Siyasar 2027: Jihohi 10 da Suka Fi Yawan Masu Rijistar Zabe a Najeriya

Siyasar 2027: Jihohi 10 da Suka Fi Yawan Masu Rijistar Zabe a Najeriya

Hukumar INEC ta kasa ta fitar da jerin jihohin Najeriya da ke kan gaba da yawan masu rajistar zaɓe da gabanin babban zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana jihohin da suka fi yawan masu rajistar zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

INEC ta fitar da jihohin da suka fi yawan masu rijistar zabe
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan yayin taro a Abuja. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Facebook

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, cewar Punch.

Amupitan ya ce rajistar masu zaɓe ta ƙunshi sama da mutane miliyan 103, bayan kammala matakai uku na ci gaba da rajistar zaɓe da tantance bayanan na’ura.

Kara karanta wannan

An saki sunayen sojoji da mutum 25 da suka rasu a hadarin jirgin soji a Ondo

Jihohin da suka fi yawan masu kuri'a

Ya ce Lagos ce ke kan gaba da masu rajistar zaɓe, sai Kano da ke mataki na biyu, sannan Kaduna mai mutane a mataki na uku.

Kididdigar ta kuma bayyana cewa Katsina ce ta biyo baya da masu rajista yayin da Rivers ta kasance ta biyar da mutane 3,736,434 a rajistar.

Amupitan ya bayyana jerin jihohin kamar haka:

1. Lagos State — 7,488,633

2. Kano State — 6,570,276

3. Kaduna State — 4,662,640

4. Katsina State — 3,876,051

5. Rivers State — 3,736,434

6. Oyo State — 3,588,111

7. Delta State — 3,525,988

8. Benue State — 3,057,225

9. Ogun State — 3,037,981

10. Bauchi State — 3,012,547

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa NADECO ya riga mu gidan gaskiya

Kano ta zamo jiha na 2 da ta fi yawan masu rijistar zabe
Taswirar jihar Kano da ta fi yawan al'umma a Arewa. Hoto: Legit.
Source: Original

Sauran jihohi da ke da karancin masu rijista

Matakan uku na ci gaba da rajistar masu zaɓe sun samar da sababbin masu rajista 10,772,421 kafin kammala tantancewar bayanan na’ura da tsaftace rajistar.

INEC ta kuma tsara fara rabon sababbin katunan zaɓe na dindindin ga masu rajista a faɗin ƙasar daga ranar 9 ga Oktoba 2026.

A ƙarshen jerin akwai Ekiti da masu rajista 1,055,708, sai Bayelsa mai mutane 1,200,691 da suka yi rajistar zaɓe.

Babban Birnin Tarayya Abuja na matsayi na uku daga ƙasa da masu rajista 1,732,043, sai Ondo da 1,733,641 da Gombe mai 1,768,560.

Amupitan ya ce jimillar masu rajistar zaɓe a Najeriya ta kai 103,428,715, bayan kammala aikin sabunta da tsaftace bayanan masu zaɓe, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Umahi: Minista ya raba gardama, ya fadi abin da zai sa Tinubu ya zarce a 2027

INEC ta shirya raba sababbin katunan zabe
Shugaban hukumar zabe a Najeriya, INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Jinsi, shekaru da masu bukata ta musamman

A bangaren jinsi, ya ce maza sun kai 53,528,218, wato kashi 51.75 cikin ɗari, yayin da mata suka kai 49,900,497.

Ya bayyana cewa masu shekaru tsakanin 35 zuwa 49 ne suka fi yawa, inda suka kai 43,265,946, wato kashi 41.83 cikin ɗari na rajistar.

Masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 sun kai 29,777,576, wato kashi 28.79 cikin ɗari, yayin da masu shekaru 50 zuwa 69 suka kai 22,982,900.

Wannan rukunin masu shekaru 50 zuwa 69 ya wakilci kashi 22.22 cikin ɗari, yayin da masu shekaru 70 zuwa sama suka kasance mafi ƙanƙanta.

INEC ta ce masu shekaru 70 zuwa sama sun kai 7,402,291, wato kashi 7.16 cikin ɗari na jimillar masu rajistar zaɓe, kamar yadda Channels TV ta ce.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da 'yan ta'adda 96, sun ceto mutum 42

Hukumar ta kuma ce ta samu mutane 232,658 masu buƙatu na musamman a fannoni 10, waɗanda suka kai kusan kashi 0.23 cikin ɗari.

Mafi yawan masu buƙatu na musamman suna cikin rukunin “wasu”, inda suka kai 101,183, wato kashi 43.49 cikin ɗari na masu buƙatun.

Masu matsalar jiki sun wakilci kashi 11.67 cikin ɗari, yayin da masu matsalar gani suka kai 19,936, wato kashi 8.57 cikin ɗari.

Masu matsalar ji sun kai 14,326, wato kashi 6.16 cikin ɗari, yayin da mutane 8,832 suka yi rajista ƙarƙashin autism.

Kamfen 2027: INEC ta gargadi yan siyasa

Mun ba ku labarin cewa Hukumar Zabe ta INEC, ta gargadi ’yan siyasa cewa burinsu na neman mulki bai kai darajar jinin ko da mutum daya daga cikin ’yan Najeriya ba.

Hukumar ta yi alkawarin daukar matakin kamawa, hukunta da gurfanar da jam’iyyu, ’yan takara da wakilai da aka samu da hannu wajen tashin hankali ko kalaman kiyayya.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi wannan gargadin ne a wani taron horaswa na musamman ga editoci da Kungiyar Editocin Najeriya ta shirya tare da hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.