Matakin da Pantami Ya Dauka kan Hadiminsa da Ya Kira Ƴan Adawa 'Munafukai'
- Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙi na Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya dakatar da ɗaya daga cikin masu kula da shafukansa na sada zumunta
- Matakin ya biyo bayan wani saƙo da aka wallafa a shafinsa na Facebook wanda ya kira masu sukar Pantami ko malaman da ba sa goyon bayansa a matsayin "munafukai"
- Pantami ya nisanta kansa da wannan bayani, inda ya bayyana cewa bai ba da izinin wallafa shi ba, kuma hakan ba ya wakiltar salon shugabancinsa
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Gombe – Farfesa Isa Ali Pantami, wanda ke son tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe, ya ɗauki matakin gaggawa wajen hukunta ɗaya daga cikin ma'aikatansa bayan wallafa kalaman ɓatanci ga abokan hamayya.
Pantami ya bayyana cewa an wallafa saƙon ne ba tare da saninsa ba, inda aka siffanta duk wanda ba ya goyon bayansa, ciki har da malamai, a matsayin munafukai.

Source: Facebook
'Munafuki': Pantami ya dakatar da hadiminsa
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Pantami ya jaddada cewa a matsayinsa na tsohon minista, malamin addini, kuma masani, ya fahimci muhimmancin suka a matsayin sinadarin da ke gyara tafiyar gwamnati da samar da ci gaba.
Babban malamin addinin ya ce siyasa tana bukatar mutunta kowa ba tare da la'akari da bambancin addini ko ra'ayi ba.
"An jawo hankali na game da wani sako da daya daga cikin masu kula da wannan shafin ya wallafa, inda ya kira dukkan masu adawa da Farfesa Pantami a matsayin munafukai, kuma duk malamin da ba ya goyon bayan siyasar Pantami munafuki ne.
"Ina son sanar da al'umma cewa ba da yawu na aka fadi hakan ba, ba ni na bada umarnin yin wannan rubutu ba. Kuma, na riga na dakatar da wanda ya yi wannan wallafa."
- Farfesa Isa Ali Pantami.
Manufar siyasar Pantami a Gombe
Farfesa Pantami ya bayyana cewa burinsa na mulkin jihar Gombe ya ginu ne a kan samar da shugabanci na adalci ga kowa, duba da cewa jihar tana da kabilu da addinai daban-daban.
Ya ƙara da cewa, addinin Musulunci ya umurci shugaba ya yi adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci ba kuma tawagar yakin neman zabensa ta ƙunshi Musulmai da Kiristoci.

Source: Facebook
Burin maye gurbin Inuwa Yahaya
Wannan dambarwa tana zuwa ne a daidai lokacin da Pantami ke shirin takarar gwamnan jihar Gombe domin gaje Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ke kammala wa'adin mulkinsa na biyu da doka ta tanada.
Pantami ya nuna cewa zai gina gwamnati mai sauraron kowa maimakon nuna kyama ga masu adawa da shi. Tuni dai aka goge saƙon da ya haddasa takaddamar daga shafinsa na Facebook bayan da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Gwamna ya nemi Pantami ya hakura da takara?
Tun da fari, mun ruwaito cewa, an yada wasu rahotanni kan batun takarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a zaben gwamnan jihar Gombe na 2027.
Rahotannin sun nuna cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci Farfesa Pantami da ya hakura da yin takara.
Sai dai, Farfesa Pantami ya fito ya ƙaryata wannan labari gaba ɗaya, inda ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinsa. Read more:
Asali: Legit.ng


