Yadda Kwankwaso Zai Ragargaji Atiku da Tinubu a Zaben 2027 a Kano
- Sanata Victor Umeh ya ce Rabi’u Kwankwaso ba zai shan kaye a Kano ba a zaben shugaban kasa na 2027
- Umeh ya ce farin jinin Kwankwaso a Kano zai bai wa NDC babbar dama, duk da adawar siyasa da ake yi masa
- Sanatan ya kuma yaba da tarbar Peter Obi a Fatakwal, yana cewa dimbin mutanen da suka fito na iya taka muhimmiyar rawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sanatan da ke wakiltar mazabar Anambra ta Tsakiya, Victor Umeh, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Rabi’u Kwankwaso ba zai sha kaye a Kano ba.
Umeh ya ce hakan zai faru ne idan aka gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci, yana mai magana kan shirin jam’iyyar NDC na tunkarar babban zaben 2027.

Source: Facebook
Sanatan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake tattaunawa a shirin Politics Today na Channels Television, inda ya yi bayani kan shirye-shiryen NDC.
'Kwankwaso zai yi nasara a Kano'
Ya ce farin jinin Rabiu Kwankwaso a Kano zai bai wa NDC babbar dama a jihar, ba tare da la’akari da irin adawar siyasar da ake yi masa ba.
Umeh ya kara da cewa yana aiki kafada da kafada da Kwankwaso da sauran shugabannin jam’iyyar, yana mai cewa NDC ta shirya sosai domin tunkarar zaben a matsayin babbar jam’iyyar adawa.
Umeh ya ce:
“Ko da wane irin hayaniya suka yi a Kano, babu wanda zai iya doke Kwankwaso a can idan zaben ya kasance sahihi, gaskiya, ’yanci da adalci. Zan iya yin fare a kan hakan.
“Ina aiki tare da shi da sauran shugabannin jam’iyyar sosai. Jam’iyyar ta shirya tsaf domin kasancewa jam’iyyar adawa da za ta fafata a wannan zabe da ’yan takara masu nagarta.”

Source: Twitter
Yadda NDC ke kara karbuwa a Najeriya
Ya kuma yi ishara da yadda dan takarar gwamnan jihar Rivers na NDC, Dumo Lulu-Briggs, ya samu gagarumar tarba a karon farko da ya shiga yakin neman zabe a Fatakwal.
Umeh ya ce taron ya nuna irin karfin da jam’iyyar ke da shi, yana mai cewa dubban mutanen da suka bi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi, za su kasance masu kada kuri’a.
Ya ce:
“Ku duba abin da dan takararmu na gwamnan Rivers, Dumo Lulu-Briggs, ya yi a Fatakwal a karon farko. An rufe Fatakwal saboda taron.
“Mutanen da suka bi su a Fatakwal a makon jiya ‘yan Najeriya ne da za su kada kuri’a. Me ya sa suke bin dan takararmu na shugaban kasa, Peter Obi, kamar Yesu yana ketarewa, mutane suna jerin gwano a bayansa? Dole ne akwai wani abu da ke motsa su kuma ke janyo hankalin masu kada kuri’a.”
Kwanwaso ya bukaci Atiku ya janye daga takara
Mun kawo muku rahoton cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya aika wa Atiku Abubakar saƙo yayin wata ganawa da mabiyansa daga jihar Adamawa.
Kwankwaso ya buƙaci a isar wa Atiku saƙonsa da harshen Fulatanci, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya fi fahimtar harshen.
Jagoran NNPP ya shawarci Atiku ya koma kula da sarautar Waziri Adamawa, yana mai cewa shekarunsa sun yi yawa don jagorantar Najeriya.
Asali: Legit.ng

