Sani Hamza
4964 articles published since 01 Nuw 2023
4964 articles published since 01 Nuw 2023
Dan majalisa, Raheem Ajuloopin ya gabatar da sabon kudiri na ƙirƙirar ƙarin kananan hukumomi a Kwara domin inganta mulki a matakin ƙasa, da ƙarfafa tsarin tsaro.
Tsohon ministan kwadago Joel Danlami Ikenya ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP, yana mai cewa matakin ya biyo bayan bukatar al’umma da makomar siyasar Taraba.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya bar PDP ya koma APC, inda ya shiga kara jerin gwamnonin da suka fice daga jam’iyyar tun bayan zaben 2023.
Gwamna Caleb Mutfwang na shirin barin PDP ya koma jam'iyyar APC kafin ƙarshen Janairu 2026, duk da adawa daga wasu manyan jiga-jigan APC a jihar Plateau.
Wata kotun jiha a Plateau ta yanke wa jami'in dan sanda, Ruya Auta hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an kama shi da laifin kashe ɗalibin UNIJOS, Rinji Bala.
Abubakar Malami ya kwana a ofishin EFCC bayan tsawon tambayoyi kan binciken asusun banki 46 da ake zargin yana da alaka da su da wasu badakaloli a lokacin Buhari.
Sarkin Daura zai yi wa Dauda Kahutu Rarara nadin sarautar Sarkin Wakar Kasar Hausa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin masoya Buhari da magoya bayan mawakin.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya tabbatar da komawarsa jam'iyyar Accord, inda zai nemi wa’adi na biyu a 2026 bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Sheikh Ahmad Gumi ya kare matsayinsa kan tattaunawa da ’yan bindiga, yana mai cewa babu wata dokar addini ko ka’ida ta duniya da ta haramta yin sulhu da miyagun.
Sani Hamza
Samu kari