'Na Leƙo Jahannama': Paparoma Ya Faɗi Adadin Lokutan da Ya Ga Sheɗan da Idonsa
- Marigayi Paparoma Francis ya bayyana cewa ya ga shaidan sau uku a rayuwarsa, ciki har da lokacin da yake gudanar da ibada a coci
- A cikin kundin bayanansa na sirri, tsohon shugaban Cocin Katolika ya ce ya ga ƙofofin gidan wuta a watan Yunin 2018, lamarin da ya firgita shi
- Paparoma Francis ya kuma bayyana nadamarsa kan ziyarar da ya kai Chile a 2018, inda aka soki shi saboda kare wani limamin da ake zargi da ɓoye cin zarafin yara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Roma, Italiya – Marigayi shugaban Cocin Katolika, Paparoma Francis, ya bayyana cewa ya taɓa ganin shaidan har sau uku a lokuta daban-daban a rayuwarsa, kamar yadda bayanan sirrinsa suka nuna.
An bayyana hakan ne a cikin wani sabon littafi mai suna The Private Diary of Pope Francis, inda aka tattara bayanan da Paparoma ya rubuta tsakanin shekarar 1992 zuwa 2024.

Source: Getty Images
A wani rubutu da ya yi a shekarar 2021, Francis ya bayyana cewa ya ga shaidan sau uku, cewar rahoton BBC.
Yadda marigayi Paparoma ya ga sheɗan
Ya ce karo na farko ya faru ne lokacin da yake cikin mota, na biyu a lokacin gudanar da ibada a coci, yayin da karo na uku ya faru a wani taro da jami'an Vatican.
Da yake bayyana yadda abin ya faru, Paparoma ya ce:
"Ba zan iya mantawa da tsananin kaushin muryarsa ba."
Ya kuma bayyana cewa ba zai manta da idanun shaidan masu ban tsoro ba, yana mai cewa sun yi kama da harshen wuta.
A cewarsa, karo na biyu da ya ga shaidan ya faru ne a wani ɗakin ibada na mabiya darikar Carmelite, lokacin da yake matsayin Archbishop na Buenos Aires.
Ya ce shaidan ya kalle shi da idanu masu kama da wuta, wadanda suka fi tsananin haske da zafin waɗanda ya gani a baya.
Haka kuma, Francis ya bayyana cewa waɗannan abubuwan sun faru ne a wasu lokutan tafiyarsa, ciki har da lokacin da ya kai ziyara Chile a shekarar 2018, yayin da ƙasar ke fuskantar rikicin zargin cin zarafin yara da wasu limaman coci suka aikata.

Source: Twitter
Paparoma Francis ya ga ƙofofin gidan wuta
A wani ɓangare na bayanansa, marigayi Paparoma ya bayyana cewa a watan Yunin 2018, lokacin da yake shirin kwanciya barci, ya ga abin da ya kira ƙofofin gidan wuta, ya ce abin ya firgita shi matuƙa, inda ya ɗauki carbi a matsayin makamin kare kansa.
A kalamansa:
"Na ɗan kalli abin, sai tsoro ya kama ni. Na ɗauki carbi a matsayin makami."
Ya ƙara da cewa kusantar ƙofofin gidan wuta na da haɗari, domin harshen wuta na iya fitowa daga cikinsu ya ƙone mutum, cewar DW.
An jefi Paparoma Leo a wurin taro
An ji cewa wani mutum ya jefi Paparoma Leo XIV da carbi inda suka same shi a fuska yayin da yake gaishe da mabiya addinin Kirista a Peru.
Lamarin ya faru ne yayin da Paparoma ke cikin motarsa ta musamman a filin jirgin saman Las Palmas da ke Lima.
Duk da faruwar lamarin, Paparoma Leo bai samu rauni ba, kuma ya ci gaba da gudanar da sauran ayyukansa kamar yadda aka tsara.
Asali: Legit.ng

