Matar Rarara Ta Fitar da Bidiyon Mijinta bayan Dukan da Aka Masa a Masallacin Abuja

Matar Rarara Ta Fitar da Bidiyon Mijinta bayan Dukan da Aka Masa a Masallacin Abuja

  • Aisha Humaira, matar fitaccen mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ta fitar da wani bidiyo bayan abin da ya faru da mijinta a Abuja
  • Rahotanni sun nuna cewa Rarara ya hadu da fushin matasa a babban masallacin kasa da ke Abuja ranar Juma'a da ta gabata
  • Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan bidiyon da Aisha ta wallafa da kuma abin da ya faru da Dauda Rarara a masallaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan abin da ya faru da fitaccen mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara a masallacin kasa da ke Abuja, matarsa ta fitar da wani bidiyo a shafinta.

Amaryar Dauda Rarara kuma tsohuwar fitacciyar jaruma a masana'antar Kannywood, Aisha Humaira ta wallafa bidiyon mijinta yana shiryawa kafin ya baro gida.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai

Rarara.
Fitaccen mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara da matarsa, Aisha Humaira Hoto: Aisha Humaira
Source: Facebook

Aisha Humaira ta wallafa bidiyon Rarara ne a shafinta na Facebook yau Asabar, 21 ga watan Nuwamba, 2026, sa'o'i 24 bayan an ruwaito cewa Rarara ya ci duka a masallacin kasa da ke Abuja.

Abin da ya faru da Dauda Rarara

Tun farko Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa yayin da mawakin ke fitowa daga masallacin, jami’an tsaro sanye da kayan farar hula da kuma waɗanda ke sanye da kayan aikinsu sun kewaye shi, sai wasu fusatattun mutane suka yi kansa.

Wani faifan bidiyon lamarin da jaridar Daily Trust ta gani ya nuna yadda dandazon mutanen ke dukan Rarara tare da kokarin yaga masa tufafi, kafin wasu masu ibada su shiga tsakani tare da fitar da shi daga wurin.

Yayin da ake ta surutu kan lamarin, wasu na ganin abin da aka yi wa fitaccen mawakin bai dace ba, wasu kuma musamman makusantansa sun musanta cewa an bugi Dauda Kahutu.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya fadi matakin da ya kamata El Rufa'i ya dauka kafin tsare shi

Aisha Humaira ta wallafa bidiyo

Sai dai da safiyar yau Asabar, Aisha Humaira ta wallafa bidiyon Dauda Kahutu Rarara yana shiryawa a gida, kafin ya fita.

A gajeren bidiyon wanda aka rubuta, "Ɗan mama mai gobarar toti," an ga Aisha na taimaka wa mijin nata wajen sanya maballin hannu a rigarsa, lamarin da kara jan hankalin mutane.

Mutane sun maida martani kan bidiyon, inda wasu ke ma Rarara da Aisha Humaira fatan alheri, wasu kuma na kara dawo da batun harin da aka kai masa a masallacin Abuja.

Abin da yan Najeriya ke cewa

Ibrahim Musa ya ce:

"Duka ya sha naga ga dukkan alama jikinsa ya yi laushi."

Babagana Musty ya ce:

"Masha Allah Hajiya Aisha a ci gaba da hakuri komai lokaci ne watarana sai labari."

Aminu Baba ya ce:

"Ubangiji Allah Ya kara kare rayuwarka da zuriyarka da arzikinka don Albarkar Annabi Muhammadu Rasulillah SAW. Amin."

Haruna Musa ya ce:

"Me yasa ba ya murmushi ne tun da na ga ana soyewa, ko dai jikin ya yi la'asar ne a kan dukan masallacin Juma'a jiya?"

Kara karanta wannan

Matasa sun far wa wawakin siyasa, Dauda Rarara da duka a masallacin Juma'a

An farmaki Rarara a Abuja

Kun ji cewa fusatattun matasa sun farmaki fitaccen mawakin siyasa na APC, Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

An ce mutane sun hau Rarara da duka lokacin da yake fitowa daga masallaci, kafin jami'an tsaro su shiga tsakani har su cece shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262