‘Abin da ’Yan Arewa Suka Gujewa da Ya Hana Tinubu Faduwa a Zaben 2027'

‘Abin da ’Yan Arewa Suka Gujewa da Ya Hana Tinubu Faduwa a Zaben 2027'

  • Fitaccen ɗan jarida Simon Kolawole ya ce tasirin yan Arewa ne ya hana Shugaba Bola Tinubu shan kaye a zaɓen 2023
  • Kolawole ya bayyana cewa kashi 39 cikin 100 na ƙuri’un Arewa sun tafi ga Tinubu, yayin da Atiku Abubakar ya samu kashi 36
  • Ya ce alaƙar siyasar Tinubu a Arewa, biyayya ga jam’iyyu da rarrabuwar kawunan ’yan adawa sun taimaka wajen nasararsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Babban dan jarida, Simon Kolawole, ya yi magana kan alakar Shugaba Bola Tinubu da yankin Arewa.

Kolawole ya ce da Tinubu ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 cikin sauƙi, idan mafi yawan ’yan Arewa a yankuna uku na siyasa sun yi amfani da bambancin ƙabila da yanki wajen zaɓe.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai

Dalilin samun nasarar Tinubu a zaben 2023 bayan rawar Arewa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Ɗan jaridar kuma marubucin ya bayyana hakan ne a cikin littafinsa mai suna Winning Formula: The Inside Story of Nigeria’s 2023 Presidential Election, cewar Leadership.

Dabarun siyasa daga yankin Arewa

Kolawole ya ce Atiku Abubakar ya dogara ne da samun kusan dukkan goyon bayan Arewa, tare da wasu ƙuri’u daga Kudu, saboda ya yi hasashen cewa ’yan Kudu za su fi zaɓar Tinubu da Obi bisa ra’ayoyin da suka shafi sauya mulki tsakanin yankuna.

Dan jaridar ya yi bayani kan dabarun siyasa, fafatawar neman mulki, haɗin gwiwa da lissafin zaɓe da suka taka rawa a zaɓen 2023, cewar Punch.

Kolawole ya ce lissafin da Atiku ya yi na samun gagarumin goyon baya a Arewa bai tabbata ba, domin Tinubu ya samu kashi 39 cikin 100 na ƙuri’un yankin, yayin da ɗan takarar PDP ya samu kashi 36, Obi kuma ya samu kashi 13.

Marubucin ya ce:

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

“Yawan ƙuri’un da Tinubu ya samu a Arewa na daga cikin abubuwan da suka fi ba da mamaki a zaɓen. Tinubu ya lashe yankuna biyu cikin ukun Arewa, wato Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, yayin da Atiku ya lashe Arewa maso Gabas. A jihohi 10 na Arewa ta asali, Atiku ya samu ƙuri’u 3,492,881, Tinubu kuma ya samu 3,287,858, inda tazarar ta kasance ƙuri’u 205,023 kacal.”

Ya bayyana wasu dalilai da dabarun siyasa da suka taimaka wa Tinubu wajen samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, duk da ƙalubalen da ya fuskanta.

Tasirin Arewa a zaben 2023 da ya ba Tinubu nasara
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Twitter

Tsawon lokaci da Tinubu ke gina siyasa

Kolawole ya ce Tinubu ya daɗe yana gina alaƙar siyasa a sassan Najeriya tun lokacin da yake gwamnan jihar Legas tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, ko ma kafin wannan lokacin.

Ya ce:

“Ya kasance cikin shirin mika mulki da bai yi nasara ba a farkon shekarun 1990. Ya haɗa kai da ƙungiyar siyasa mai ƙarfi ta Manjo Janar Shehu Musa Yar’Adua, sannan aka zaɓe shi sanata a shekarar 1992.
“Wasu daga cikin waɗannan alaƙoƙin sun ci gaba da aiki lokacin da ya zama gwamna bayan shekaru bakwai."

Gwamnatin Tinubu za ta raba takin zamani

An ji cewa Gwamnatin Tarayya ta ce za ta saki buhunan takin zamani miliyan uku da hatsi da ta tanada domin rage farashin abinci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Jam'iyyar adawa ta yanke shawara, ta umarci mabiyanta su zaɓi Tinubu a 2027

Ministan noma, Abubakar Kyari, ya ce za a fitar da takin cikin wata guda, yayin da za a saki hatsin da aka ajiye nan ba da jimawa ba.

Gwamnati ta kuma ce za ta fara rabon taraktoci 2,000, yayin da ake sa ran amfanin gona 13 cikin 17 zai samu karuwar yawan amfanin gona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.