
‘Yan majalisar sun fice daga APC ranar 3 ga Oktoba, ta hanyar aika wasiku daban-daban ga shugabannin jam’iyyar na mazabunsu.

Source: Twitter
Farfesa Abubakar Abdullahi ya ce matakin ya kara bayyana rarrabuwar kawuna cikin APC a Zamfara, kuma hakan na iya raunana tsarin jam’iyyar na kasa, cewar The Nation.
Yan majalisa sun bar APC a Zamfara

Kara karanta wannan
Duk da matsalar da ake ciki da Wike, APC ta bayyana shirin da ta yi saboda Tinubu
Ya ce biyar daga cikin ‘yan majalisar takwas sun fito ne daga yankin sanatan Zamfara ta Yamma, wanda ya kira karfin siyasar tsohon gwamna Abdul’aziz Yari.
Daga cikinsu akwai Aliyu Ango Kagara mai wakiltar Talata Mafara ta Kudu, Ibrahim T. Tukur mai wakiltar Bakura da Faruk Musa Dosara mai wakiltar Maradun 1.
Ya kuma danganta lamarin da rikicin siyasa tsakanin manyan jiga-jigan Zamfara, musamman Yari, karamin ministan tsaro Bello Matawalle da Gwamna Dauda Lawal.
Abdullahi ya yi gargadin cewa rarrabuwar kawunan na iya rage karfin APC wajen tattara kuri’u da goyon bayan Tinubu a Zamfara a zaben 2027.
Ya ce idan ba a dauki mataki ba, yana ganin Tinubu zai iya shan babban kaye a Zamfara saboda wasu mutane sun kasa sauke nauyin da ke kansu.

Source: Facebook
Yadda rikicin zai shafi Gwamna Dauda Lawal
A cewarsa, lamarin na iya shafar damar wasu ‘yan takarar APC a 2027, ciki har da Yari, Sulaiman Abubakar Mahmud Gummi, Isah Mamman Anka, Abba Ahmad Sani da Gwamna Lawal.
Ya kuma ce wasu fitattun mutane sun yi kokarin sasanta ‘yan majalisar da Gwamna Lawal, amma kokarin bai haifar da sakamako ba, cewar Tribune.
Ya yi zargin cewa rikicin, tare da korafe-korafen wasu tsofaffin abokan siyasar gwamna, na iya shafar yadda APC za ta yi a zaben 2027.
Masanin ya kuma soki wasu manufofin gwamnatin Lawal, ciki har da karbar kudaden shiga, haraji iri-iri da dakatar da wasu nade-nade.
Abdullahi ya bukaci Shugaba Tinubu ya shiga tsakani kan rikicin APC na Zamfara, ta hanyar hada Sanata Abdulaziz Yari, Matawalle da Gwamna Lawal domin warware matsalolinsu.
Ya ce akwai bukatar Tinubu ya gayyaci jiga-jigan siyasar jihar ukun zuwa teburin sulhu domin sake tsara APC da samun nasara a zaben 2027.
Ya yi gargadin cewa rashin warware rikicin na iya shafar sakamakon APC da kuma yawan kuri’un da Tinubu zai samu a Zamfara a 2027.
Yari ya fadi alherin Tinubu a Arewa
Mun ba ku labarin cewa Abdulaziz Yari ya ce ya kamata ’yan Arewa su mara wa Tinubu baya a 2027 saboda yadda ya taimaka wajen ganin Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa.
Yari ya tuna cewa Tinubu ya ƙi tsayawa takara a 2019, yana mai cewa lokacin Arewa ne, sannan ya ci gaba da goyon bayan Buhari.
Daraktan yaƙin neman zaɓen na APC ya ce kwamitin ba ya neman Tinubu ya yi wa'adi biyu saboda tsarin karba-karba kawai, sai don ganin ya ci gaba da ayyukansa.
Asali: Legit.ng
