
Abun Bakin Ciki







Wata 'yar Najeriya, Funke Iyanda na fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 a Amurka kan zargin zamba da karɓar $40,980 daga tallafin rashin aikin yi ba bisa ka’ida ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah a Filato bayan buda baki. An taba kai masa hari sau uku kafin daga karshe a kashe shi.

Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya zargi tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun, da rusa masa aikin ginin sabon kamfanin da ya shirya ginawa a jihar.

Wata matashiya daga jihar Abeokuta, mai suna Temitope Adenike ta tuno yadda aka ci zarafinta, aka rika lalata da ita har ta samu ciki a hanyar Libiya.

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar mahaifiyar Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta wanda za a yi sallar jana'izarta a yau Asabar da rana.

Yan Najeriya da dama sun soki hukumar NYSC kan barazana ga matashiya yar bautar ƙasa a Legas da ta caccaki Gwamnatin Bola Tinubu a cikin wani bidiyo.

Hukumar kashe gobara ta Kano ta bayyana cewa ta ceci mutane 7, yayin da gobara ta kashe 7 tare da haddasa hasarar dukiyar Naira miliyan 50 a watan Fabrairu.

Taohon mamba a Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Hon. Kehinde Subair ya riga mu gidan gaskiya kwanaki ƙalilan gabanin bikin cikarsa shekaru 60 da haihuwa a duniya.

Rahotanni sun tabbatar cewa wata matar aure mai shekara 42 da ake Maman Zainab ta fadi ta rasu yayin tafsirin azumin Ramadan a masallaci a Abuja.
Abun Bakin Ciki
Samu kari