'Kowa Ya Yi Ta Kansa,' Isra'ila Ta Saki Sunayen Garuruwa 11 da Za Ta Kai wa Hari
- Rundunar sojin Isra'ila ta gargaɗi mazauna garuruwa da ƙauyuka 11 a kudancin Labanon da su fice daga gidajensu cikin gaggawa
- Sojoji sun bukaci farar hula da su matsa akalla mita 1,000 nesa da garuruwansu domin kauce wa hare-haren da suke kai wa kan kungiyar Hezbollah
- Abin lura shi ne garuruwa uku daga ciki na karɓar wannan umarni ne a karon farko, yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kasa kare fararen hula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Lebanon – Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da sabon gargaɗi na kai hare-hare kan wasu yankunan kudancin Labanon.
Sojojin sun bukaci mazauna garuruwa 11 da su gaggauta kwashe ya-nasu-ya-nasu su bar gidajensu kafin su ji saukar ruwan makamai.

Source: Getty Images
Isra'ila za ta kai hari garuruwa 11
A wani labari da Aljazeera ta fitar, sojojin Isra'ila sun bukaci mazauna garuruwa 11 su fice daga gidajensu, da suka hada da:
- al-Duwayr
- Arab Salim
- al-Sharqiya (Nabatieh)
- Jibshit
- Braashit
- Sarafand
- Dounin
- Briqa
- Qaaqaiya al-Jisr
- al-Qasiba (Nabatieh)
- Kfar Sir
Wannan umarni na mutane su fice daga garuruwansu na sanya matsin lamba ga gwamnatin Labanon wadda ke fuskantar rauni, musamman ta fannin ayyukan jin ƙai da kiwon lafiya.
Masana na ganin cewa babu wani tabbaci da zai ba mutane kwarin gwiwar komawa gidajensu a halin yanzu, in ji rahoton The Independent.
Hare-hare a gundumar Tyre
Hukumar dillancin labarai ta ƙasar Labanon (NNA) ta ruwaito cewa sojin Israel sun yi luguden wuta a gundumar Tyre, wanda ya shafi yankunan Froun, Ghandouriyeh, al-Mansouri, Qlailah, da kuma tuddan Majdal Zoun.
Hare-haren sun tsananta ne a daren Asabar zuwa safiyar Lahadi, inda ake jin kararrakin fashe-fashe akai-akai, in ji rahoton First Post.
Akwai rahotannin "rushe-rushe da gangan" da sojojin Israel suka yi a garin Chihine, baya ga wani mummunan hari da aka kai a garin Ar-Rayhan da ke gundumar al-Tuffah.
Har yanzu ana jin karar fashe-fashe yayin da jirage marasa matuƙa ke shawagi a sararin samaniyar kudancin ƙasar.

Source: Getty Images
Fargabar sake tashin mutane daga garuruwansu
Al'ummar kudancin Labanon na cikin fargaba sakamakon tsananta waɗannan hare-hare a cikin sa'o'i 12 da suka gabata.
Wannan yanayi na barazanar haifar da wani sabon rukunin gudun hijira, domin mutane da dama sun fara tunanin sake barin yankin bayan sun koma gidajensu yayin yarjejeniyar tsagaita wuta.
Abin lura shi ne, yarjejeniyar tsagaita wutar ba ta yi wani tasiri mai girma ba wajen dakatar da hare-haren da ake kai wa gine-ginen farar hula da gidajen mutane.
Hezbollah ta samu nasara kan Isra'ila
A wani labari, mun ruwaito cewa, Hezbollah ta kai hare-hare ta hanyar amfani da jirage marasa matuka mau dauke bama-bamai kan sojojin Israila.
Mayakan na Hezbollah sun kashe sojan Isra’ila guda ɗaya, yayin da wani kuma ya ji rauni matsakaici a harin wanda aka kai a Kudancin Lebanon.
Wani jirgi mara matuki daban da ƙungiyar Hezbollah ta harba ya sauka a wani sansanin manyan bindigogi a kan iyaka, inda ya raunata wasu sojoji 12.
Asali: Legit.ng

