Mutane Suna Shan Wahala a Kasa, Tinubu Ya Shirya Kawo Sauki Ta Hanyar Sufuri

Mutane Suna Shan Wahala a Kasa, Tinubu Ya Shirya Kawo Sauki Ta Hanyar Sufuri

  • Gwamnatin Tinubu na shirin sauƙaƙa zirga-zirgar ’yan Najeriya ta hanyar rage kuɗin mota da kusan kashi 40 cikin 100
  • An cimma yarjejeniya da kamfanin Yutong domin samar da motocin bas 300 da za su yi aiki da iskar gas ta CNG
  • Ana sa ran motocin farko guda 100 za su iso a watan Disamba, yayin da za a haɗa sauran a masana’antar da za a kafa a Ibadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya bayyana shirin rage kuɗin sufuri da kusan kashi 40 cikin 100.

Shugaban zai yi haka ne a wasu hanyoyin sufuri da ke cikin shirin gwamnati tsakanin shekarar 2027 zuwa 2031.

Tinubu ya shirya ragewa yan Najeriya wahala
Shugaba Bola Tinubu yayin tunawa da mazan jiya a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba wanda fadar shugaban ta wallafa a shafinta.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a jihar Kano ya yi ƙamari, an aika saƙon gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari

Matakan da Tinubu ke dauka

Tinubu ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin samar da sauƙi ga ’yan Najeriya ta hanyar rage kuɗin da suke kashewa wajen zirga-zirga.

Ya bayyana cewa tsadar sufuri na ƙara wa iyalai matsin tattalin arziki, domin tana rage kuɗin da mutane ke iya adanawa ko amfani da shi wajen biyan buƙatun gida.

Shugaban ƙasar ya jaddada cewa rage wannan nauyi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.

Jihohi 10 sun fara amfana da shirin CNG

Tinubu ya bayyana cewa shirin na fara haifar da sakamako a aƙalla jihohi 10 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ya ce an samu raguwar kuɗin sufuri a wasu hanyoyi, yayin da wasu jihohi suka fara bayar da zirga-zirga kyauta ga jama'a.

Shugaban ƙasar ya kawo misalin tafiyar Enugu zuwa Nsukka, inda ya ce kuɗin mota da a baya ya kai Naira 4,000 ya ragu zuwa Naira 1,600 a motocin bas ɗin CNG da ke cikin shirin.

Kara karanta wannan

An ba 'yar Amurka Dala miliyan 4.5 bayan ta yi hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya ta bayyana

Haka kuma, ya ce akwai motocin bas da ke karɓar Naira 50 a Borno, yayin da ake gudanar da zirga-zirgar motocin CNG kyauta a Kaduna.

Tinubu zai kawo sauki a sufuri
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: AFP

Yadda motocin CNG suka rage kuɗin sufuri

Shirin motocin bas masu amfani da CNG ya fara samun karɓuwa a wasu jihohi, inda aka samu raguwar kuɗin sufuri domin ragewa mutane radadi.

A watan Satumba, Tinubu ya ce motocin CNG da aka bai wa kamfanin Pacesetter Transport a Oyo sun rage kuɗin tafiyar Legas zuwa Ibadan daga kusan Naira 8,000 zuwa Naira 3,200.

Haka kuma, ya ce motocin bas 100 da aka girke a Enugu sun rage kuɗin tafiyar Enugu zuwa Nsukka daga Naira 2,500 zuwa Naira 1,500.

A Kaduna kuwa, ya ce motocin bas 100 sun yi jigilar fasinjoji kusan miliyan 3.2 kyauta a shekararsu ta farko.

Tinubu ya ba jami'o'i kyautar motocin CNG

A baya, an ji cewa Daliban jami’o’i uku da ke Kano sun karɓi motocin bas masu amfani da CNG daga Gwamnatin Tarayya a bikin Ranar Dimokuraɗiyya.

Gwamnatin Bola Tinubu ta ce shirin zai rage wa ɗalibai wahalar sufuri tare da ƙarfafa amfani da makamashi mai tsafta a Najeriya.

Hukumar NELFUND da shirin PI-CNG sun jagoranci rabon motocin ga ƙungiyoyin ɗaliban jami’o’in BUK, NWU da YUMSFUE a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.