Kotu Ta Rike wa Gwamnonin Najeriya $100m a Banki saboda Bashin Paris Club
- Wata kotu a Abuja ta rufe dala miliyan 100 da ake danganta wa da Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kan takaddamar kuɗin Paris Club
- Wani lauya, Ted Iseghohi-Edwards, ya ce kuɗin nasa ne bisa yarjejeniyar da ya yi da ƙungiyar gwamnonin kan kuɗin aikin shari’a
- Bayan an yi zama a gaban alkali, kotu ta umarci bankuna 29 da su rufe kuɗin kuma aka dage sauraron ƙarar zuwa Disamban 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Wata Babbar Kotun Tarayya a birnin Abuja ta yi umarnin a rufe dala miliyan 100 da ake zargin suna hannun Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya.
A sakamakon takaddama kan kuɗin da lamarin bashin Paris Club ya sa aka rike kudin da aka yi lissafin cewa sun kai kimanin Naira biliyan 135.58.

Source: Facebook
Kotu ta yi umarnin rike dukiyar kungiyar gwamnoni
Vanguard ta ce Mai shari'a O.C. Agbaza ya bayar da umarnin wucin gadi a ranar 19 ga Nuwamba, 2026, bayan karar Dr. Ted Iseghohi-Edwards.
Lauyan ya shigar da ƙara a kan ƙungiyar gwamnonin da wasu bankunan kasuwanci 29 a Abuja.
Kotun ta hana ƙungiyar gwamnonin cire kuɗin, tura su wani wuri, ɓoye su, kashe su ko yin duk wani abin da zai sauya matsayinsu sai an gama shari’a.
An umarci bankuna su bayyana asusun gwamnoni
Mai shari'ar ya umarci bankunan da su gabatar da bayanai cikin sa'o'i 48 domin a ji ko ƙungiyar gwamnonin tana da kudin nan a cikin asusun ajiyarsu.
Bankunan za su bayyana lambobin asusun, kuɗin da ke cikinsu, irin kuɗin da ake amfani da su wajen ajiya da kuma adadin abin da aka rufe a cikin asusu.
Abin da ya sa lauyan yake neman $100m
Lauyan mai ƙara, Ted Iseghohi-Edwards, ya ce kuɗin nasa ne bisa wata yarjejeniya da ƙungiyar gwamnonin ta shiga tun cikin Disamban 2018.
Lauyan ya ce ALGON ce ta ɗauke shi aiki ya wakilci ƙananan hukumomin 774 na ƙasar a batutuwan da suka shafi bashin London da Paris Club.
Daga bisani, ya shigar da ƙara a kan Gwamnatin tarayya, yana neman a biya shi kuɗin aikin da ya yi kamar yadda tashar Arise TV ta fitar da rahoto.
A cewar takardun da ya kai kotu, an yanke hukunci ranar 16 ga Fabrairu, 2018, inda kotu ta tabbatar da yana bin Gwamnatin tarayya bashin $318m.
Ya ce daga baya Gwamnatin tarayya ta biya wani ɓangare na kuɗin, ya samu dala miliyan 159.
Iseghohi-Edwards ya yi iƙirarin hukuncin ya cika sharadin da ke cikin yarjejeniyar da aka yi, don haka ya kamata a biya shi ragowar dala miliyan 100.
Lauya ya jawo an riƙe dukiyar ƙungiyar gwamnoni
Ya kuma ce ya aika wa ƙungiyar gwamnonin jihohi takardar neman kuɗin a ranar 8 ga Oktoba, 2026, amma ba ta cika alƙawarin da ta ɗauka ba.
Saboda haka, ya garzaya kotu domin neman rufe kuɗin cikin asusunsu har sai an kammala shari'ar.
An rahoto shi yana mai fargabar cewa ƙungiyar gwamnonin za ta iya karkatar da kuɗin ko kashe su kafin a yanke hukunci, kuma aka duba maganarsa.
Kotu ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 1 ga Disamba, 2026, domin sauraron buƙatar da aka gabatar.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Mutane da dama sun mutu da aka yi yunkurin kashe sanata a wurin kamfe

Source: Facebook
An rubuta littafin tarihin Muhammadu Buhari
Rahoton nan ya ce littafin tarihin marigayi Muhammadu Buhari ya yi nazarin nasarorin gwamnatinsa, gazawa da ce-ce-ku-cen da suka dabaibaye ta.
Udo Yakubu ne ya rubuta littafin bayan kwashe sama da shekaru biyu yana bincike. Littafin ya bi diddigin rayuwar shi tun daga yarintarsa a Daura.
A wajen kaddamarwar, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da tsohon shugaban ƙasar Nijar, Mahamadou Issoufou, sun yabi marigayin.
Asali: Legit.ng

