Abin da Matasa Suka Yi Wa Dauda Kahutu Rarara a Masallacin Abuja Ya Fusata Jigon APC

Abin da Matasa Suka Yi Wa Dauda Kahutu Rarara a Masallacin Abuja Ya Fusata Jigon APC

  • Tsohon mai neman takarar sanatan APC a Imo, Hon. Belusochukwu Enwere, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara
  • Ya yi gargaɗin cewa tsoratarwa da tashin hankalin siyasa na iya kawo cikas ga dimokuraɗiyya gabanin zaɓen 2027
  • Enwere ya buƙaci jami’an tsaro su binciki harin, gano waɗanda suka aikata shi tare da tabbatar da an hukunta su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Imo, Nigeria - Tsohon mai neman takarar sanatan jam’iyyar APC a Imo ta Gabas, Hon. Belusochukwu Enwere, ya yi Allah wadai da hari da aka kai wa fitaccen mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara, a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Enwere ya bayyana rahoton harin da kuma barazanar da ake yi wa magoya bayan Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki a matsayin abin damuwa.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai

Rarara.
Fitaccen mawakin APC mai mulki a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta rahoto cewa ya yi gargaɗin cewa tashin hankalin siyasa na iya kawo cikas ga shigar jama’a cikin harkokin dimokuraɗiyya da kuma amincewarsu da tsarin zaɓe.

Ya ce lamarin da ya shafi Rarara ranar Juma’a ya nuna yadda ƙiyayya ga mutanen da ake ganin suna goyon bayan jam’iyya mai mulki ke ƙaruwa.

A cewarsa, tsoratarwar siyasa na iya ƙara zafafa rikici, hana masu zaɓe fitowa kaɗa ƙuri’a da kuma sa jama’a ƙaurace wa zaɓe gabanin zaɓen 2027.

“Dole ne a dakatar da wannan hali saboda yana da mummunan sakamako ga dimokuraɗiyyarmu da tsarin gudanar da zaɓe. Waɗannan ayyukan ’yan daba na siyasa na iya jawo ƙaurace wa zaɓe gabanin babban zaɓen 2027,” in ji shi.

Tsohon mai neman takarar sanatan ya jaddada cewa kowane ɗan Najeriya yana da haƙƙin kundin tsarin mulki na goyon bayan duk jam’iyyar siyasa ko ɗan takarar da yake so ba tare da fargabar cin zarafi, barazana ko kai masa hari ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Enwere ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa kan irin goyon bayan siyasar da Tinubu ke samu, inda ya danganta hakan a wani ɓangare da sauye-sauyen tattalin arziki da shirye-shiryen tallafin al’umma na gwamnatinsa.

Sai dai ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan harin da aka ce an kai wa Rarara, su gano waɗanda ke da hannu a ciki tare da tabbatar da an hukunta su.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro su ƙarfafa matakan kare ’yan ƙasa da kuma hana tashin hankalin da ya shafi siyasa yayin da harkokin siyasa ke ƙara ƙamari gabanin babban zaɓe na gaba.

Matar Rarara ta wallafa bidiyo

Kun ji cewa Aisha Humaira, matar fitaccen mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ta fitar da wani bidiyo bayan abin da ya faru da mijinta a Abuja.

Mutane sun maida martani kan bidiyon, inda wasu ke ma Rarara da Aisha Humaira fatan alheri, wasu kuma na kara dawo da batun harin da aka kai masa a masallacin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262