Dalilin Matsalar Atiku da Minista a 2023 da Ya Jawo Wike Ya Tarwatsa PDP

Dalilin Matsalar Atiku da Minista a 2023 da Ya Jawo Wike Ya Tarwatsa PDP

  • Wani rahoto ya bayyana yadda zaɓin Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin Atiku Abubakar ya haddasa rikici tsakaninsa da Nyesom Wike
  • Kwamitin mutum 17 na PDP ya zaɓi Wike a matsayin wanda ya fi cancanta, amma Atiku ya yi watsi da shawarar, inda ya zaɓi Okowa
  • Marubucin littafin ya ce Wike ya ji an wulaƙanta shi, daga bisani ya ƙaurace wa kamfen ɗin Atiku tare da yin aiki don ganin ya sha kaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Wani sabon littafi da Simon Kolawole, ya rubuta ya yi bayani kan yadda rikicin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya ɓarke gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Kolawole ya danganta ɓarkewar rikicin da matakin Atiku na zaɓar tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa, duk da rahotannin da suka nuna cewa an ba Wike tabbacin samun tikitin.

Kara karanta wannan

Abin da matasa suka yi wa Dauda Kahutu Rarara a masallacin Abuja ya fusata jigon APC

Dalilin matsalar Atiku da Wike kafin zaben 2023
Ministan Abuja, Nyesom Wike day Atiku Abubakar. Hoto: Lere Olayinka, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Dalilin rikicin Wike day Atiku

A cikin bayanan littafin da jaridar Punch ta samu, Kolawole ya ce kalaman da Atiku ya yi lokacin sanar da zaɓin Okowa a ranar 16 ga Yuni, 2022, sun ƙara dagula al'amura tare da sa Wike jin an wulaƙanta shi.

Marubucin ya bayyana cewa Atiku ya sanar da zaɓin Okowa ne bayan kammala zaɓen fitar da gwani na PDP, inda ya ce ya tattauna da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar kafin yanke shawarar wanda zai zama mataimakinsa.

Atiku ya bayyana cewa yana son abokin takararsa ya kasance mutumin da zai iya maye gurbinsa a kowane lokaci tare da samun cancantar zama shugaban ƙasa.

Sai dai Kolawole ya ce wannan bayani ya zama kamar cin fuska ga Wike, wanda shi ma yake neman tikitin mataimakin shugaban ƙasa.

Ya ce Wike ya shirya yaƙi har ƙarshe, Atiku kuma ya kasance a shirye ya tunkare shi, amma a ƙarshe dukansu sun yi asarar burinsu na siyasa.

Kara karanta wannan

Har yanzu Atiku na cikin jerin 'yan takarar shugaban ƙasa a shafin INEC? Bincike ya gano gaskiya

Yadda Atiku ya samu matsala da Wike
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Yadda rikicin ya fara tsakaninsu

Littafin ya kuma bayyana jerin tarurrukan da Atiku da Wike da yaransu suka gudanar bayan zaɓen fidda gwani na PDP a watan Mayun 2022.

Ɗaya daga cikin tarurrukan ya gudana ne a gidan Wike da ke Guzape, Abuja, ranar 30 ga Mayu, 2022, bayan Atiku da shugaban PDP na lokacin, Iyorchia Ayu, sun kai ziyara ga tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal.

A cewar Kolawole, Wike bai ji daɗin yadda Atiku ya fara ziyartar Tambuwal ba, wanda janyewarsa daga takarar shugaban ƙasa ya taimaka wajen samun nasarar Atiku.

Wike ya nuna damuwa kan yadda PDP ta zaɓi ɗan Arewa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, duk da fahimtar da gwamnonin Kudu suka cimma na cewa mulki ya kamata ya koma yankinsu.

Daga bisani, Atiku Abubakar da Wike sun tattauna su kaɗai a ɗakin karatun Wike, inda aka ce sun amince cewa za su ɓoye abin da suka tattauna.

Kara karanta wannan

An samu daidaito, gwamnatin Tinubu za ta suburbuɗo wa ma'aikata N70,000 duk wata

Kolawole ya ce a yayin tattaunawar, Atiku ya nuna sha'awarsa ta yin aiki da Wike a matsayin abokin takararsa.

Wike ya tambaye shi cikin mamaki cewa:

"A wane matsayi?"

Atiku ya amsa da cewa:

"A matsayin abokin takarata."

Sai dai Wike ya tunatar da shi cewa an riga an gaya masa cewa Okowa ne zaɓin da ake so.

Wike ya ce:

"Amma an gaya min cewa ka riga ka yi wa Okowa alƙawari."

Atiku kuma ya amsa da cewa:

"A'a, ban yi wa kowa alƙawari ba."

Marubucin ya ce wannan tattaunawa ta faranta ran Wike, har ya yi alƙawarin tallafa wa kamfen ɗin Atiku da kuɗi da kuma ƙarfafa masa goyon bayan jama'a a matakin ƙasa.

Kwamitin PDP ya zaɓi Wike amma Atiku ya ƙi

Kolawole ya bayyana cewa a ranar 8 ga Yuni, 2022, Atiku ya sake ganawa da Wike, inda ya sanar da shi cewa zai kafa kwamiti domin tantance mutanen da suka cancanci zama abokin takararsa.

Atiku ya ce zai ɗauki shawarar kwamitin a matsayin wadda za ta ɗaure masa hannu wajen zaɓen mataimakinsa.

Kara karanta wannan

'Zan ba kowace mazaba N40m': Ɗan takarar shugaban ƙasa ya ɗauki alƙawari

Abin da zai hana Atiku nasara a Arewa

An ji cewa Obafemi George ya ce sauya sheƙar Abba Atiku Abubakar zuwa APC da goyon bayan Tinubu na sake jefa shakku kan ikirarin Atiku na samun goyon bayan Arewa.

Jigon na APC ya tambayi yadda Atiku zai samu ƙuri’un masu zaɓe miliyan 25 a Arewa maso Yamma idan ya kasa shawo kan ɗansa.

George ya kuma yi zargin cewa ’yar shugaban ADC, David Mark, Odon Odon, na neman takarar majalisar wakilai ne a ƙarƙashin tutar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.