Hadimin Dan Takaran Gwamnan Kano Ya Lissafo Abubuwa 3 da Za Su Kashe Abba a 2027
- Adnan Mukhtar Adam Tudun Wada ya yi wa jam’iyyar APC hasashen shan kashi a Kano a zaben shekarar 2027
- Ya ce Abba Kabir Yusuf zai fuskanci rashin nasara a kokarinsa na neman wa’adi na biyu saboda dalilai uku
- Malam Adnan ya ce dalilin farko shi ne mutane sun fusata da shi saboda ya raba gari da Rabiu Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Adnan Mukhtar Adam Tudun Wada matashin ‘dan siyasa ne kuma mai sharhi a kan harkokin yau da kullum a Najeriya.
Matashin ya yi hasashen cewa Abba Kabir Yusuf ba zai zarce a matsayin gwamnan jihar Kano ba, zai sha kashi a zaben 2027.

Source: Facebook
Adnan ya yi wa Abba bakin hasashe
A wani rubutu da ya yi a shafin Facebook, Adnan Mukhtar Adam Tudun Wada ya jero abubuwan da ya ce za su kada APC a Kano.
Kafin nan, sai da ya soki yadda Mai girma Abba Kabir Yusuf yake yawo da jar hula mai tambarin Bola Tinubu dare da rana.
Ya ce a duk gwamnonin Arewa, na Kano ne kadai yake sa wannan hula a koyaushe, alhali ko Sanwo Olu na Legas bai yin haka.
Malam Adnan Mukhtar Tudun Wada ya zargi Abba da yin hakan saboda shugaba Bola Tinubu ya taimaka masa ya lashe zabe.
Sai dai a cewarsa, bakin alkalami ya riga ya bushe game da tazarcensa a zaben shekarar 2027.
An soki yadda Abba yake yawo da hular Omologo
Adnan Mukhtar Tudun Wada ya rubuta:
“Daga cikin dukkan gwamnonin Arewa, gwamna na ne kadai yake yawan sanya wannan hular ta Omologo. Ko Sanwo-Olu, wanda ya fito daga Legas, ba ya yin haka.
Yusuf ya yi tunanin Omologo zai zo Kano ya tilasta a zabe shi. Bai san cewa lokaci ya riga ya kure ba.

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu
Adnan Tudun Wada wanda hadimi ne wajen ‘dan takaran gwamnan Kano a ADC ya ce abubuwa uku ne za su hana Abba zarcewa.
Matsololi 3 da ya ce Abba zai fuskanta a Kano
Kamar yadda ya fada, rabuwa da mai gidansa, Rabiu Kwankwaso da Abba Gida Gida ya yi zai sa mutane su ki zaben shi a jihar Kano.
Mai taimaka wa Ibrahim Amin Little din ya kuma kara da cewa mutane ba su kaunar jam’iyyar APC saboda bakar wahalar da aka sha.
"Abba zai rasa tazarce saboda dalilai uku. Na farko mutane ssun yi fushi da shi saboda raba jiha da Kwankwaso. Bisa al’ada, mutane ba su son cin amana.
"Na biyu, jam’iyyar da yake neman takara a karkashin tutarta. Mutane ba su son APC saboda irin wahalhalun da suka fuskanta a karkashin mulkin jam’iyyar."
- In ji shi
Bugu da kari, Adnan ya zargi gwamna Abba da rashin sanin kan mulki da iya jagorantar jama’a. Yake cewa:
"Dalili na uku shi ne rashin iya yanke matakin da ya dace, gazawar gudanar da mulki da ake gani, da sauran batutuwan da suka shafi yadda yake jagoranci.”
Gwamnan Bauchi ya jinjina wa Tinubu
Ana da rahoto cewa duk da ba su tare, Gwamnan jihar Bauchi ya yaba wa sauye-sauyen tattalin arzikin Bola Tinubu kwanan nan.
Mai girma Bala Mohammed ya gode wa shugaban kasa Tinubu saboda kafa sansanonin soja a Alkaleri da Tafawa Balewa da ya yi.
Gwamnan wanda 'dan jam'iyyar APM ne ya fadi haka ne da aka kaddamar da wata cibiyar bincike a Asibitin Koyarwa na jami’ar ATBU.
Asali: Legit.ng

