Hari kan Rarara: Siyasa Ta Shiga Masallatai, an Bukaci Taimakon Sarkin Musumi
- Ƙungiyar matasan Arewa (NEYGA) ta nemi Sultan Sa’ad Abubakar ya shiga tsakani kan zargin amfani da masallatai wajen siyasa
- Ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara a Masallacin Ƙasa da ke Abuja yayin sallar Juma’a
- NEYGA ta kuma buƙaci shugabannin JNI da MURIC su ɗauki mataki domin dakile siyasantar da masallatai da kare zaman lafiya a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ƙungiyar Northern Ethnic Youth Group Assembly (NEYGA) ta nuna damuwa kan yadda ake ƙara amfani da masallatai a yankin Arewa wajen aikata tashe-tashen hankula na siyasa.
Ƙungiyar ta buƙaci shugabannin siyasa su gargaɗi magoya bayansu kan amfani da masallatai wajen siyasa, tana mai cewa wajibi ne a kiyaye wuraren ibada.

Source: Twitter
Kungiya ta yi Allah-wadai da siyasa a masallatai

Kara karanta wannan
Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai
NEYGA ta bayyana matsayarta ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Alhaji Ibrahim Dan-Musa, ya sanya wa hannu a ranar Asabar, cewar Tribune.
Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda rikicin siyasa ke ƙara shiga masallatai, lamarin da ke jefa masu ibada cikin haɗarin fuskantar hare-hare yayin gudanar da ibadarsu.
Dan-Musa ya ce:
“Masallaci wuri ne mai tsarki, inda ake miƙa kai ga Allah Maɗaukaki, ba wurin yaƙin neman zaɓe ko fagen yaƙi ba.
“Abin kunya ne ga ƙasa yadda ’yan siyasa ke shigo da ’yan daba cikin masallatai duk ranar Juma’a domin tsangwamar mutane, cin zarafinsu da kai musu hare-hare saboda kawai suna da ra’ayin siyasa daban.”
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa wannan al'amari na ƙara haifar da rashin haƙuri da bambancin ra’ayi a Arewa, inda har wasu fitattun mutane ke tsoron zuwa masallatai domin gudanar da sallah.
Ta kawo misalin harin da aka kai wa shahararren mawaƙin siyasa na Hausa, Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, a cikin Masallacin Ƙasa da ke Abuja yayin sallar Juma’ar da ta gabata.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027
Bidiyon lamarin ya bazu a kafafen sada zumunta, inda aka ga wasu matasa suna tunkarar mawaƙin tare da dukansa, kafin daga bisani su yaga tufafinsa da ke ɗauke da tambarin Shugaba Bola Tinubu.
NEYGA ta yi Allah wadai da harin, tana mai bayyana shi a matsayin cin zarafin tsarkin wurin ibada, tare da jaddada cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya kawo cikas ga gudanar da ibada ba.
Ƙungiyar ta kuma tuna da harin da aka kai wa ayarin motocin Shugaba Tinubu a wani masallaci da ke unguwar Garki a Abuja ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamba, 2026, jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama mutum 78 da ake zargi bayan wasu mutane sun kai hari kan ayarin motocin shugaban ƙasar da duwatsu.

Source: Twitter
Rokon kungiyar ga Sulta, JNI da MURIC
Domin magance matsalar siyasantar da masallatai, NEYGA ta roƙi Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, da ya shiga tsakani.
Haka kuma, ta buƙaci shugabannin ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) da su kira taron gaggawa na majalisa domin nazarin yadda siyasa ke shiga masallatai da kuma samar da hanyoyin hana sake faruwar irin waɗannan abubuwa.
Haka zalika, ƙungiyar ta yi kira ga ƙungiyar Muslim Rights Concern (MURIC) da ta fito fili ya yi Allah wadai da lamarin tare da haɗa kan masu ruwa da tsaki domin dakile amfani da wuraren ibada wajen harkokin siyasa.
Tinubu ya yafewa wadanda suka masa ihu
An ji cewa shugaba Bola Tinubu ya yi wa waɗanda aka kama a Abuja bayan yi masa ihu a masallacin Juma'a afuwa.
Fadar shugaban ƙasa ta bayar da umarnin gargadinsu tare da sakin su lamarin ya jawo martani ga matakin.
Wata kungiya ta yaba wa Tinubu kan matakin afuwar, inda ta bayyana shi a matsayin karamcin uba, amma ta gargaɗi ’yan siyasa da kada su mayar da cibiyoyin addini wuraren sasanta rikicin siyasa.
Asali: Legit.ng
