Kwana Ya Kare: Fitaccen Jarumin Fim da Ya Zauna a Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Fitaccen Jarumin Fim da Ya Zauna a Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Fitaccen jarumi fim a Najeriya kuma mai shirya fina-finai, Oludotun Baiyewu Jacobs, wanda aka fi sani da Olu Jacobs, ya rasu yana da shekaru 84
  • Ɗansa, Olusoji Jacobs, ne ya sanar da rasuwar mahaifinsa a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta ranar Laraba
  • Olu Jacobs ya shafe shekaru yana taka rawa a wasan kwaikwayo, talabijin da fina-finai, tare da samun lambobin yabo da dama a masana’antar fina-finai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun, Najeriya - Fitaccen jarumin masana'antar fim ta Nollywood da ke Kudancin Najeriya kuma mai shirya fina-finai, Oludotun Baiyewu Jacobs, wanda aka fi sani da Olu Jacobs, ya rasu.

Bayanai daga iyalansa sun nuna cewa Jrumi Olu Jacobs ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 84 da haihuwa a duniya.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa malaman jami’a 600 a Arewa suke goyon bayan tazarcen Tinubu

Olu Jacobs
Fitaccen jarumin fim a masana'sntar Nollywood ta Najeriya, Olu Jacobs Hoto: Olusoji Jacobs
Source: Instagram

Ɗansa, Olusoji Jacobs, ne ya sanar da rasuwar mahaifinsa a wani saƙo da ya wallafa a shafin Instagram ranar Laraba, 16 ga watan Satumba, 2026.

An sanar da rasuwar jarumin Nollywood

A madadin iyalansa, Olusoji ya ce:

“Cike da godiya ga Allah bisa rayuwar da ya yi mai ma’ana kuma ya yi gwagwarmaya a cikinta, muna sanar da rasuwar sbin kaunarnu, mahaifinmu, kakanmu da kawunmu. Zakin Lufodo."
“Muna kira ga dukkan masu rubutun ra’ayi a yanar gizo da masu tasiri a kafafen sada zumunta da su mutunta sirrin iyalanmu a wannan lokaci.”

Yadda Olu Jacobs ya yi fice

Iyayen da suka fito daga Egba Alake a Jihar Ogun, sun haife shi kuma rahotanni sun nuna cewa ya yi yarintarsa a jihar Kano.

Sha’awar yin wasan kwaikwayo ta ƙara ƙarfi a zuciyarsa bayan da ya halarci ɗaya daga cikin bukukuwan wasan kwaikwayo na shekara-shekara na Cif Hubert Ogunde a Colonial Hotel da ke Kano.

Kara karanta wannan

Murtala Asada ya caccaki gwamnatin Sokoto kan rufe masallacin Sheikh Lukuwa

Olu Jacobs na daga cikin fitattun tsofaffin jaruman Najeriya, inda ya shafe tsawon rayuwarsa yana taka rawa a wasan kwaikwayo, shirye-shiryen talabijin da fina-finai.

Ya yi karatu a Royal Academy of Dramatic Arts da ke Landan, inda ya fara sana’ar tasa a shirye-shiryen talabijin na Birtaniya.

Jarumim ya fito a fina-finai da dama

Daga bisani ya fito a shirye-shiryen ƙasa da ƙasa da dama kafin ya dawo Najeriya, inda ya zama ɗaya daga cikin manyan mutane a masana’antar fina-finai ta Nollywood.

Jacobs ya fito a fina-finan Najeriya da dama kuma ya shahara saboda ƙwarewarsa da yadda yake taka rawar da ke buƙatar nuna ƙarfi da kwarjini, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya samu lambobin yabo da dama a masana’antar, ciki har da Industry Merit Award a Africa Magic Viewers’ Choice Awards da Lifetime Achievement Award a Africa International Film Festival.

Jacobs.
Jarumin Nollywood, Oludotun Baiyewu Jacobs, wanda aka fi sani da Olu Jacobs Hoto: Olusoji Jacobs
Source: Instagram

Olu Jacobs ya kuma kasance mai gudanar da harkokin fina-finai, inda shi da matarsa, fitacciyar jaruma Joke Silva, suka taka rawa wajen gudanar da Lufodo Group da kuma bunƙasa harkar wasan kwaikwayo a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An shiga cikin gida an kashe babban malamin Najeriya a ƙasar waje

Jarumi Hassan Taiwo ya kwanta dama

Kun ji cewa fitaccen jarumin Nollywood, Taiwo Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo, ya rasu, kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar.

Rasuwar Ogogo ta zo ne kwanaki kadan bayan da ‘ya’yansa mata, KairaNda Lima Taiwo, suka nemi taimakon likitoci da sauran al’umma domin neman hanyoyin taimakawa mahaifinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262