Pantami Ya Yi Martani da APC Ta Yi Amfani da Tsarin 'Sulhu' a Tsayar da Ɗan Takara

Pantami Ya Yi Martani da APC Ta Yi Amfani da Tsarin 'Sulhu' a Tsayar da Ɗan Takara

  • Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami, ya yi martani game da fitar da takara da aka yi a Gombe a yau Lahadi
  • Pantami ya ce doka ta tanadi cewa dole ne duk masu neman takara su amince kafin a yi sulhu, in ba haka ba a gudanar da zaɓen fitar da gwani
  • Kungiyar Pantamiyya ta bukaci magoya baya su kwantar da hankali tare da shirin zaɓen kai tsaye, yayin da lauyoyi ke duba matsalolin kundin jam’iyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital, Farfesa Isa Pantami, ya yi watsi da tsarin sulhun APC da aka sanar a Gombe kan mukaman zaɓe.

An gudanar da zaman sulhun ne a Gombe inda Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa an tsayar da Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna.

Kara karanta wannan

Matakin da Pantami ya dauka kan hadiminsa da ya kira ƴan adawa 'munafukai'

Pantami ya yi watsi da tsarin fitar da dan takara a Gombe
Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Pantami ya kalubalanci tsarin fitar da dan takara

Haka na cikin wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed ya fitar madadin magoya bayan Pantamiyya wanda Farfesa Pantami ya wallafa a Facebook.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa tsohon minista, Pantami yana Abuja lokacin da labarin sulhun ya bayyana.

Sanarwar ta bayyana tsarin a matsayin nadin sarauta kawai, tana cewa ba a bi ka’idojin doka da suka dace wajen cimma matsayar ba.

Mohammed ya ce babu wata sahihiyar matsayar sulhu da za a iya cimmawa ba tare da haɗa dukkan masu neman takara da suka karɓi fom ba.

Ya bayyana cewa dokar zaɓe ta 2022 ta fayyace hanyoyin tantance ‘yan takara, ciki har da sulhu ko kuma zaɓen fidda gwani kai tsaye.

A cewarsa, idan ɗan takara guda ya ƙi janyewa daga takara, wajibi ne jam’iyya ta koma tsarin zaɓen fidda gwani kai tsaye.

Pantami zai yi amfani da lauyoyi bayan rasa takara
Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Gombe: Shawarar da aka ba magoya bayan Pantami

Kara karanta wannan

Sanata ya yi wa gwamna kara, zai ajiye kujerarsa a majalisa domin ba shi wuri

Kungiyar Pantamiyya ta kuma buƙaci magoya baya su kasance masu bin doka duk da abin da ta kira rashin adalci da karya ƙa’idoji wanda ya sosa wa masoyan tsohon ministan rai.

Sanarwar ta ce tsarin sulhun da aka gabatar ya saɓa wa dokar ƙasa, umarnin shugabannin APC da kuma umarnin Shugaba Bola Tinubu.

Kungiyar ta ƙara da cewa lauyoyinta suna aiki kan matsalolin da suka shafi kundin rajistar mambobin jam’iyyar APC a Gombe a halin yanzu.

Daga ƙarshe, ta bukaci magoya bayan Pantami su shirya domin yiwuwar gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye a cikin jam’iyyar APC.

Pantami ya dakatar da haɗimimsa

An ji cewa tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙi na Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya dakatar da ɗaya daga cikin masu kula da shafukansa na sada zumunta.

Matakin ya biyo bayan wani saƙo da aka wallafa a shafinsa na Facebook wanda ya kira masu sukar Pantami ko malaman da ba sa goyon bayansa a matsayin "munafukai"

Pantami ya nisanta kansa da wannan bayani, inda ya bayyana cewa bai ba da izinin wallafa shi ba, kuma hakan ba ya wakiltar salon shugabancinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com