Tashin Hankali: An Nemi Wasu Sojojin Amurka an Rasa da Suka Je Kasar Morocco

Tashin Hankali: An Nemi Wasu Sojojin Amurka an Rasa da Suka Je Kasar Morocco

  • An nemi wasu sojojin Amurka sama ko kasa an rasa a kasar Moroco bayan da suka je wani aikin atisaye da ya hada jami'ai da dama
  • Mahukunta sun bayyana cewa tuni aka bazama neman sojojin domin gano inda suke bayan bacewarsu
  • Sojojin dai sun yi batan dabo ne biyo bayan wani atisayen soja na kasashe da dama da ake yi duk shekara a kasar wadda take a nahiyar Afirika

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kasar Morocco - Wasu sojojin Amurka guda biyu sun yi ɓatan dabo a yankin Kudu maso Yammacin kasar Morocco.

Sojojin sun bace ne biyo bayan wani atisayen soja na ƙasashe da dama da ake yi duk shekara, lamarin da ya sa dakarun Amurka da na ƙawayenta suka kaddamar da aikin neman su da ceton su.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ritsa 'yan ta'adda a Borno, an kashe tsageru

Wasu sojojin Amurka sun bace a Morocco
Sojojin Amurka a cikin jirgin ruwa Hoto: @uscentcom
Source: Twitter

Tashar Fox News ta kawo rahoton cewa jami'ai ne suka bayyana hakan a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2026.

Sojojin Amurka sun bace

Rundunar sojojin Amurka a Afirka (AFRICOM) ta ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a wurin atisaye na Cap Draa da ke kusa da Tan Tan, wani birni a Morocco mai tazarar kusan mil 15 daga Tekun Atalantika.

A cikin wata sanarwa a shafin X, rundunar ta ƙara da cewa aikin ceton ya haɗa da dakarun ƙasa, na sama, da na ruwa.

“Har yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma aikin neman su yana ci gaba." Inji sanarwar

Ba a bayyana fannin aikin soja ko rukunin da sojojin da suka ɓace suka fito ba.

An tuntuɓi AFRICOM don samun ƙarin bayani amma ba a samu amsa nan take ba.

Wane atisaye ake yi a Morocco

Atisayen yaƙin, wanda aka sani da African Lion, an fara shi ne a cikin watan Afrilu kuma ana gudanar da shi a ƙasashe hudu, waɗanda suka haɗa da Tunisia, Ghana, da Senegal. An tsara kammala shi a farkon watan Mayu.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun rikita Amurka da damfara, sun wawure miliyoyin daloli a jihohi 47

An fara atisayen ne a Tunisia tare da mambobi daga sassa daban-daban na rundunar sjoojin Amurka, ciki har da dakarun tsaron cikin gida, dakarun tarraya na Reserve, na sama, da na ruwa.

Sojojin Amurka sun yi batan dabo
Wasu dakarun sojojin Amurka a hamada Hoto: @SETAF_Africa
Source: Twitter

Sama da sojoji 7,000 ne daga ƙasashe sama da 30 ke halartar atisayen a fadin ƙasashe hudun da suka karɓi baƙuncinsa.

African Lion shi ne babban atisayen soja na Amurka mafi girma da ake yi duk shekara a Afirka, wanda ke tattara manyan kwamandoji daga Amurka da manyan ƙawayenta na yankin. An ƙaddamar da shi ne tun a shekarar 2004.

Jami’an Amurka sun ce atisayen na ƙasashe da dama an tsara shi ne don ƙarfafa alaƙar tsaro da kuma ƙara nuna karsashin sojoji don tunkarar yuwuwar rikice-rikice a duniya..

Amurka za ta iya sake kai hari a Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan yiwuwar sake kai hari a Iran.

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa na iya sake kai hare-haren sojoji kan kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Da aka tambaye shi abin da zai iya janyo sabon harin soja, shugaban ya ƙi bayyana dalla-dalla, yana mai cewa lokaci ne zai nuna abin da zai faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com