'Yan Bindiga Sun Kashe Malamai 2, Sun Yi Awon Gaba da Mutane Sama da 10

'Yan Bindiga Sun Kashe Malamai 2, Sun Yi Awon Gaba da Mutane Sama da 10

  • ’Yan bindiga sun kashe malamai biyu a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara yayin da suke aiki a gonakinsu
  • Maharan sun kuma yi garkuwa da mutane 13 a wani hari daban, ciki har da jariri mai watanni 11 da wasu ƙananan yara
  • Rundunar ’yan sanda ta ce ta tura jami’an tsaro domin ceto waɗanda aka sace tare da kama waɗanda suka aikata laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - ’Yan bindiga sun kashe malamai biyu a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara, yayin da suka yi garkuwa da wasu mazauna yankin 13, ciki har da jariri mai watanni 11.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da hare-haren biyu a cikin bayanan ayyukan tsaro da ta fitar a faɗin ƙasar ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

Bayan rashin 'yan APC 15, tsohon sakataren gwamnatin Zamfara ya rasu

Leadership ta rahoto cewa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Ani Iniedu, ya bayyana sunayen malaman da aka kashe a matsayin Kabiru Umar, mai shekaru 35, da Shuaibu Salisu, shi ma mai shekaru 35.

A cewar rundunar ’yan sandan, an yi wa malaman kwanton ɓauna ne tare da kashe su yayin da suke aiki a gonakinsu da ke ƙauyen Tungar Janbuzu, ƙaramar hukumar Maru.

Sai dai sanarwar ’yan sandan ba ta bayyana sunayen makarantun da malaman ke koyarwa ba.

A lokacin haɗa wannan rahoto, ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da makarantun da suke aiki daga Hukumar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Maru da reshen Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) a Jihar Zamfara.

An sace mutane 13 a Jabaka

A wani hari na biyu, ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Jabaka, wanda shi ma yake cikin ƙaramar hukumar Maru, a daren Laraba, inda suka yi garkuwa da mutane 13, ciki har da jaririn da wasu ƙananan yara.

Rundunar ’yan sandan ba ta fitar da sunayen mutanen da aka yi garkuwa da su ba.

CSP Iniedu ya ce an haɗa jami’an rundunar da ke gudanar da ayyuka na musamman, sojoji, ’yan sa-kai da mafarauta domin ceto waɗanda aka sace da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Yan bindiga sun banka wa gari wuta, sun ƙona mutane da ransu

Ya ƙara da cewa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sanda (CID) da ke Gusau ya fara gudanar da bincike kan hare-haren.

Sabbabin hare-haren sun ƙara tsorata mazauna Maru da sauran al’ummomin Jihar Zamfara, inda mutane ke ci gaba da fuskantar kashe-kashe, satar mutane da tilasta musu barin muhallansu.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, domin samun ƙarin bayani kan aikin ceto mutanen da aka sace bai yi nasara ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Yan bindiga sun kona kauye a Zamfara

Kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Duhuwaya da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara, inda suka kashe wasu mazauna yankin.

Maharan sun ƙona gidaje da dama, ciki har da waɗanda wasu tsofaffin mata masu shekaru tsakanin 70 zuwa 80 ke zaune a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262