Sani Hamza
5224 articles published since 01 Nuw 2023
5224 articles published since 01 Nuw 2023
Tinubu ya ƙaddamar da ginin sansanin sojoji a Abuja, ya yi alkawarin tallafi da inganta jin daɗin sojojin Najeriya yayin da ƙarancin gidaje ya zama kalubale.
Hukumar NAHCON ta ce maniyyata aikin hajjin 2025 za su samu tallafin $500. Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi ya fadi matsalolin da aka samu a shekarar 2024.
Farashin kayan hatsi a kasuwar Dandume da ke jihar Katsina ya karye sosai, shinkafa N55,000, wake N90,000, gero N67,000; yayin da kasuwar ke ci sau uku a sati.
Hukumar NDLEA ta kama wani Malam Sabo da ke noma tabar wiwi a jihar Kano. A cikin wani bidiyo, dattijon ya fadi yadda jami'ai suka kama shi a cikin gonarsa.
Wani malamin addini kuma limami a jihar Ondo ya fusata matuka da 'yan kungiyar asiri suka kashe mata da dansa. Ya yi ruwan kalaman tsinuwa kan makasan.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume na daga cikin tsofaffin gwamnonin PDP da za su iya goyawa Shugaba Bola Tinubu baya a 2027.
Sunny Moniedafe ya shigar da ƙara a kotu kan APC, yana neman jam'iyyar ta mayar masa da N10m da ya biya na fom ɗin takara a 2022, da kuma diyyar N100m.
An kori Admiral Linda L. Fagan, mace ta farko da ta jagoranci wani reshe na rundunar sojin kasar Amurka a cikin sa'o'i 24 da rantsar da shugaba Trump.
Trump ya zama shugaban Amurka na 47. An rantsar da shi a gaban iyalinsa, ciki har da Barron, wanda Trump ya ce ya taimaka wajen samun kuri’un matasa.
Sani Hamza
Samu kari