Hajjin Bana: An Kaddamar da Jigilar Maniyyata 50,000 daga Najeriya zuwa Saudiyya

Hajjin Bana: An Kaddamar da Jigilar Maniyyata 50,000 daga Najeriya zuwa Saudiyya

  • Hukumar NAHCON ta fara jigilar maniyyatan Hajjin 2026 da maniyyata 474 daga Kogi, yayin da manyan jami’ai suka halarci bikin ƙaddamarwar a Abuja
  • Shugaban NAHCON, Abba Yusuf, ya bukaci maniyyata su bi dokokin Saudiyya tare da amfani da katin Nusuk domin tabbatar da sauƙin zirga-zirga da tsaro
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da gwamna Ahmed Ododo sun roki maniyyata su wakilci Najeriya cikin mutunci, addu’a, zaman lafiya da biyayya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta fara gudanar da aikin Hajjin 2026 da jigilar maniyyata 474 daga Kogi zuwa Saudiyya domin aikin hajji mai albarka.

An gudanar da bikin ƙaddamar da jigilar maniyyatan a Abuja bayan an sauya wajen taron daga Ogun, inda jami’ai da sarakuna suka halarta.

Kara karanta wannan

Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

An fara diban maniyyata zuwa Saudiyya
Dandazon maniyya na shiga jirgi domin zuwa aikin hajji a Saudiyya. Hoto: NAHCON.
Source: Facebook

Shugaban NAHCON, Abba Yusuf, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima saboda goyon bayan gudanar da hajjin bana cikin nasara, cewar Daily Trust.

Hukumar NAHCON ta shawarci maniyyata

Ya bukaci maniyyata su bi dukkan dokokin hukumar NAHCON da Saudiyya, musamman amfani da katin Nusuk domin sauƙaƙa zirga-zirga da shiga wuraren ibada daban-daban.

Abba Yusuf ya ce duk motsin maniyyata zai kasance cikin tsari tare da haɗin kai, saboda hukumar ta shirya masauki da kayan aiki yadda ya kamata.

Ya gargadi maniyyata kan karya dokokin hajji, yana mai cewa hukumomin Saudiyya suna ɗaukar matakan hukunci masu tsauri kan masu sabawa ƙa’idoji.

Shugaban ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da an gudanar da duk gwaje-gwajen lafiya ga maniyyata kafin tafiyarsu zuwa kasar Saudiyya domin hajji.

Ya ƙara da cewa NAHCON ta mayar da hankali kan sauye-sauye masu tabbatar da jin daɗi, tsaro da ingantacciyar hidima ga dukkan maniyyatan Najeriya.

Kara karanta wannan

Duk da Allah wadan Abba, matar da ta jagoranci ɗaga kamfai ta samu mukami a Kano

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci maniyyata su zama jakadu nagari na Najeriya tare da nuna mutunci, haƙuri da gaskiya a Saudiyya.

Shettima ya ce aikin hajji ibada ce mai tsarki, yana mai jaddada cewa babu gurbin sakaci yayin gudanar da aikin hajjin bana.

An fara jigilar maniyyata a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da shugaban hukumar NAHCON, Abba Yusuf. Hoto: National Hajj Commission of Nigeria.
Source: UGC

Minista ya yabawa hukumar NAHCON

Karamar Ministar Abuja, Maryam Mahmoud, ta yabawa shirye-shiryen NAHCON tare da kira ga haɗin kan masu ruwa da tsaki domin samun nasarar aikin hajjin bana.

Ta roki maniyyata su yi addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya yayin gudanar da aikin hajji a ƙasa mai tsarki.

Gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya bayyana aikin hajji a matsayin wata babbar ni’ima ta addini da ke buƙatar tawali’u da gaskiya, cewar The Nation.

Ododo ya bukaci maniyyata su yi amfani da damar wajen tuba, yin tunani mai kyau da kuma yi wa Najeriya addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba.

Sauran manyan baki da suka halarci taron sun haɗa da Ohinoyi na Egbira, Ahmed Tijani Anaje, da Sarkin Jiwa, Idris Musa, wakilin Sarkin Musulmi.

Kara karanta wannan

Abba ya kinkimo aiki, za a kashe sama da N21bn don jiƙa Kanawa da ruwan sha

Hajji: Man jirgin sama yayi tsada

Mun ba ku labarin cewa an fara korafi game da yadda farashin man jirgin sama ya yi mummunan tashi a Najeriya da fargabar lamarin ya shafi aikin Hajjin bana.

Wata kungiya mai alaka da hada-hadar jiragen sama ta ce matukar gwamnati ba ta shiga lamarin ba kudin aikin Hajji zai tashi sosai a kasar nan.

Masu jiragen sama sun yi barazanar fara yajin aiki a Najeriya, inda suka ce wasu kamfanoni sun fara daina aiki saboda matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com