Zance Ya Kare: Peter Obi Ya Fice daga Jam'iyyar ADC, Ya Bayyana Dalili

Zance Ya Kare: Peter Obi Ya Fice daga Jam'iyyar ADC, Ya Bayyana Dalili

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya tabbatar da cewa ba zai iya ci gaba da zama a cikin jam’iyyar ADC ba
  • Peter Obi ya bayyana cewa yanayin siyasar Najeriya yanzu ya koma tamkar guba da ke barazana ga duk masu son yin shugabanci na gaskiya
  • Yayin da yake bayyana dalilin ficewarsa daga ADC, Peter Obi ya ce matakinsa ba shi da alaƙa da David Mark ko kuma Atiku Abubakar

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam'iyyar ADC.

Peter Obi ya bayyana cewa daukar wannan mataki ya zama dole duk da cikas da matsin lamba da yake fuskanta a halin yanzu.

Kara karanta wannan

An yi wa Nafiu Bala barazanar raba shi da rayuwarsa kan ADC? Gaskiya ta fito

Peter Obi ya fice daga jam'iyyar ADC
Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasa na LP da ya fice daga ADC. Hoto:@PeterObi
Source: Facebook

Dalilan Peter Obi na barin jam’iyyar ADC

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Peter Obi ya ce:

“Na tashi yau da sassafe bayan dawowa daga coci da zuciya mai cike da tunani… kuma na ga ya kamata in sanar da ku abubuwan da waɗannan tunane tunane suka kunsa.”

Peter Obi ya bayyana cewa ya fuskanci ƙalubale iri ɗaya da waɗanda suka addabe shi a lokacin da yake cikin jam'iyyar LP a baya.

Ya yi zargin cewa jami'an gwamnati sun jefa rarrabuwar kawuna, zargi, da kuma shari'o'in kotu marasa ƙarewa a cikin jam'iyyar ADC.

Hakan ya sa ya ga cewa ci gaba da zama a jam'iyyar zai zama ɓata lokaci ne kawai duba da yanayin da ake ciki.

Dangantaka da shugabannin jam'iyya da Atiku

Obi ya fayyace cewa ficewarsa ba ta da alaƙa da wani saɓani na kashin kai tsakaninsa da shugaban jam’iyyar ADC, David Mark.

Kara karanta wannan

Sharadin Trump ga Iran yayin da ya ke shirin afkawa kasar da yaki karo na 2

Haka kuma ya wanke tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da ya nuna masa rashin adalci.

Obi ya ce:

“Bari in bayyana sarai: shawarata ta barin ADC ba domin shugabanmu ya nuna min rashin kyautawa ba ne, ko don sabani da Atiku Abubakar.”

Ya ƙara da cewa dukkan waɗannan shugabanni abokan tafiyarsa ne waɗanda yake girmama wa, amma matsalolin tsarin jam'iyyar sun fi ƙarfin dangantakarsu.

Ana hasashen cewa Peter Obi tare da Kwankwaso ne za su fice daga ADC lokaci guda.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a wajen wani taro. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Burin Obi na ganin sabuwar Najeriya

Duk da fita daga ADC, Peter Obi ya tabbatar da cewa burinsa na ganin an samu sauyi a Najeriya bai canza ba ko kaɗan.

Ya jaddada cewa ba ya neman shugabancin ƙasa domin son zuciya, amma yana son ganin ƙasar da za ta kare kowa da adalci.

Obi ya ce:

“Ba na neman zama shugaban ƙasa ido rufe… ina marmarin ganin al’ummar da za ta iya tausaya wa mahaifiyar da aka sace mata ɗa.”

Daga ƙarshe, ya nuna yaƙinin cewa Najeriya za ta iya samun shugabanci nagari wanda ya ginu a kan tausayi da daidaito ga kowa.

Kara karanta wannan

"Umarnin jagora": Jigo a Kwankwasiyya ya fice daga jam'iyyar ADC a jihar Kano

Karanta sanarwar a nan kasa:

Kwankwaso zai fice daga ADC

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon 'dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi na shirin ficewa daga ADC zuwa jam’iyyar NDC.

Kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa Kwankwaso zai sanar da komawarsa sabuwar jam'iyya watau NDC a makon gobe.

Ana ganin dai rikicin da ke addabar jam'iyyar ADC shi ne babban dalilin da ya jawo Kwankwaso da Obi suka nemi mafita kafin lokaci ya kure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com