Gwamnatin Tinubu Za Ta Kashe Naira Tiriliyan 1.1 a Kaduna, Uba Sani Ya Yi Bayani
- Gwamnatin Tarayya ta amince da manyan kwangiloli guda biyu na ayyukan more rayuwa a jihar Kaduna waɗanda darajarsu ta haura Naira triliyan ɗaya
- Ayyukan sun haɗa da ginin layin dogo na zamani da kuma gyaran babbar hanyar Mando zuwa Birnin Gwari
- Gwamna Uba Sani ya jinjina wa Shugaba Bola Tinubu, inda ya bayyana tasirin wadannan ayyukan ga sauya fasalin tattalin arziki da sufuri a Kaduna
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna – Gwamnatin Tarayya ta amince da ware maƙudan kuɗaɗe domin aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa a jihar Kaduna, matakin da ake kallo a matsayin gagarumin ci gaba ga yankin Arewa maso Yamma.
Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ce ta amince da waɗannan ayyuka waɗanda suka haɗa da gina layin dogo na cikin birni da kuma gyaran babbar hanyar da ta daɗe tana ci wa jama'a tuwo a ƙwarya.

Source: Twitter
Aikin layin dogo na cikin Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ne ya bayyana hakan a cikin wani sakon godiya da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya yi bayani dalla dalla game da ayyukan da za a yi.
Da farko, Uba Sani ya tabo batun aikin layin dogo, wanda darajarsa ta kai kusan Naira triliyan ɗaya, zai mamaye tsawon kilomita 50 a cikin birnin Kaduna.
Layin dogon zai haɗa muhimman sassa na birnin kamar haka:
- Kilomita 30: Daga Rigachikun zuwa Sabon Tasha.
- Kilomita 20: Daga Millennium City zuwa Rigasa.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa wannan aiki zai sa Kaduna ta zama jiha ta biyu kacal a Najeriya da ke da irin wannan tsarin sufuri na zamani.
Aikin ya yi daidai da tsarin gyaran sufuri na jihar, wanda ya riga ya haɗa da ginin hanyar motocin safa na BRT mai tsawon kilomita 24.
Gyaran hanyar mando zuwa Birnin Gwari
Aiki na biyu shi ne sake gina babbar hanyar Mando zuwa Birnin Gwari mai tsawon kilomita 122, akan kuɗi Naira biliyan 178.
Wannan hanya tana da matuƙar muhimmanci, inda za ta ta taimaka wa jami'an tsaro wajen gudanar da ayyukansu cikin sauri.
Hanyar za ta kuma sauƙaƙa jigilar kayan gona daga yankunan karkara yayin da za ta sake buɗe yankunan da suka daɗe a killace saboda rashin hanya.
Gwamna Sani ya tuna yadda Shugaba Tinubu ya ziyarci Birnin Gwari lokacin yaƙin neman zaɓe kuma ya yi alƙawarin gyara hanyar.

Source: Facebook
Tasirin ayyukan ga tattalin arziki
Gwamnan ya tabbatar wa jama'ar jihar cewa gwamnatinsa za ta sanya ido sosai domin ganin an kammala waɗannan ayyuka cikin inganci.
A cewarsa, waɗannan ba ayyuka ba ne kawai na lokaci guda, a'a, jari ne na dogon lokaci da zai haɓaka tattalin arziƙin jihar da kuma sauƙaƙa rayuwar mazauna Kaduna.
Wannan mataki ya nuna kwarin gwiwar da Gwamnatin Tarayya ke da shi akan tsarin ci gaban jihar Kaduna da kuma iyawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da manyan ayyuka.
Karanta sakon Uba Sani a nan kasa:
Kuri'un da Tinubu zai samu a Kaduna
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya yi magana game da kuri'un da Shugaba Bola Tinubu, zai samu a jihar a zaben 2027 da ake tunkara.
Gwamna Uba Sani ya nuna kwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai samu akalla kashi 70 cikin 100 na ƙuri’un jihar a lokacin babban zaɓen shekarar 2027.
Gwamna Uba Sani ya danganta hasashen nasa ga abin da ya bayyana a matsayin rawar gani da shugaban kasar yake takawa a kan mulki, wanda ya ce hakan ya gamsar da mutanen jihar.
Asali: Legit.ng


