Siyasar 2027: Manyan Kusoshi a APC, PRP da NNPP Sun Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar NDC

Siyasar 2027: Manyan Kusoshi a APC, PRP da NNPP Sun Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar NDC

  • Sabuwar jam'iyyar NDC mai adawa ta samu karuwa bayan da manyan 'yan siyasa suka sauya sheka zuwa cikinta
  • Manyan 'yan siyasa daga jam'iyyun APC, PRP da NNPP suka sanar da sauya shekarsu zuwa jam'iyyar NDC a hukumance
  • Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya yi masu maraba zuwa jam'iyyar bayan da suka raba gari da jam'iyyunsu

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Jam’iyyar NDC ta samu gagarumar karuwar mambobi bayan da fitattun ’yan siyasa suka shigo cikinta.

Fitattun 'yan siyasa daga jam’iyyun APC, PRP, da NNPP sun fice tare da shiga NDC a hukumance gabanin babban zaɓen 2027.

Jam'iyyar NDC ta samu karuwa
Sanata Seriake Dickson tare da masu sauya sheka zuwa NDC Hoto: @IamHSDickson
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar har da Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, tsohon ɗan majalisar wakilai kuma tsohon mamba a hukumar ɗa’ar ma’aikata (CCB), wanda ya yi murabus daga APC domin komawa NDC.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Kwankwaso da Peter Obi ke shirin barin ADC

NDC ta samu karuwa

Sauran waɗanda suka shiga jam’iyyar sun haɗa da Babatunde Alli, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PRP na kasa, da Mohammed Sani Yahaya, ɗan takarar gwamnan Taraba na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023.

Sun koma NDC ne tare da dubun-dubatar magoya bayansu da tsarin siyasarsu da suka riga suka gina.

Yayin da yake jawabi a wajen taron karɓar su a Abuja, Agbonayinma ya nuna damuwa kan halin da Najeriya ke ciki, inda ya siffanta NDC a matsayin sahihin dandamali na sabunta ƙasa.

“Najeriya na cikin mawuyacin hali kuma tana neman madogara. Abin da aka yi mana alkawari a matsayin ‘Renewed Hope', ga ’yan Najeriya da dama, ya koma sabon yanke ƙauna. Dole ne mu yaƙi cin hanci da rashawa tare da maido da amana a harkar shugabanci."

- Ehiozuwa Johnson Agbonayinma

Meyasa jiga-jigan APC, PRP, NNPP suka koma NDC

Babatunde Alli ya danganta ficewarsa daga PRP ga matsalolin cikin gida na jam’iyyar, inda ya jaddada buƙatar sanya kowa a cikin harkoki, samar da damar shiga matasa, da kuma adalci a tsarin siyasa.

Kara karanta wannan

"Umarnin jagora": Jigo a Kwankwasiyya ya fice daga jam'iyyar ADC a jihar Kano

“Bullowar NDC ta ba ni sabon fata cewa za a iya yin siyasa ta hanyar da ta dace."

- Babatunde Alli

Shi ma Mohammed Yahaya, a ɓangarensa, ya yi alƙawarin tattara magoya baya daga matakin gundumomi zuwa jam’iyyar, inda ya bayyana goyon bayansa ɗari bisa ɗari daga sansaninsa na siyasa da ke jihar Taraba.

“A dukkan matakai, muna shiga NDC gaba ɗayanmu. Mun riga mun gina tsari, kuma mun himmatu wajen ƙarfafa jam’iyyar gabanin 2027."

- Mohammed Yahaya

Jam'iyyar NDC ta samu karuwa
Jiga-jigan da suka sauya zuwa jam'iyyar NDC Hoto: @IamHSDickson
Source: Twitter

Sanata Dickson ya yi masu maraba

Yayin da yake maraba da waɗanda suka sauya sheƙar, jagoran NDC na kasa, Seriake Dickson, ya bayyana matakin nasu a matsayin alamar ƙaruwar kwarin gwiwa kan hangen nesa na jam’iyyar na shugabanci da ya haɗa da kowa da kuma sauya fasalin ƙasa.

Haka zalika, shugaban jam’iyyar na kasa, Moses Cleopas, ya buƙaci sabbin mambobin da su kasance masu jajircewa ga kyawawan manufofin jam’iyyar tare da bayar da gudunmawa wajen ƙarfafa tsarinta na cikin gida.

Kwankwaso ya gana da shugabannin NDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shuganannin ADC.

Kara karanta wannan

2027: Alamu sun nuna Kwankwaso da Obi za su fita daga jam'iyyar ADC

Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi bakuncin wasu manyan shugabannin jam’iyyar NDC a ranar Litinin 27 ga watan Afrilu, 2026 a Abuja.

Majiyoyi sun nuna cewa ganawar ta gudana ne a gidansa da ke babban birnin tarayya, inda aka tattauna batutuwan siyasa da suka shafi makomar zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com