Kwankwaso Ya Je Maiduguri, Ya Fito da Abubuwa 3 da Za Su Sa Yan Arewa Su Nemi Canji a 2027
- Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Arewa maso Gabas na fuskantar kalubale daban-daban
- Ya bayyana haka ne a taron jama’a na jam’iyyar NDC da aka gudanar a Maiduguri, inda ya buƙaci ’yan Najeriya su nemi sauyin shugabanci
- Kwankwaso ya nemi mata su taka rawa wajen wayar da kan jama’a, tare da yin kira ga magoya bayan jam’iyyar su kare ƙuri’unsu a zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna damuwa kan ƙara tabarbarewar rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziki da mutanen Arewa maso Gabas ke fuskanta.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a taron jama’a na NDC da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Source: Facebook
A rahoton da Leadership ta kawo, jagoran Kwankwasiyya ya yi kira ga ’yan Najeriya, musamman mata, da su haɗa kai wajen neman sauyin siyasa gabanin zaɓe.
Kwankwaso ya fito da matsalolin Arewa
Ya koka da cewa rashin tsaro da ya daɗe yana faruwa ya lalata harkokin kasuwanci, ya kawo cikas ga zuba jari, tare da tilasta wa mazauna yankin da dama barin gidajensu zuwa sansanonin ’yan gudun hijira (IDP) da wasu garuruwa mafi tsaro.
A cewarsa, halin da ake ciki ya sa ’yan Najeriya da dama ke rayuwa cikin tsoro da rashin tabbas, yayin da suke fama da wahalar biyan buƙatun yau da kullum.
“Ba za mu ci gaba da nuna kamar komai yana tafiya daidai ba alhali al’ummarmu na shan wahala,” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma nuna damuwa kan yadda kuɗin kula da lafiya ke ƙara tsada, yana mai cewa ’yan Najeriya da dama ba sa iya biyan kuɗin jinya saboda tsadar rayuwa.
Abin da Najeriya ke bukata
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC ya kuma soki abin da ya kira tara dukiya da wasu jami’an gwamnati ke yi, yayin da talakawa ke ci gaba da fama da talauci.
Ya ce ƙasar na buƙatar shugabanni waɗanda suka fahimci halin da talakawa ke ciki, kuma suke da niyyar amfani da dukiyar gwamnati domin amfanin al’umma.
“Muna buƙatar shugaba da ya fahimci wahalhalun da talakawan Najeriya ke ciki, kuma yake shirye ya yi musu aiki,” in ji shi.
Kwankwaso ya buƙaci mata su taka rawa sosai wajen tattara goyon baya ga jam’iyyar NDC, inda ya ce su kai saƙon neman sauyin siyasa ga mazajensu, iyalansu, maƙwabtansu da sauran al’ummominsu.

Source: Facebook
Ya kuma nemi a mara wa ɗan takarar gwamnan jihar Borno na NDC, Rear Admiral Sunusi Kashim Ibrahim, baya, yana mai bayyana shi a matsayin fitaccen jami’in soja da ya yi wa Najeriya hidima na tsawon shekaru 35.

Kara karanta wannan
2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa
Ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar su guji ruɗani kan ainihin jam’iyyar da suke yi wa kamfe, tare da tabbatar da cewa masu zaɓe sun fahimci jam’iyyar, ɗan takararta da shirye-shiryenta.
Kwankwaso ya soki gwamnatin Gombe
Kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin jihar Gombe da kawo cikas ga shirinsa na gudanar da taron jam’iyyar NDC a jihar.
Kwankwaso ya ce an tilasta sauya wurin taron babu shiri bayan da ake zargin gwamnatin jihar ta matsa wa masu wurin taron lamba.
Asali: Legit.ng

