Atiku Zai Shilla zuwa Amurka, Zai Yi Magana kan Matsalolin Najeriya

Atiku Zai Shilla zuwa Amurka, Zai Yi Magana kan Matsalolin Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai ziyarci kasar Amurka domin gabatar da jawabi kan halin da ake ciki a Najeriya
  • Atiku Abubakar zai yi magana kan matsalolin rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da su a kasar nan
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kare kansa kan wadanda suke sukar ziyarar da zai kai zuwa kasar Amurka

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja -Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya tabbatar da shirin sa na kai ziyara ƙasar Amurka.

Atiku zai kai ziyarar ne domin jawo hankalin duniya kan taɓarɓarewar tsaro, halin ƙuncin tattalin arziƙi, da kuma faduwar darajar shugabanci a Najeriya.

Atiku zai kai ziyara zuwa Amurka
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Paul Ibe, ya fitar a shafinsa na X, a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

2027: Rigima ta kunno kai a ADC kan 'tikitin' Kwankwaso/Obi da Atiku, Amaechi

Me Atiku zai yi a Amurka?

A yayin tattaunawar da za a yi, Atiku zai gana da masu ruwa da tsaki kan manufofi da hukumomi a Amurka.

Atiku ya ce ƙasar tana fuskantar “cikakken rikicin cikin gida” wanda ba za a iya ci gaba da raina shi ko mayar da shi batun siyasa ba.

Atiku ya koka kan rashin tsaro

“Tun daga tashe-tashen hankula a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, zuwa zubar da jini da ba ya ƙarewa a yankin Middle Belt, da kuma ƙaruwar yaɗuwar garkuwa da mutane da miyagun ayyuka a faɗin ƙasar nan."
"Atiku ya yi gargaɗin cewa lallai Najeriya tana ci gaba da rasa ikon gudanar da babban nauyin da ya rataya a wuyanta: wato kare rayuka da dukiyoyi."
“A cewarsa, lamarin ya wuce batun abubuwan da ke faruwa lokaci-lokaci, ya koma wani tsari na gazawar shugabanci gaba ɗaya. Ana mamaye al’ummomi, ana lalata hanyoyin samar da abinci, kuma an bar ’yan ƙasa cikin halin ko oho."

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Amurka za ta dauki mummunan mataki kan kasar Najeriya

“Ya kafa hujjar cewa duk gwamnatin da ba za ta iya tabbatar da tsaro na yau da kullum ba, to ta rasa hurumin ci gaba da rike amanar da aka ba ta."

- Paul Ibe

Game da tattalin arziƙi, Atiku ya bayyana abin da ya siffanta a matsayin ƙuncin rayuwa mai tsanani, inda ya buga misali da hauhawar farashin kayayyaki, raunana darajar kuɗi, da kuma raguwar ƙarfin sayayya na jama’a.

Atiku zai ziyarci Amurka
Atiku Abubakar da Gwamna Seyi Makinde a wajen taron 'yan adawa a Ibadan Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku ya yi martani kan masu sukarsa

Yayin da yake mayar da martani kan sukar da ake yi wa wannan ziyara tasa ta Amurka, Atiku ya yi watsi da iƙirarin cewa tuntuɓar ƙawayen ƙasa da ƙasa yana nufin gayyato tsoma baki daga waje ne.

“Atiku ba shi da wata tantama: faɗar gaskiya game da Najeriya ba rashin kishin ƙasa ba ne. Ya yi watsi da ra’ayin cewa tattaunawa da abokan haɗin gwiwa na duniya yana nufin neman tsoma bakin ƙasashen waje, inda ya jaddada cewa Najeriya ba ta rayuwa ita kaɗai, kuma ba za ta iya nuna kamar gazawarta na cikin gida ba shi da wani tasiri a waje ba."

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zubar da jinin 'yan Najeriya zai kawo karshen Tinubu a 2027

“Ya jaddada cewa duniya tuni tana ganin abin da yake faruwa; babban abin tambaya shi ne ko shugabannin Najeriya a shirye suke su fuskanci gaskiya."

- Paul Ibe

Atiku Abubakar ya yi gargadi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan shirin dakatar da yakin neman zabe.

Atiku Abubakar, ya yi gargadi kan yunkurin dakatar da yakin neman zabe a wasu sassan Arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa hakan na iya tauye hakkin kundin tsarin mulki da kuma kara fargabar hana jama’a damar kada kuri’a a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara tsananta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com